Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya gana da ‘yan jarida na gida da waje a yau Juma’a, inda suka tattauna kan manufofin ketare da huldar waje na kasar Sin, a gefen taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14.
Wang, mamba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana cewa, an samu gagaruman sauye-sauye a shekarar 2024 a yanayin huldodin kasa da kasa.
- An Fara Gangamin Babban Taron LEADERSHIP Da Karrama Gwarazan 2024
- Karin Kudin Lantarki Da Na Kira: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shirya Zanga-zanga A Fadin Nijeriya
Ya ce, kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a fannin diflomasiyya a bara, har ila yau ya kara da cewa, kasar ta samar da kyakkyawan yanayi na huldar waje don samun ci gabanta mai inganci, da samar da kwanciyar hankalin da ake bukata a duniya mai cike da rikice-rikice, kana ta samu sabbin ci gaba mai inganci wajen gina al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama.
Wang, ya kuma bayyana cewa, kudurin diflomasiyya na kasar Sin bai sauya ba, yana mai cewa, kasar Sin tare da sauran kasashe za su ci gaba da kiyaye abin da ya fi zama daidai, da tafiyar da alkiblar zamaninmu, da kare daidaito da adalci na kasa da kasa, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Kana Wang Yi ya bayyana nahiyar Afrika a matsayin wuri mai muhimmanci a karni na 21, yana cewa, ba za a iya zamanantar da duniya ba tare da zamanantar da nahiyar ba. Ministan ya kara da yin kira ga kasashe masu tasowa su karfafa kansu, kuma su hada kai tare da neman ci gaba. Ya ce, kasashe masu tasowa su ne ke da ikon tabbatar da zaman lafiya da kyautata yanayin duniya.
Har ila yau Wang Yi, ya ce Sin da Amurka za su kasance a doron duniya na tsawon lokaci, don haka dole ne su nemi yadda za su yi zaman jituwa cikin lumana. A cewar Wang Yi, mutunta juna muhimmiyar ka’ida ce ta hulda kasashen biyu.
Da yake tsokaci game da matakin Amurka na sanya karin haraji kan kayayyakin kasar Sin bisa fakewa da batun Fentanyl, Wang Yi ya ce, bai kamata Amurka ta saka alheri da sharri, ko kuma kakaba haraji ba. Yana cewa, tu’ammali da maganin Fentanyl a Amurka, matsala ce da ya kamata kasar ta warware da kanta. Ya kara da cewa, ba zai yiwu a yi tunanin za a danne kasar Sin, sannan kuma a ci gaba da gudanar da kyakkyawar hulda da ita ba. Ya ce, jamhuriyar jama’ar kasar Sin na tsaye ne tsayin daka kan tabbatar da adalci a duniya, kana tana adawa da siyasar neman iko da babakere, yana cewa, “Mu a kasar Sin, mun yi imanin cewa, abota ta dindindin ce, kuma ya kamata mu nemi cimma muradunmu tare.”
Bayan haka kuma, Wang Yi, ya ce dabarar sanya shinge da kayyade fitar fasahohi, ba za iya dakushe ruhin kirkire-kirkire ba, kuma duk wanda yake raba gari ko kawo tsaiko ga tsarin samar da kayayyaki a duniya, kebanta kan shi yake yi. Wang Yi ya ce, bai kamata a yi amfani da kimiyya da fasaha a matsayin katangar karfe ba, kamata ya yi su zama arzikin da kowa zai amfana da shi.
Ya kara da cewa, a duk inda aka sanya shinge, an samu nasara, kuma a duk inda aka yi danniya, an kirkiro sabbin abubuwa.
Bugu da kari, yayin da ba a daina danne kasar Sin ba gaira ba dailili ba ta fuskar kirkire-kirkiren kimiyya ko samar da na’urar chip, hanyar da Sin ta dauka na zama mai karfi a bangaren kimiyya da fasaha na kara fadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp