A baya-bayan nan ne dai ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar ya fito fili ya bayyana cewa, Amurka na yin matsin lamba ga kasashen Afirka, don su karbi bakin hauren da Amurka ta kora daga cikin gidanta. Inda Najeriya, a bisa matsayinta na wata babbar kasa, ta daure da matsin lambar, kuma ta ce “A’a” ga Amurka. Sai dai ga wasu kasashe masu raunin tattalin arziki, da suke fuskantar matsin lamba daga Amurka, yawancinsu ba su da wani zabi illa mika wuya.
A cewar gidan telabijin na CNN, a kwanan baya kasar Amurka ta kori bakin haure biyar, ‘yan kasashen Jamaica, Laos, Cuba, Yemen da Vietnam, wadanda ake zargi da aikata manyan laifuffuka a kasar. Sa’an nan ta tusa keyarsu zuwa kasar da take wa lakabin “kasa ta uku mai tsaro”, wato kasar Eswatini dake kudancin nahiyar Afirka. Wannan lamari dai ya haifar da fushi mai tsanani a tsakanin al’ummar Eswatini. Har ma jam’iyyar adawa ta kasar, PUDEMO, ta ce karbar wadannan bakin haure da Amurka ta kora “yana da babbar barazana ga al’ummar Eswatini, wadanda da ma sun kasance cikin yanayi mai rauni.”
- An Samu Rarrabuwar Kai Kan Makin Shiga Manyan Makarantu
- Yadda Hauhawar Farashin Kayan Abinci Ya Ragu A Nijeriya
Abin da ya ba ni sha’awa a cikin wannan al’amari shi ne sunan da Amurka ta lakaba wa Eswatini, wato “kasa ta uku mai tsaro”. A cewar wasu takardun bayani na kungiyar kasashen Turai ta EU, kukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta taba jaddada cewa, ya kamata a sami “alaka mai ma’ana” tsakanin “kasa ta uku mai tsaro” da ‘yan gudun hijira masu neman mafaka, misali, dangin da ke zaune a kasar. Bugu da kari, ya kamata “kasa ta uku mai tsaro” ta tabbatar da cewa ‘yan gudun hijirar sun sami cikakkiyar kariya a cikin yankunanta.
Bisa ga wannan ma’auni, bai kamata a dora Eswatini a matsayin “kasa ta uku mai tsaro” ba. Saboda, da farko, babu wata “alaka mai ma’ana” tsakanin mutanen biyar da kasar Eswatini. Na biyu, da alama kasar ba za ta iya ba wa wadannan mutane “cikakkiyar kariya” ba. Bisa wani rahoton batun kare hakkin dan Adam na kasar Eswatini da ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar, an ce akwai lamarin “aikata hukuncin kisa ba bisa doka ba” da “hukunce-hukunce na zalunci” da suka afku a kasar, kuma gidajen yarin kasar na fuskantar matsalolin “cunkoso, da lalacewar kayayyaki, da rashin abinci mai gina jiki, da yawan samun fadace-fadace tsakanin fursunoni.”
Amma duk da haka kasar Amurka ta mai da Eswatini a matsayin “kasa ta uku mai tsaro”. Saboda me? Dalili na farko shi ne domin kasar Amurka ta ga yana da sauki a sarrafa wata karamar kasa, wadda za ta karbi bakin hauren da aka kora, bayan an dan matsa mata lamba. Bugu da kari, wata takardar gwamnati da jaridar Washington Post ta nuna wa jama’a ta shaida ce, watakila da gangan ne gwamnatin Amurka ke korar bakin haure zuwa kasashen da ba a samun cikakken hakkin dan Adam. Ta haka ne gwamnatin Amurka ke fatan tilasta wa bakin haure don su bar kasar da kansu, in ba haka ba za a iya korarsu zuwa Eswatini, ko kuma Sudan ta Kudu da ke fama da tashin hankali, har ma za a iya kulle su a rumbun ajiyar kaya na wani sansanin sojan Amurka dake nahiyar Afirka (wani abu da ya taba faruwa a kasar Djibouti a baya-bayan nan) .
Ana iya takaita halin Amurka game da wannan al’amari da kalma daya: Maras kulawa. Saboda kasar ba ta damu da nauyin da ke kanta bisa la’akari da matsayinta na babbar kasa ba, balle ma dangantakar diflomasiyya, da adalci, da hakkin bil’adama, da muradu na wasu kasashe. Sai dai abu daya kawai dake janyo hankalinta, wato kokarin cika burin korar baki. Hakika wannan ra’ayi na “Amurka na gaba da kome” da yanayi na son kai sun kasance cikin dukkan manufofin kasar.
Eswatini, wadda Amurka ta manna ta kan matsayin “kasa ta uku mai tsaro” a wannan karo, ba a san irin “yarjejeniya” da ta kulla da Amurka ba. Amma, zai yi matukar wahala Eswatini ta kare muradunta, yayin da take mu’amala da wata babbar kasa kamar Amurka mai matukar son kai. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp