USAID Ta Horas Da Malamai 7,169 A Jihar Borno

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Malaman makarantun firamare da ƙaramar sakandiri kimanin dubu bakwai da ɗari ɗaya da sittin da tara (7,169) ne a JiharBorno suka samu horo na musamman daga hukumar bunƙasa ƙasashe ta Amurika (United State Agency for International Deɓelopment), baya ga buƙatar hakan ga hukumar ta hannun gwamnan Jihar,Kashim Shettima. Matakin wanda ya zo a ƙarƙashin shirin gwamnatin jihar wajen gina sabbin makarantu da tsuffin a baki ɗayan jihar tare da fasalta tsarin su ya tafi kafaɗa da kafaɗa da zamani.

Kamar yadda mai Daraktan haɗa labarai na Gwamnan jihar, Malam Isa Umar Gusau ya naƙalto, ya ce hukumar ta USAID a ƙarƙashin cibiyar bayar da ɗauki a tafarkin matsalolin da ilimi a ƙarƙashin jagorancin babban Daraktan ayyukan hukumar, Ayo Oladini, ablokacin wata ziyara da tawagar sa ta kaiwa Gwamna Shettima, ranar Alhamis da ta gabata. Domin yin tilawar nasarorin da suka cimma ta hanyar hoɓɓasar da gwamnatin jihar take basu. Tawagar ta haɗa da mataimakin shugaban gamayyar ƙungiyar malamai(NUT) ta ƙasa.

Yayin da ya fara da bayyana cewa, hukumar USAID- ayyukan cibiyar bayar da ɗauki a sha’anin ilimi ta kammala horas da malaman makarantun firamare 7,169 dabarun koyarwa na zamani dake gundumomi biyar a JiharBorno da suka haɗa da; Biu, Jere, Kaga, Konduga da kuma ƙwaryar Maiduguri. Haka kuma, kwamishina mai kula da sha’anin ilimin jihar, Alhaji Musa Inuwa Kubo da manyan jami’an gwamnatin suka kasance daga cikin mahalarta taron.

Har wala yau, Malam Isa Gusau ya ce gwamnan ya bukaci cibiyar da ta ci gaba da tallafawa wajen baiwa malaman makarantun jihar horon dangane da hoɓɓasar da gwamnatin JiharBorno ke yi wajen samar da ƙwararrun malamai a cikin sabbin makarantun da ta girka ɗaukwacin jihar.

Gwamna Shettima ya ankarar da cewa hukumar tana gudanar wannan aiki, tare da taka muhimmiyar rawa dangance da matsalolin da suka shafi ilimi, a cikin shekaru uku da suka shuɗe a jihohin Adamawa da Bauchi da Borno, Gombe da Yobe. Kuma yanzu haka tana tafiyar da wani shiri bunƙasa ilimi wanda ya ƙunshi yara da matasa sama da 47,722 a jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe haɗi da Yobe; wanda aka fara shi a cikin watan October bara.

Bugu da ƙari kuma, babban jami’in tsare-tsaren hukumar ta USAID ya sake bayyana adadin alƙaluman da suka nuna cewa, suna gudanar da horas da yara da matasa 37,069 a cikin cibiyoyi koyarwa 731 na makarantun da ba na zamani ba, da kuma ƙarin adadin 10,653 da suke ba horo a cikin makarantun zamani.

Exit mobile version