Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta ƙaddamar da jakadun wayar da kai game da alluran rigakafin yara da ƙarfafa kiwon lafiya a matakin farko a jihar, a taron da aka gudanar a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko ta Dr. Karima da ke Tudun Wada, Gusau.
Taron ya samu halartar jami’an gwamnati, da Sarakunan gargajiya, da shugabannin ƙananan hukumomi da ƙungiyoyin bayar da tallafi. Hajiya Huriyya ta bayyana gangamin a matsayin wani muhimmin mataki na kare rayukan yara, tana mai jaddada cewa haɗin gwuiwa tsakanin iyaye, da al’umma da shugabanni na da matuƙar muhimmanci wajen ƙaruwar amsar rigakafi.
- Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
- Musulmin da Aka Kashe A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN
A wajen taron, Uwargidan Gwamnan ta rantsar da Maman Jakadu, matan shugabannin ƙananan hukumomi – waɗanda za su na isar da bayanai ga al’ummomi don ƙarfafar iyaye su kai ƴaƴansu rigakafi kafin haihuwa da bayan haihuwa. Ta ce jita-jita da labaran ƙarya game da rigakafi na kawo cikas, inda ta tabbatar da cewa duk alluran da ake amfani da su a Nijeriya suna da aminci kuma babu wata illa da ke tattare da su. Ta yabawa sarakuna da malamai bisa rawar da suke takawa wajen ƙarfafa wayar da kan jama’a.
Babban Sakataren hukumar lula da lafiya a matakin farko a jihar, Dakta Hussaini Anka, ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara cikin watanni 11 da suka gabata ta fuskar raguwar cututtukan da rigakafi ke iya hanawa, sakamakon sabbin shirye-shiryen ceton rai da aka aiwatar. Ya ce Gwamna Dauda Lawal ya kashe sama da Naira biliyan biyu don gyaran cibiyoyin lafiya 147 a matakin farko, a ƙoƙarin magance ƙarancin amsar rigakafi da tabbatar da cewa jama’a na samun kulawa kai tsaye.
Sarkin Zamfaran Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, ya buƙaci iyaye su karɓi rigakafi don ƴaƴansu ba tare da tsoro ko shakka ba, yana mai jaddada cewa Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta tabbatar da cewa rigakafi ba shi da wata matsala ga lafiya. Ya ce masarautun gargajiya za su ci gaba da tallafa wa gwamnati wajen yaƙi da cututtukan da za a iya maganinsu, domin tabbatar da cewa duk wani yaro a Zamfara ya samu kariyar da ta dace.














