Blog: Shafin Intanet ne da yake bukatar sabuntawa (regular updates). Zai iya kasancewa mallakin mutum daya ko mutane biyu ko fiye, wajen ba shi kulawa da wallafa sababbin ayyuka.
Kusan shafukan Blog sun mamaye kaso mai girma a Intanet. Ana iya tsara shafin blog a kan kowane irin al’amari domin yadawa a duniya baki daya.
Business Website: Shi kuma wannan shafin na kasuwanci ne, kuma shi ne ya maye gurbin shaguna ko kasuwannin mu na zahiri a Intanet, tamkar duniya a tafukan hannunmu.
Shi ne hanya mafi sauki wajen bayyana wa duniya irin abubuwan da mutum yake sayarwa, hanya ce ta jan hankalin abokan hulda daga sassan duniya baki daya. Ana sanya cikakken adireshi, cikakken bayani a kan sana’a ko kasuwanci komai kankantarsa a idon duniya da sauran su… Kuma shi ma ana sabunta shi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Brochure Website:
Shi ma wannan nau’in shafin Intanet ne da ya kunshi bayanan kasuwanci, musamman na kananan ‘yan kasuwa. Bayanan cikinsa takaitattu ne, wadanda basu gaza adireshi ba, da kuma jerin sunaye da hotunan kayayyaki, sannan kuma ba a sabunta shi kamar wadanda na bayyana a sama. Shi yana daga cikin rukunan shafukan intanet masu lakabin STATIC WEBSITE. Kuma darajarsa ba ta kai na Business website ba.
SITE123 – Wannan shafi suna da tsari na musamman wajen taimakawa mutane masu sha’awar bude shafukan blog. Suna nuna faifan bidiyo a kan yadda mutum zai bude blog.
GoDaddy – Wannan za a iya cewa sabo ne. Amma yana da tsarin taimako wajen bude shafin blog da sauran su.
Kowanne za a iya amfani da shi wajen bude shafin blog. Za ku iya ziyartar kowane domin ganin yadda tsarinsu yake.
Bincike ya bayyana cewa a kullum ana kirkirar ko bude sababbin shafukan Intanet (new websites) a kalla guda 380 a kowane minti daya, wato kimanin shafuka guda 6 kenan a kowace dakika guda.