A jiya Asabar 14 ga wata, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Araqchi.
Wang Yi ya bayyana cewa, a fili kasar Sin tana Allah wadai da matakin kasar Isra’ila, na keta hurumin kasar Iran a fannonin mulkin kai, da tsaro da kuma cikakken ‘yancin yankinta, tana kuma adawa da irin munanan hare-haren da ake kai wa jami’an Iran da fararen hula na kasar, kana kasar Sin tana goyon bayan Iran kan yadda take kokarin kare mulkin kai, da hakki da moriyarta, da tabbatar da tsaron jama’ar kasar.
- Babban Hafsan Soji Ya Ƙalubalanci Sabbin Sojoji Da Su Shirya Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda
- NAF Na Shirin Siyo Jiragen Yaki Masu Saukar Ungulu Daga Amurka
Wang ya ce, kasar Sin tana son ci gaba da yin mu’amala da Iran da dukkan bangarorin da abin ya shafa, da kuma ci gaba da taka rawa wajen sa kaimi ga sassauta yanayin da ake ciki.
A nasa bangare, Abbas Araqchi ya bayyana godiyarsa ga kasar Sin bisa yadda take fahimtar ra’ayin kasar Iran da nuna mata goyon baya, kuma ya yi imanin cewa, kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Sa’an nan, duk dai a jiya 14 ga wata, Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Isra’ila, Gideon Sa’ar. Bayan sauraron ra’ayin bangaren Isra’ila kan halin da ake ciki da kuma matsayin da kasar ke dauka, Wang Yi ya bayyana cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana ba da shawarar cewa, ya kamata a warware duk wata takaddama ta kasa da kasa ta hanyar tattaunawa da shawarwari, kuma tana adawa da amfani da karfin tuwo da takunkumi.
Bisa la’akari da haka, a fili kasar Sin tana adawa da matakin da Isra’ila ta dauka na keta dokokin kasa da kasa, inda ta kai wa kasar Iran hari, lamarin da ba za a amince da shi ba, musamman ma ta la’akari da yadda kasashe daban daban ke ci gaba da neman hanyar daidaita batun nukiliyar kasar ta Iran ta hanyar siyasa.
Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta bukaci Isra’ila da Iran da su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari, da lalubo bakin zaren kasancewa tare cikin kwanciyar hankali da lumana. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp