Dan wasan damben nan, Kubrat Pulev, ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa dan wasa Tyson Fury zai doke Anthony Joshua a fafatawar da ‘yan birtaniyan biyu zasu yi nan gaba a cikin wannan shekarar.
A farkon watan Disambar daya gabata ne dai Anthony Joshua, ya doke Pulev a wani dambe da suka fafata a birnin Landan, wanda hakan yasa yanzu ake ganin mutum daya ne zai iya takawa Anthony Joshua birki, wato Tyson Fury.
Sai dai shima tuni Anthony Joshua, ya bayyana cewa shima ya gama shiryawa domin fafata wasa da Tyson Fury, dan burtaniya, a wasan da zakarun biyu zasu kece a sabuwar shekarar nan da muke ciki.
A ranar da Pulev yasha kashi a hannun Joshua, Tyson Fury ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin fafata wasan Dambe da zakaran wannan lokacin Anthony Joshua a wasan da ake saran za’a fafata a birnin Landan din Ingila.
A tsakiyar wannan watan ne dan damben Burtaniya Anthony Joshua ya doke Kubrat Pulev, dan asalin kasar Bulgeria wanda hakan ya kara fitowa da batun karawarsa da Tyson Fury fili kuma Joshua ya yi nasara ne a fafatawar da aka kai zagaye uku ana yi.
‘Yan kallo 1,000 ne dai aka bai wa damar shiga filin wasa na Wembley Arena, la’akari da daukar matakan bayar da tazara saboda annobar korona kuma jim kadan bayan nasarar da Anthony Joshua ya samu ne magoya bayansa suka rika fadar cewa ‘saura Fury’.
‘Yan kallo 1,000 ne aka baiwa damar shiga filin wasa na Wembley Arena, la’akari da daukar matakan bada tazara saboda annobar Korona sai dain idan ba’a manta ba kadan ya rage ganiyar Joshua ta ruguje a watan Disambar bara, a lokacin da ya dauki fansa kan Andy Ruiz Jr.
Kuma kisan da ya yi wa Kubrat Pulev a daren Asabar ya nuna cewa a yanzu Tyson Fury ne kawai ya rage su saka zare, don ya tabbatar wa duniya kololuwar inda kwarewarsa ta kai a duniyar dambe.
Anthony Joshua Murdadde ne na kin karawa, hannayensa cike suke da damatsa, sannan yana magana da murya mai sanyi, hade da murmushi a fuskarsa sannan a fagen dambe, yana da tarihin yiwa abokan karawarsa kwaf daya, yana da sunaye iri-iri na jarumta, abin da ke nufin cewa ga mutane da dama, Joshua ne gagarabadau cikin yan damben da suka fito daga Najeriya tun bayan gwarzon NBA Hakeem Olajuwon.
Tuni Joshua ya fara shafar rayuwar samari da yawa musamman a kudu maso yammacin Najeriya, kamar Legas babban birnin kasuwancin kasar domin da yawa daga cikinsu sun kalli yadda ya zama shahararre ya cika burinsa na rayuwa, kuma labarinsa kusan yazo dai-dai da nasu, na wanda ya sha wahalar rayuwa kafin daga bisani kofar arzikinsa ta bude ya sha kwana.
Labarinsa, wani abu ne da aka jima ana nuna irinsa a fina-finai irin na Nollywood, kamar dai ace na mutumin da burinsa na rayuwa ya cika bayan shan kwarba shekara da shekaru sannan Joshua ya zama wata sila ta samun karvuwar harkar dambe a Najeriya, domin a yanzu, har ta kai ga ana horar da mutane wasan a makarantu bayan tashi daga karatu, da kuma ranakun hutu da sauran wurare da dama.