ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wataƙila Messi Ba Zai Halarci Bikin Ronaldo Ba

by Abba Ibrahim Wada
1 month ago
messi

Duk da cewa har yanzu ba a fitar da jerin sunayen waɗanda aka gayyata ba. Haka kuma ba a sani ba ko Lionel Messi, wanda ya daɗe yana gogayya da Ronaldo kan kambun Ballon d’Or, yana cikin waɗanda aka gayyata. Amma kuma Ronaldo bai halarci bikin auren Messi ba a bikin da aka yi a ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2017 a Argentina.

Kamar yadda kafofin yaɗa labarai suka bayyana, Rahotanni sun bayyana, ɗan wasa Cristiano Ronaldo na shirin auren abokiyar zamansa Georgina Rodríguez bayan kusan shekara goma da suka shafe tare.

An yi wa Ronaldo da Georgina baiko kwanan nan, bayan shekaru ana ta hasashen yaushe ne za su yi aure. Ma’auratan sun shafe kusan shekara goma tare kuma suna da ƴaƴa tare. A baya Ronaldo ya taɓa cewa zai yi aurensa ne bayan gasar cin kofin duniya, domin yana fatan ya lashe kofin kafin ya yi aure. Sai dai hakan bai samu ba kuma hakan ba zai hana yin auren ba, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

ADVERTISEMENT

Ana sa ran Ronaldo zai gudanar da gagarumin bikin auren ne a mako mai zuwa kuma  za a yi bikin a garin Funchal da ke tsibirin Madeira na ƙasar Portugal, inda aka haifi Ronaldo. Har ila yau, za a ɗaura auren ne a babban Cocin Cathedral Church da ke Funchal.

Kamar yadda rahotanni suka fara fita, ana sa ran shahararrun mutane daga sassa daban-daban na duniya, kafofin yaɗa labarai da manyan attajirai za su halarci bikin, an kuma kulle otal ɗin alfarma na Saɓoy Palace domin bikin, sannan kuma za a rufe shi na tsawon kwana biyu daga ranar Asabar 8 ga watan Agusta.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Amma kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa Ronaldo mai shekara 41 da Georgina mai shekara 32 sun riga sun yi aure a asirce a bara, sai dai Ronaldo bai tabbatar da hakan ba duk da cewa a baya an sha yi masa tambayar.

Tun bayan rabuwar Cristiano Ronaldo da tsohuwar budurwarsa, Irina Shayk, Georgina Rodríguez ta zama abokiyar rayuwarsa, lamarin da ya ja hankalin duniya. Ronaldo ya taɓa bayyana a wata hira da Piers Morgan cewa yana matuƙar son Georgina kuma yana son su yi rayuwa tare har ƙarshen rayuwarsu.

A wani bikin ranar haihuwarta, ya haskaka wasu manyan gine-gine a Dubai da hotunanta domin nuna irin ƙaunar da yake mata. Kafin Georgina, Ronaldo ya shafe shekara biyar yana soyayya da fitacciyar ƙwararriyar mai tallan kayan sawa ta Rasha, Irina Shayk.

Mutane da dama sun fassara wannan a matsayin cewa babu yiwuwar su sake komawa tare. Sannan ana kuma cewa Ronaldo ba ya da halin komawa ga macen da ya taɓa rabuwa da ita. Haka kuma an ce baya son zama da macen da ba ta girmama mahaifiyarsa.

Mutane da dama sun daɗe suna tambayar ko wace ce Georgina. A wani shiri game da rayuwarta, ta ce mafi yawan mutane sun san sunanta amma ba su san ainihin ko wace ce ita ba. Georgina Rodríguez abokiyar rayuwar Cristiano Ronaldo ce, mai tallan kayan sawa, tsohuwar mai rawa kuma fitacciyar mai tasiri a kafofin sada zumunta. Tana da sama da mabiya miliyan 44 a Instagram, o da yake tana da takardar zama ƴar Sifaniya. An haifi Georgina ne a Buenos Aires na Argentina, daga baya ta taso a birnin Jaca da ke Arewacin Sifaniya. Jaca na da tazarar kusan kilomita 450 daga birnin Madrid, kuma ƙaramin gari ne kusa da iyakar Faransa mai yawan jama’a kusan dubu 13,000.

A lokacin tana aiki a matsayin ma’aikaciyar kula da baƙi. Jaridar wasanni ta AS ta ce Ronaldo da Georgina sun haɗu ne a wani shagon Gucci da ke birnin Madrid. A lokacin Georgina tana aiki a matsayin mai tallace-tallace a shagon, yayin da Ronaldo ke buga wasa a Real Madrid.

A cikin shirin rayuwarta, Georgina ta ce tsarinsa, jikinsa da kyawunsa sun ja hankalinta nan take. Kuma ta ci gaba da cewa za ta iya cewa ta ƙaunace shi tun daga lokacin.

A lokacin Georgina tana zuwa aiki ne da motar haya saboda ba ta da mota, kuma wani lokaci ba ta da kuɗin sufuri. Bayan Ronaldo ya san hakan, ana cewa ya kan kai ta aiki da motocinsa masu tsada, lamarin da ke sa tsofaffin abokan aikinta su fito waje domin kallon motocin.

Ba da jimawa ba, dangantakarsu ta bayyana ga jama’a, kuma masu ɗaukar hoto suka fara bibiyar su. A shekarar 2016 ma an ga Ronaldo yana sanya gashin ƙarya da tabarau domin ka da mutane su gane shi.

Ana yaba wa Georgina saboda kulawar da take bai wa ƴaƴan Ronaldo. Tana da kyakkyawar alaƙa da babban ɗansa, Cristiano Jr., kuma ana yawan ganinta tare da shi a filayen wasanni suna kallon wasannin Ronaldo.

Mutane da yawa na ganin girmamawa da ƙaunar da take nuna wa iyali ne ya sa Ronaldo ke matuƙar daraja ta. An haifi Cristiano Jr. a Amurka a shekarar 2010, amma har yanzu ba a bayyana ko wace ce mahaifiyarsa ta haihuwa ba.

Ronaldo ya ɓoye wannan sirri, yayin da mahaifiyarsa Dolores da Georgina suka taka muhimmiyar rawa wajen kula da ɗan nasa har kawo wannan lokacin kuma shima matashin yaron yana buga ƙwallo kamar mahaifinsa.

messi
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Hajji 2026: Kano Za Ta Fara Jigilar Maniyata Ranar 14 Ga Mayu

Rashin Miƙa Fasfo A Kan Lokaci Na Iya Sanya Alhazai A Kano Rasa Kujerun Aikin Hajji

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.