Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home Waiwayen Kanun Labarai

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 9 Zuwa 12 Ga Rabi’ul Sani 144  

by Muhammad
November 27, 2020
in Waiwayen Kanun Labarai
8 min read
Kanun Labaru
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Ishak Idris Guibi

LITININ

samndaads

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yaba da tura ‘yan sanda na musamman da Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Mohammed Adamu ya ce zai yi zuwa jihar Nasarawa don gano wadanda suka sace shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, daga bisani aka tsinci gawarsa da harbi biyu na bindiga.

Kidinafas sun sako ‘ya’yanmu daliban jami’ar ABU Zariya da suka yi kidinafin su tara, bayan an biya kudi, daidai arzikin gidan yaro daidai cinikinsa. In kai dan talaka ne naira miliyan biyu, in dan mai hali ne har naira miliyan ashirin da biyar. Haka kowa aka biya nasa aka sako shi shekaranjiya wuraren karfe daya da wasu mintoci na dare.

Nijeriya da Nijar sun sanya hannu a wata yarjejeniya ta shigo da danyen mai kasar nan.

Atiku Abubakar ya ce da an bi shawararsa da tattalin arzikin kasar nan bai kuma shiga mawuyacin halin da ya shiga a halin yanzun ba wato RECESSION.

A jihar Zamfara gwamnan jihar Matawalle ya ce ya ceto mutum goma sha daya, maza goma mace daya da suka kwashe wata biyu zuwa uku a hannun kidinafas, sakamakon sasantawar da ya yi da kidinafas.

Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

Ministan Kwadago Ngige ya ce su ba su tsame malaman jami’a daga tsarin IPPIS ba, sun dai ce ne a biya malaman da ba su shiga tsarin ba zuwa yanzun, albashin da suke bi na wata da watanni ta amfani da tsohon tsarin da ba na IPPIS ba.

Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Wata kotu ta yi fatali da wani korafin shugaban Amurka Donald Trump a kan kayen da ya sha a hannun shugaban Amurka mai jiran gado Biden.

 

 

 

 

TALATA

 

A ranar Lahadi da daddare wasu kidinafas sun je daya daga cikin gidajen ma’aikata na jami’ar E.BI.YU. /A.B.U. da ke Samarun Zariya, suka yi kidinafin wani malami da matarsa da diyarsa. Da yake an sanar da ”yan sandan kwantar da tarzoma, nan take suka kai dauki aka yi harbe-harbe, da kidinafas suka lura za a fi karfinsu, suka bar matar da diyar suka tafi da shi mijin. Har na ji wasu na cewa su kidinafas ba su san yawanci malaman jami’a rabonsu da albashi tun watan Maris na wannan shekarar ba ne?

Bayanai na nuna kidinafas sun sako wanda suka yi kidinafin a kwalejin foliteknik ta Nuhu Bamalli da ke Zariya.

An yi kidinafin wani Baba Wuro dan uwan wani Minista mai ci.

Wasu ‘yan kungiyar Boko Haram sun yi sanadiyyar mutuwar sojoji bakwai da JTF daya, a hanyarsu ta kai kayayyakin agaji wajen ‘yan gudun hijira a jihar Barno, ashe ‘yan kungiyar sun bisne bom a hanyar.

Wata kotu ta sa a tsare mata Sanata Ndume a gidan yari na Kuje saboda shi ya tsaya wa Abdulrasheed Maina beli, ga shi ya kasa gabatar da Maina, ana batun Maina ya gudu. Kotu na bukatar Ndume ya biya gwamnatin tarayya wata Naira Miliyan Dari Biyar ko sayar da kaddararsa don biyan kudin. Sai dai na ji wasu na korafin don me ba a yi wa Sanata Aberibe da ya tsaya wa Nnamdi Kanu, a karshe Kanun ya gudu haka ba, sai Sanata Ndume?

“Allah Ya jikan Ahmed Usman da Ahmed Aja Gwarzo. Shi Ahmed Usman mun yi aiki tare da shi a kamfanin Newage Network a shekarar 2010. Shi kuwa Ahmed Aja Gwarzo da wuya ya ji an yi Hausar da ba ta dace ba a rediyo bai kira ni a waya ya shaida mun ba. Sannan duk juma’a sai ya sayi jaridar Leadership ta Hausa don karanta rubutun da na saba yi a shafin adabi. Yana buda shafin zai kira ni a waya ya ce ga rubutunka nan ina karantawa. Ni ma kuma kusan duk Lahadi shirinsa na wasa kwakwalwa ba ya wuce ni. Lahadi da ta gabata da na ji Muhammad Lawal Kaya ya soma gabatar da shirin da bayanin Aja Gwarzo ba lafiya, sai na kira wayar Aja Gwarzo, na ji ya amsa mun da kyar sai jikina ya yi sanyi. Ya ce “Guibi ne?” Na amsa masa ni ne. Ya ce “ina asibiti” Da yake na san yakan kai ‘ya’yansa asibitin Biba, sai na tambaye shi “Wanne asibiti? Na Biba?” Ya ce “Asibitin Dutse” Na ce masa “Allah Ya ba ka lafiya sai gobe da safe Idan za ni ofis zan biyo” Ya ce ya gode. Iyali da yake sun san yadda yake yawan waiwayata a waya suka tambaye ni na ce musu Aja Gwarzo ba lafiya muryarsa ta canza. Da safe Allah Bai ba ni ikon biyawa ba don gaskiya na shafa’a. Na dawo gida daga Birnin Yero wuraren karfe daya na rana iyalina suka ce sun ji sanarwar rasuwar mutumina Ahmed Aja Gwarzo. Allah Ya jikansu da rahama, ya yafe musu kurakuransu, mu da muka yi saura Allah Ka sa mu cika da kyau da imani Amin”

 

 

LARABA

An ci gaba da shari’ar Maina duk da ba ya nan, shari’ar da ake zargin ya wawuri wata Naira Biliyan Biyu.

Al’umomi na Arewa na ta nuna rashin jin dadinsu a kan yadda matsalar tsaro ke addabar Arewa, kuma shugabanni suka gaza kare Arewar.

Jami’an tsaro sun ce sun dakile yunkurin da wasu kidinafas suka yi shekaranjiya da daddate, na tare hanyar Kaduna zuwa Abuja, kusa da Kakau. Jami’an sun ce kidinafas din yawancinsu sun tsere da harbin bindiga a jikinsu. Suka biya kauyen Maigiginya da ke yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, suka huce fuhinsu a can, suka kashe mutum biyu, Nasiru Yahaya da Isah Bature. Haka nan jami’an tsaron sun ce wasu kidinafas sun tare hanyar Zariya zuwa Funtuwa jiya da safe, aka fatattake su, aka ceto mutum biyu a hannunsu, aka kai su asibitin Shika.

Da nake wannan rubutun wuraren karfe uku da wasu mintoci na dare, ga jiniya can ina ji ta jami’an tsaro, watakila suna tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro.

Ana ci gaba da tofa albarkacin baki a kan wata ziyara da gwamnonin jam’iyyar APC karkashin shugaban jam’iyyar suka kai wa Jonathan har gida. Inda suka ce sun je yi masa HAPPY BIRTHDAY ne. Wasu masu korafin suka ce saboda su wadannan gwamnonin ne, talakawa suka dinga tsinewa Jonathan amma sai ga shi a yau Jonathan ya zama gwarzo da shi ake damawa a komai a gwamnatin APC.

Majalisar Dattawa ta nemi Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa jihohin da zanga-zangar #ENDSARS ta shafa da kashi daya cikin harajin tamanin kaya BAT. Sai dai a AF na rubutun yau, za a ga martanin da Sanata Shehu Sani ya mayar a kai.

A game da yajin aikin malaman jami’a, har yanzun tana kasa tana dabo domin akwai alamun wasu sabbin bukatun daga malaman, ciki har da bukatar majalisar dokoki ta kasa ta yi wata dokar da za ta hana manyan kasar nan kai ‘ya’yansu jami’o’i na kasashen waje karatu.

 

ALHAMIS

‘Yan Arewa daga sama zuwa kasa na ci gaba da korafi a kan matsalar tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a yankin Arewa.

Jama’a na ci gaba da korafin ga shi an kara kudin wuta, ga ba wutar. Talaka na ci gaba da biyan kudin zama a duhu, kuma duhun sai kara tsada yake yi.

Talakan Nijeriya, na ci gaba da korafin rayuwar sai kara tsada take yi, komai ya yi tsada.

‘ Yan Nijeriya na ci gaba da korafi a kan tsadar mai, tsadar da ta sanya komai ya yi tsada.

Gamaiyar kungiyoyin matasan Arewa, ta ci gaba da korafin saboda Sanata Ndume mutumin Arewa ne shi ya sa kotu ta tsare shi tun Litinin da ta gabata a kan Maina, har ma kotun ke shirin sayar masa da kaddarorinsa. Matasan suka ce ai ga su Aberibe nan da suka tsaya wa Kanu, har Kanu ya gudu ya kuma ci gaba da tsine wa Nijeriya da shugabanninta da buga gangar yaki, ba abin da aka yi wa wadanda suka tsaya masa, sai dan Arewa, da yake shi ne ba shi da gata a wannan gwamnatin. A yau kotu za ta saurari bukatar ba da belin Sanata Ndumen.

Talaka musamman na Arewa, na ci gaba da korafi a kan rufe bodojin kasar nan, kodayake gwamnati na shirin bude su nan gaba kadan, inda ake shirin mika wa shugaban kasa rahoton kwamitin da ya kafa a kan rufewar.

Dan Majalisar Wakilai daga jihar Kaduna na ci gaba da korafi a kan yadda kidinafas ke damun jami’ar E.BI.YU Samarun Zariya, har ya kawo shawarar a samar da kan iyaka, da ofishin ‘yan sanda da bataliyar soja a jami’ar.

‘Yan Majalisar Dokokin Kasar Birtaniya, na ci gaba da korafi a kan zargin jami’an tsaro na amfani da makaman yakin da har da ita Birtaniya ke tallafa wa a ba Nijeriya, ke kashe jama’a da makaman, zargi na baya-baya nan shi ne na Lekki. Birtaniya ta yi barazanar takunkumi, sai dai Gwamnatin Nijeriya na kokarin wanke kanta wajen Birtaniya.

‘Yan Majalisar Dattawa na ci gaba da korafi a kan yadda kidinafas ke iya amfani da waya, su yi ciniki har a biya su kudin fansa da waya, ba tare da an gano su ba. Saboda haka suka nemi Ministan Sadarwa Pantami ya je ya musu bayani, saboda sun ce ba su gane ba an yi yamma da kare.

Daliban jami’a na Nijeriya, na ci gaba da korafin sun gaji da zaman gida, iyayensu da marikansu, su ma suna ta korafi.

‘Yan PDP na jihar Adamawa na ci gaba da korafin Sanata Elisha Abbo ya cika wa rigarsa iska ya fice daga PDP ya koma APC.

Lauyan Maina na ci gaba da korafin Maina ba ya biyansa kudin aikin da yake masa, saboda haka ya janye daga yi masa aikin lauyanci.

Pele fitaccen dan wasan Birazil, na ci gaba da korafin Diego Maradona fitaccen dan wasan Ajantina, ya mutu ya bar shi, sai dai ya ce bai cire ran za su ci gaba da buga kwallon kafa a lahira ba.

‘Yan Nijeriya na ci gaba da korafi a kan yadda alkaluman masu kwaronabairos ke karuwa, su kuma ba sa ganin masu cutar ko matattun a zahiri.

Af! Ina shawagi a fesbuk sai na ga wata Salamatu Isah tana ci gaba da korafi a kan wasu matan aure kamar haka:

WALLAHI ! Wallahi !! Wallahi !!! Gaskiya daya ce ya za a ce mace da mijinta da yayanta amma take ta alfarmar auranta ta wulakanta auranta ta tozarta auranta da sunan taje wurin aiki SAI tayi sati ba ta kwana adakin mijinta yau ta kwana wurin wancan bayan ta gama bin yan fira Anya wannan abun kadai be ishemu ya hanamu zaman lafiya akasar nanba yanzu munkai lokacin da Mara aurema tafi me aure kamun kai ga hakkin miji ga na iyaye gana yaya. Wallahi Tallahi yanzu matan aure sun fi karuwai karuwanci Allah ya bamu ikon gyarawa inba hakaba to mudaina zagin shuwa gabanni sakamakon mummuna mummuna ne inji Manzan Allah S.A.W

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Babban Sinadarin Hade Zukatan Masoya Wuri Guda

Next Post

Matsayin Kananan Hukumomi A Matakin Cigaba Da kuma Tsaron Kasa

RelatedPosts

Kanun Labaru

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Lahadi 19 Zuwa Alhamis 23 Ga Jimada Ula 1442, Bayan Hijira  

by Muhammad
2 weeks ago
0

  LAHADI   Gwamnatin Tarayya ta dage hanin da ta...

Kanun Labaru

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 6 Zuwa Alhamis 9 Ga Jimada Ula 1442, Bayan Hijira

by Muhammad
4 weeks ago
0

LITININ Gwamnatin jihar Kaduna ta umarci ma'aikatanta kasa da matakin...

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 28 Ga Rabi’ul Sani Zuwa 2 Ga Jimada Ula 1442, Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 28 Ga Rabi’ul Sani Zuwa 2 Ga Jimada Ula 1442, Bayan Hijira

by Sulaiman Ibrahim
1 month ago
0

LITININ Mutanen Kankara ta jihar Katsina sun yi zanga-zangar a...

Next Post
Duka

Matsayin Kananan Hukumomi A Matakin Cigaba Da kuma Tsaron Kasa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version