Yayin da shekara ta 2025 ke yin bankwana, akwai abubuwa da dama a fannin fasahar zamani da kasar Sin ta yi fice tsakaninta da sauran kasashen duniya da ya kamata a yi waiwaye a kai. A nan za mu yi waiwaye adon tafiya a fannin fasahar kirkirarriyar basira wato AI, musamman bisa ga yadda ta yi fice a duniya, kasancewar a wannan zamani, fasahar AI ita ce kan gaba a duk fannoni na rayuwar dan adam, kamar su fannin noma, kiwon lafiya, masana’antu, ilimi da dai sauransu.
A cikin wannan shekara mai shudewa kasar Sin ta girgiza duniya a fannin fasahar kirkirarriyar basira, a lokacin da ta kaddamar da wani sabon nau’i na Deepseek V3, wato manhajar da kamfaninin mallakar Liang Wenfeng ya kirkiro tun shekara ta 2023. Wannan manhaja ta sanya kasashen yammaci da Amerika suka yi matukar mamakin irin wannan fasaha, musamman bisa ga yadda suke ganin su ne kan gaba a fannin fasahar kirkirarriyar basira a duniya. Wannan lamari ya sanya har sai da Amerika ta nuna hassadarta a fili, tana mai cewa ya zama wajibi a takawa Sin birki bisa ga irin wannan ci gaba da take samu a fannin fasahar AI.
Manhajar DeepSeek ta kawo babban sauyi a fagen fasahar kirkirarriyar basira, musamman idan aka yi la’akari da yadda ta kasance ta farko a dandalin manhaja na Apple, sannan kuma ana samunta cikin sauki da araha, ko kuma kyauta ta yadda kowa zai iya amfani da ita, sabanin manhajar Chat GPT da ire-irensu wadanda ba kowa ke iya samunsu ba cikin sauki.
Gabanin samuwar Deepseek, kasashe masu tasowa na Afirka an mai da su saniyar ware a fannin fasahar kirkirarriyar basira. To amma al’amurra sun sauya yayin da kasar Sin ta yunkuro wajen samar da fasahar Deepseek, abin da ya baiwa kasashen Afirka damar cin gajiyar fasahar AI ta Deepseek, ta hanyar samar da horo a fannin fasahar kirkirarriyar basira ga dubban matasan Afirka, abin da ya bunkasa kwarewarsu a fasahar AI. Baya ga wannan ma, kamfanonin kasar Sin suna zuba dimbin jari a bangaren fasahar kirkirarriyar basira a kasashen Afirka da suka hada da cibiyoyin tara bayanai da cibiyoyin samar da hidima kan kididdigar bayanan na’ura mai kwakwalwa. Bugu da kari Sin tana hada gwiwa da kasashen Afirka wajen samar da fasahar kirkirarriyar basira domin bunkasa fannonin kiwon lafiya, aikin gona da ilimi.
In dai ba a manta ba, a cikin wannan shekara mai shudewa ce aka bullo da wasu matakai na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za su bunkasa fasahar kirkirarriyar basira da suka hada da hadin gwiwa na tsawon shekaru biyu a fannin bincike, bayar da horo da shugabanci a kan kirkirarriyar fasaha ta AI. Akwai kuma shirin bayar da horo ga dalibai da matasan Najeriya a fannin fasahar kirkirarriyar basira.
Muhimman alfanun da wannan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ya samar sun hada da cike gibin dake akwai tsakanin kasashen Afirka wadanda aka mai da saniyar ware da kasashen yammacin duniya a fannin AI. Akwai kuma alfanu na samun bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka, bunkasuwar harkar kiwon lafiya a yankunan karkara da kuma bunkasuwar bangaren aikin gona, duk ta hanyar yin amfani da kirkirarriyar fasaha ta AI wadda kasar Sin ta samar ga wadannan kasashe masu tasowa na Afirka.
Wannan rawa da Sin take takawa ga kasashen Afirka tana da muhimmanci matuka, kuma ana fatan za ta ci gaba da dorewa a matsayin linzami ga makomar kasashen Afirka a fannin fasahar kirkirarriyar basira ta AI.














