Mummunar manufar nan kan bakin haure da shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya bullo da ita ta jefa dubban baki dake zama a kasarsa cikin mawuyacin hali na kaskanci, yayin da matakin ya raba dubban baki da iyalansu, sabo da yadda ake bi sako da lungu ana farautar bakin mazauna Amerika ba tare da bin ka’ida ba.
Da dama wadanda aka kame a matsayin bakin hauren ba su cikin rukunin wadanda suka cancanci kora. Wato irin wadanda ke zama Amerika ba tare da cikakkun takardu ba, ko wadanda bizarsu ta kare, ko kuma wadanda suka aikata miyagun laifuka, kamar su fashi da makami, hada-hada da miyagun kwayoyi, sata ko zamba cikin aminci da makamantansu.
To yanzu dai shugaba Trump ya rasa yadda zai yi da wadannan dubban bakin haure da aka kame, amma a ganinsa akwai mafita, wato ta tursasawa kasashen Afirka da su karbi bakuncin wadannan bakin haure, idan kuma suka ki amincewa, to shugaba Trump ya sha alwashin kakaba harajin cinikayya a kan wadannan kasashe.
Yanzu haka dai Sudan ta kudu ta ba da kai, domin kuwa tuni har wani rukunin bakin hauren su takwas sun sauka birnin Juba, babban birnin Sudan ta kudu. Daya ne tak dan asalin Sudan ta kudu, sauran kuwa sun hada da ’yan kasashen Myammar, Cuba da Vietnam. Akasarinsu dai mutanen da suka aikata muggan laifuka ne, kuma suka shafe shekaru da dama a gidajen kurkuku na Amerika.
Kazalika, shugaba Trump ya yi yunkurin turo irin wadannan bakin haure ’yan asalin Venezuela zuwa Nijeriya, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba. Nan take dai ma’aikatar kula da harkokin wajen Nijeriya ta ki amincewa da wannan bukata. Nijeriya ba za ta zama jujin da Amerika za ta jibge sharar bakin haurenta ba, wadanda akasarinsu tsaffin masu aikata muggan laifuka ne wadanda suka kwashe shekara da shekaru gidan kaso. Don haka abar Nijeriya ta ji da matsalar da ke gabanta na yaki da rashin tsaro, ba wai a kara ingizo mata karin matsala ba.
Babban abin dubawa a nan shi ne ko mene ne hikimar tura irin wadannan bakin haure zuwa kasashen Afirka? Misali kamar bakin hauren da Amerika take son turawa Nijeria, ’yan asalin kasar Venezuela, ko kuma bakin hauren da Sudan ta kudu ta karba ’yan asalin Myammar, da Cuba da Vietnam, al’adunsu da harshensu sun sha banban da na ’yan Afirka. Sabo da haka babu wata alaka tsakanin juna.
To idan ba domin isgilanci da gadara ba, ta yaya Mr. Trump zai nemi tursasawa kasashen Afirka karbar irin wadannan bakin haure maimakon ya tasa keyarsu zuwa kasashensu na asali?(Lawal Mamuda)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp