Abdulfatah Hassan" />

Wasu Shugabannin Da Suka Gabata Ne Suka Janyo Wa Nijeriya Matsala –Dakta Bature, MON

DAKTA BATURE ABDUL’AZIZ, MON shi ne shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya, a wannan wata tattaunawa da ya yi da ABDULFATAH HASSAN ya yi tsokaci ne dangane da cikar Nijeriya shekaru 58 da samun ‘yancin kai. Inda ya lissafo wasu daga cikin matsalolin da Nijeriya ke da su, da kuma wadanda suka haifar mata da su. ga yadda hirar ta kasance:

Me Dakta zai ce dangane da cikar Nijeriya shekara 58 da samun ‘yanci?

Da farko dai muna taya Nijeriya murnar cika shekara 58 da samun ‘yancin kai. Kuma muna rokon Allah ya tabbatar da Nijeriya a matsayin kasa daya al’umma daya, har zuwa cimma nasara.

Wadanne nasarori aka samu daga lokacin da aka samu ‘yanci zuwa yanzu?

Daga 1960 zuwa yanzu an samu ci gaba da nasarori, gaskiya ne cewa an yi shugabanni irinsu Sa Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello, sun wuce. An kuma samu wadanda su suka fara kawo juyin mulki a Nijeriya. suka yi musu Juyin mulki, wani wanda ake ce masa Ironsi, wanda shi ma ya zo kafin wata takwas da yake abu ne na zalunci da cin amana, shi ma aka yi mishi juyin mulki aka nada Janar Gowon. Alhamdulillah, a takaice dai bayan Goyon ya sauka, Murtala ya zo, bayan Murtala sai Shagari ya zo. Daga nan kuma Buhari ya zo a matsayin soja. Bayan Buhari Babangida, sai Shonekan, Abacha, Abdussalam. Sai kuma Obasanjo lokacin da aka dawo mulkin farar hula.Wanda a mulkin Soja bayan da aka kashe Murtala, Obasanjo ne ya amsa ya shekara uku. Daga Obasanjo sai Yar’aduwa, sai Jonathan sai kuma Buhari a yanzu.

Toh Alhamdu lillahi duk shugabannin nan da aka yi wadanda na lissafa akwai wadanda yake ‘yan kishin kasa ne, akwai kuma wadanda suke ‘yan kishin kasa ne amma sun dan so kansu kadan, akwai kumawadanda suke ‘yan son mulki ne kawai, su kawai abin da za su samu shi ne hadafinsu. Su masu kishin kasa sun eke da burin gina Nijeriya. Su kuma marasa kishin kasa su ne masu rushe ginin da ‘yan kishin kasa ke yi.

A yanzu ba ma a Nijeriya ba, duk Afirka babu mau kudinsu saboda satar da suka yi. Amma dai jinni ba ya maganin kishi. Nijeriyar nan kasa ce mai albarka, komi muna da shi a karkashin kasa, tun daga man fetur, da karafa da su kuza da sauransu. ga ta shimfidaddiyar kasa, kasar noma.

Ni tunda nake yawo ban taba ganin kasa irin Nijeriya mai shimfidaddiyar kasa ba. wasu kasashen sai ka gansu da tulin duwatsu da sauransu. Amma Nijeriya kuwa bah aka bane, don muna kyakkyawan wuraren noma.

Duk da wadannan albarkatu da kasarmu ke da su, me ke kawowa Nijeriya Cikas?

Wannan ba ya rasa nasaba da wadanda suka shugabance mu, su ne suka jefa kasar nan cikin wani hali. Zan iya rantsewa, a iya abin da na sani, kasashen da suke sa’o’in Nijeriya ne wanda suke sun tasarwa 20, a yanzu sun taso sun bar Nijeriya nesa ba kusa ba. Alal misali, na je Saudiyya, indai tattalin arziki ne na san lokacin da Saudiyya ba ta fi Nijeriya ba. Na je Thailand, Dubai, Indonesia, Malaysia, Taiwan, Chana, Indiya, Hongkong, Pakistan, Iran da sauransu. Wadannan duk a da Nijeriya ta fi su, amma yanzu ba za ka soma hada Nijeriya da su ba. duk sun wuce mu.

Me ya janyo mana haka?

Shugabanni ne da aka yi a baya suka janyo mana wannan. Yau Nijeriya mu ne koma baya. Na san lokacin da Nijeriya ta mallaki jirgin sama 30 da wani abu, amma saboda rashin kishin kasa, akwai Shugaban da ya zo gabadaya ya sayar da jirage guda tara, aka kada gwanjonsu aka sayarwa da Kasar Holland. Wanda a yanzu sun gyara su, sun mayar da su sababbi. Kudin kwaya daya sai ya biya kudin guda taran nan. Kuma lokacin muna sane, babu inda jiragen kasa ba su yawo. amma sai da aka wayi gari kan jirgin da muke da shi bai kai guda shida ba, wanda a da ana da sun kai 60.

Idan aka duba aikin gona, ana kawo kayan amma saboda son rain a siyasa sai ka ga wannan kaya an dauki mutum daya an ba shi tan dari biyar, tan 1,000. Kuma ba manomin bane. a takaice hanyoyin zalunci da son turmutsar da kasa iri daban-daban.

Sannan a lokacin wani daga cikin tsoffin shugabannin kasan ne kuma aka kirkiri siyo man fetur a shigo da shi kasar nan. Mu fa a Afirka mu ne na daya, amma sai aka wayi gari muna da manyan matatun man fetur, akwai a Kaduna da Jos da sauransu. A takaice duk wadannan matatun man fetur sai da aka durkusar da su. A ka koma ana shigo da man fetur din daga kasashen waje. Sai aka koma kawo man fetur din ta jirgin ruwa. Abin haushin ma sau da yawa idan jiragen suka zo, sai a juyar da su ba tare da an shigo da su kasar ba, amma a lissafi an shigarwa da Nijeriya cewa an kawo man fetur din.

Sannan kuma akwai lokacin da wutar lantarki ta wadata a Nijeriya, gabas da yamma, kudu da arewa, amma wadancan Shugabanni da suka gabata ne suka yi ta jan lamarin wutar lantarkin baya. a takaice dai har zuwa irin tabarbarewar da fannin yayi a yanzu da Buhari ya amshi kasar nan. Akwai wanda ya amshi sama da Dala miliyan 16 da sunan gyaran kudin wuta. Ya amshi sama dad ala biliyan 35, wanda ba a san ina ya kai su ba. Durkushewar wutar lantarki shi ke haifar da macewar masana’antu da sauransu. Wannan kuma ya haifar da rashin aikin yi a fadin kasar.

Haka kuma idan ka duba makudan kudaden da aka fitar domin yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabashin Nijeriya, shi ma abin da ban tsoro. Dala Biliyan 40 aka ware, amma irin wadancan Shugabanni ne suka wawushe wadannan kudade.

Wadannan su ne dalilan da suka hana mu samun ci gaba, suka kare mu daga kai wa ga nasara. amma a yau su ne suka fi kowa ihun kasa na cikin talauci, bayan akwai daya daga cikinsu da shi ne ya fi kowa sayar da kadarorin Nijeriya. shi yayi ta karyar da su yana siyarwa wadanda yake tare da su. Ina fatan Shugaban Kasa Buhari zai bi wadannan kadarori duk a dawo da su, wadanda su kadai ma sun takura tattalin arzikin Nijeriya.

Mene ne kiranka ga ‘yan Nijeriya?

Tunda yanzu Allah ya bamu shugaba tsayayye mai kishin kasa, mu ba shi hadin kai da goyon baya.

Exit mobile version