ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025

by Abubakar Abba and Sulaiman
6 months ago
Gona

Wata kungiya ta masu sayar da Kifin Tarwada (IDIPR Eriwe) da ke kauyen Ijebu Ode na jihar Ogun, ya bayyana yadda a shekara 2024, gonar ta sayar Tarwada ta kimanin Naira biliyan 4.5.

Gonar na da wuraren yin kiwon Tarwada kimanin 46, wanda ake gudanar da kiwonsu a karkashin shirin bunkasa kiwon Kifi da kuma rage talauci wato (DIPR), wanda aka saba yi a duk shekara, ake kuma samar da kimanin tan na Kifin.

  • Gwamnan Gombe Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Da ‘Yan Daba Suka Yi Wa Amadi Kasiran
  • Gwamnati Ta Yi Karin Haske Kan Biyan Tallafin Rage Radadi Da Mafi Karancin Albashi

Ana yin kiwon Tarwadar ne, a gonar da girmanta ya kai tsawon hekta 156, wadda kuma gwamnatin jihar ta Ogun ce ta samar da ita da ake ganin ta a matsayin gona mafi girma na kiwon wannan Tarwada a dukkanin fadin Afirka ta Yamma.

ADVERTISEMENT

Kazalika, an gina Tankunan ruwa na kankare guda 67 a gonar tare da kwami-kwamin kiwon Tarwadar kimanin guda 5,400.

Haka zalika, an kuma gina rijiyoyin burtsatse guda 2,720 da cibiyar zamani ta sarrafa Tarwada da kuma wasu injina na busar da Tarwadar da wutar sola mai aiki da wutar lantarki da kuma wasu famfuna da kuma wajen cin abincin Tarwadar na zamani.

LABARAI MASU NASABA

An Horas Da Masu Kiwon Dabbobi Dabarun Kiwon Zamani

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa

Bugu da kari, akwai kuma masu kiwon Tarwada a gonar da sama da su 600, wadanda aka rage yawan adadinsu daga 1,327 zuwa 600, bayan bullar cutar annobar Korona, saboda kalubalen ci gaba da gudanar da sauran ayyukan gonar.

A shekarar 2024, masu kiwon Tarwadar a gonar; sun samar da Tarwadar da yawanta ya kai kimanin tan 1,700, wadda kuma aka kiyasata cewa; kudinta ya kai na Naira biliyan 4.5.

Wannan ba karamin ci gaba ba ne, musamman duba da cewa; gonar ta kasance abin koyi ga sauran kungiyoyin da ke kiwon Tarwada a daukacin fadin wannan kasa.

Bisa wannan nasarori da gonar ta samar, hakan ya nuna yadda take ci gaba da samun yabo daga kasashen duniya, cikin masu yabon har da Hukumar Bunkasa Samar da Abinci da Habaka Aikin Gona (FAO) da kuma wani yabon daga wurin sauran hukumomin kasa da kasa da ke tallafa wa fannin.

Ya zuwa yanzu, Hukumar ta FAO; ta wanzar da wani aiki na kiwon Kifi da ake kira da ‘FISH4ACP’, wanda kuma Tarayyar Turai (EU) da Gidauniyar Giz ke zuba kudade a cikin aikin, musamman domin tabatar da ganin an samar da damar samun kudade da taimakawa wajen gudanar da yin bincike a fannin.

Babban Jami’in gudanar da aikin ‘FISH4ACP’ da ke Hukumar ta FAO, Dakta Abubakar Usman ya bayyana cewa; an samu kyakkyawan sakamako a binciken da aka gudanar, wanda kuma har yanzu ake ci gaba da amfana da shi sakamakon binciken, musamman ganin cewa; bincken zai taimaka wajen rage kalubalen da ake fuskanta na tsadar abincin ciyar da Tarwadar zuwa sama da kashi 20 cikin 100.

Shi kuwa, babban shugaba a shirin nan na IDIPR, Marcus Adeniyi, a tattaunawar da aka yi da shi a gonar da ke kauyen Eriwe a Ijebu Ode, ya sanar da cewa, kungiyar ta masu kiwon Tarwadar; na kara tumbatsa ne matuka.

Ya sanar da cewa, duk yawan Tarwadar da aka sayar, ana tura kudaden cinikin ne kai tsaye zuwa ga asusun ajiyar kudade.

A cewar Adeniyi, Tarwadar da ake da ita a yanzu a gonar; ta kai ta kimanin Naira biliyan shida, inda ya kara da cewa; bisa bayanansu a zango farko na shekarar 2025, an sayar da Tarwada sama da tan 600.

“Idan har a shekarar 2024, mun samar da tan 1,700 na Tarwada, wadda kudinta ya kai kimanin Naira biliyan 4.5, a wannan shekarar ta 2025, muna sa ran adadin zai zarta wannnan; wanda zai iya kai wa kimanin Naira biliyan shida,” in ji Adeniyi.

Kazalika, ya bayyana cewa; muna sa ran samar da yawan Tarwadar da za ta kai sama da tan 2000, kafin karshen shekarar 2025.

Bugu da kari, ya bayyana cewa; kungiyar a kowane zango daya na shekara, tana shirya wa masu kiwon Tarwadar horo na musamman, inda sabbin shiga cikin kungiyar ke biyan Naira 2,500, domin yin rijista da su.

Ya ce, kungiyar na raba wa ‘ya’yanta wuraren kiwon Tarwadar, inda ake cazar su Naira 15,000.

Kazalika, bayan mai kiwon ya samar da Tarwada ta farko, kungiyar za ta ba shi, rancen Naira miliyan biyu, inda rancen zai kasance kashi 18 cikin 100 na kudin ruwa, har zuwa karshen shekara daya.

Shi kuwa, wani mai kiwon Tarwadar mai suna Oyinade Matthew Adeneye, wanda kuma yake tafiyar da Kwamin kiwon Tarwadar guda sha biyu, wanda kuma tun a shekarar 2008 yake yin kiwon a yankin ya sanar da cewa; yanzu haka; yana da sama da Tarwada 30,000 wadanda kuma suke kan matakai daban-daban.

A cewarsa, aikin na ‘FISH4ACP’, zai taimaka wajen karfafa samar da ilimin yadda za a rika kula da kiwon Tarwada da kuma magance kalubalen da masu kiwon ke fuskanta na rashin samun riba mai yawa.

Adeneye ya ci gaba da cewa, aikin zai kuma samar da sauyi a fagen kiwon na Tarwada tare kuma da samar da damar samun rancen kudaden yin kiwon.

Manufar aikin na ‘FISH4ACP’ dai, zai kasance wajen bayar da gudunmawar ci gaba da kiwon Tarwadar da kuma samun kudaden shiga.

A yanzu haka, ana gudanar da wannan aiki a kasashe sha biyu, inda ake gudanar da aikin a kasashe tara da ke Nahiyar Afirka biyu, a kuma yankin Caribbean, daya kuma a tekun Pacific, wanda aka zuba kimanin Yuro miliyan 40 tare da kuma karin wasu kudade daga Gwamnatin Kasar Jamus.

A bangaren Nijeriya kuwa, an mayar da hankali ne a fannin na kiwon Tarwada, domin samun riba; wanda kuma aka wanzar da aikin a shiyoyin siyasa shida na fadin kasar nan.

Jihohin da aka wanzar da ayyukan su ne, Jihohin Kudu Maso Yamma, inda ake wanzar da aikin a Jihar Ogun, sai kuma a Kudu Maso Kudu da ake wanzar da aikin a Jihar Delta.

Sauran su ne; Kudu Maso Gabas da kuma Arewa Ta Tsakiya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Abubuwa Biyar Game Da Kiwon Talotalo
Noma Da Kiwo

An Horas Da Masu Kiwon Dabbobi Dabarun Kiwon Zamani

December 20, 2025
Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa
Noma Da Kiwo

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa

December 19, 2025
Kiwon Dabbobi Da Fasahar Kimiyyar Zaman
Noma Da Kiwo

Kiwon Dabbobi Da Fasahar Kimiyyar Zaman

December 14, 2025
Next Post
Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA

Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne - HJRBDA

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.