Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, ta ce wani mutum ya samu raunuka bayan da wani abu da ake zargin wayar hannu ce ta fashe a wani gidan mai mai zaman kansa da ke garin Badagry na Jihar.
Babban jami’i da ke kula da reshen hukumar na Badagry, Abel Husu, ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) faruwar lamarin.
- Wani Ya Yi Alkawarin Auren Matashiyar Da Aka Yi Wa Sanadin Rasa Kafa A Sakkwato
- Allah Ya Yi Wa Hakimin Rimi A Masarautar Katsina NUHU ABDULKADIR Rasuwa
Ya ce hukumar tasu ta samu labarin abin da ke faruwa ne a gidan man Yemoral Oil and Gas Petrol Station da ke kan hanyar Ajara a Badagry da misalin karfe 8:55 safiyar ranar Litinin.
Ya ce jami’ansu sun isa gidan man bayan minti 10 da samu rahoton kuma nan take suka fara kokarin kashe gobarar.
“Bincikenmu ya tabbatar cewa wani direban mota ne ya haddasa gobarar, bayan da ya riga ya sayi man fetur a cikin motarsa”.
Ya kuma ce “Bayan da mai motar ya tayar da injin motar sai ta yi bindiga, inda gobara ta tashi nan take”.
Sai dai ma’aikata a gidan man sun shaida wa NAN cewa wani mutum ne ya yi sanadin gobarar bayan da ya amsa wayarsa a daidai lokacin da ake zuba masa fetur cikin wata jarka.
Gidajen mai na saka alamar hana amsa waya a lokacin da ake zuba wa mutum man fetur, wanda watakila hakan na da nasaba da irin wannan lamarin.