Hukumomi sun tabbatar da mutuwar akalla mutane bakwai bayan wani turmutsutsu a yayin taron karbar sadaka da ya gudana a Bauchi a karshen mako.
Hukumomin ‘yan sanda sun bayyana cewa, shida daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su an tabbatar da mutuwarsu a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, daya kuma ya mutu a gida.
- Mutane 4 Sun Mutu A Turmutsutsun Karɓar Zakka A Bauchi
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 3 Da Ake Zargi Da Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane A Bauchi
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakili, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a yayin da yake bayar da karin haske kan lamarin.
Wakili ya bayar da bayanan wadanda suka mutu a wurin da suka hada da Aisha Usman da Sahura Abubakar da Aisha Ibrahim Abubakar da kuma Khadija Isah.
Sauran wadanda suka rasun su ne; Maryam Suleiman da Maryam Shuibu da kuma Hassana Saidu wadda ta fito daga Dutsen Tanshi, rahoton wadanda abin ya rutsa da su duka mata ne kuma ‘yan jihar Bauchi.
LEADERSHIP Hausa ta rawaito faruwar lamarin a ranar Lahadi a kamfanin Shafa Holdings Plc daura da hanyar Jos a cikin birnin Bauchi.
Mutane da dama ne suka taru a wurin don karbar sadakar Naira 10,000 a hannun wani mutum da ba a bayyana sunansa ba.
Yawan jama’ar da ke wurin ne ya haifar da hargitsi da turmutsutsu wanda ya zama sanadiyar mutuwar mutane bakwai a yayin karbar sadakar.