Wani yaro karami dan shekara 12 ya harbe tare da hallaka mahaifiyarsa ‘yar Nijeriya mai suna Ayobiyi Cook, kodayake da farko yaron ya so boye gaskiyar abun da ya faru, a cewar hukumomin a kasar Amurka.
Ofishin Jefferson County Sheriff da ke Alabama ya ce a ranar Litinin jami’ansa sun fara gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar wata mace mai shekara 29 a Forestdale da ke Alabama.
A lokacin binciken, masu binciken sun gano cewa dan Cook mai shekara 12 a duniya (ba a bayyana sunansa ba) ya ciro bindiga ba da gangan ba inda ya bude wa Mamarsa wuta tare da kasheta.
“Yaron ya kirkiri labari da masu bincike suke ganin hakan ba zai faru ba,” a cewar sanarwar ofishin Sheriff.
“Amma daga baya yaron ya yi bayanin hakikanin abun da ya faru.”
Masu bincike sun ce hujjoji ya nuna cewa harbin da yaron ya yi ba bisa gangan ya yi ba.
Yaron wanda ya tare da iyalansa har yanzu an ce kotun kula da tsarin iyali ne zai kula da kes din.
Bayanan farko da sashin binciken ya fitar, ya ce babu wani alamar fita da karfi a gidan lokacin da suka je inda abun ya faru, sai dai wani ya gudu daga gidan bayan an kira lambar 911.
Mijin matar mai suna Djuan Cook, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa za a bisne matar a ranar 12 ga Agustan.
A 2022 zuwa yanzu, yara sun yi harbin ba na gangan ba har guda 169 kamar yadda wata cibiya mai fadakarwa kan illar amfani da bindiga ba bisa ka’ida ba wato Everytown for Gun Safety ta shaida.
Harbe-harben yaran ya janyo mutuwar 74 a jikkata 104 a Amurka a cikin wannan shekarar.
A shekarar 2021, harbin da ba na ganganci ba guda 392 ne aka samu rahoton faruwarsu a Amurka da ya janyo mutuwar 163 da jikkata wasu 248.