Duk da cewa wuta ta kasancewa aba ce da galibin dan Adam ke daukarta a matsayin abokiyar gaba, idan aka sa tabarau na hangen nesa ta fannoni da dama ta kan zama ni’ima ga rayuwa. A sanadiyyar ta ana iya sarrafa abubuwa da dama ta bangaren abinci, masana’anta (musamman gidan burodi) da kuma sauran kamfanonin da ke sarrafa karafa. To, sai dai duk da amfanin da wutar ke yi, akwai sassan da koda wasa aka ce za a yi amfani da ita ta kan haifar da gagarumar barna.
Daya daga cikin irin wadannan sassan shi ne muhalli wadda ya ke kunshe da tsirrai, dabbobi da shi kansa dan Adam da sauran halittun Allah da walau ido na iya ganin su ko ba ya iyawa. Tun ba yau ba, musamman a Nijeriya da zaran yanayi na rani ya kankama za ka ga dazuzzuka na ta ci da wuta babu kakkautawa. Irin wannan mummunar dabi’a tana haifar da dimbin asarar dukiya har ma wani sa’in ta kai ga rasa rayuka.
An sha ba da rahotannin cewa wutar daji ta yi sanadiyyar asarar amfanin gona ko kuma idan aka yi rashin sa’a a ji cewa ta yi sanadiyyar gobara a kauyuka musamman wadanda su ke yin dakuna na ciyawa da bukkoki inda hakan kan sa mutanen da ke cikin wadannan wuraren musamman mata da yara kan tsallaka rijiya da baya (idan kona su kawai wutar ta yi ta bar su da ransu) ko kuma ma lamarin ya kai ga mutuwa bakidaya.
Wani karin abin ban takaici game da wutar dajin shi ne hatta a wuraren da su ke da saurin hadarin yaduwar wutar za ka ga an bar ta tana ci bal-bal. Kowa ya san hanyar Kaduna zuwa Abuja ta shahara wurin ci da wuta da zaran yanayi na rani ya kankama. irin wannan sakaci yana da matukar hadari kasancewar hanyar ba ta rabuwa da zirga-zirgar motoci ciki har da tankunan dakon man fetur, gas da kananzir. Sai ka ga da zaran mota ta dan yi wani layi ta sauka kan titi koda ba ta fadi ba sai ta kama da wuta saboda gefen titin yana ci da wuta ko kuma akwai ragowar hayakin da aka cinna wutar.
Har ila yau, daga cikin amfanin gonan da ake nomewa akwai wadanda tilas sai an jira rani ya shiga sosai kafin a girbe musamman irin su dawa, dauro, gero, maiwa da wake. Abin bakin ciki! A sa’ilin da ake jiran girbe wadannan amfanin gona tare da kaiwa gida ko kasuwa sai a cinna wa daji wuta, ta haka sai ka ga wutar ta kone amfanin gonan kurmus, manomi ya tashi a tutar babu duk da irin wahalhalun da ya sha na noma. Irin wannan rashin imani da me ya yi kama?
A gaskiya ya kamata gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wurin shawo kan wannan abin ban takaici su mike tsaye wurin lalubo bakin zaren warware wannan matsala. Wutar dajin nan ba a Nijeriya kadai ake samunta ba (koda ya ke na sauran kasashe ta sha bamban da ta Nijeriya, saboda ta Nijeriya da gangar mutane ke cinna ta, ta kasashen kuwa a kan rasa ainihin ummul’haba’isin tashinta). Idan hakan ta faru a wasu kasashe, su kan tura jami’an kashe gobara su yi ta yin aiki babu dare, babu rana har sai sun kawo karshenta. Me ya sa a Nijeriya ba za a yi haka ba?
Har ila yau, galibin masu cinna wutar kananan makwaidata ne masu farautar berayen daji. A hada hannu da sarakuna musamman na yankunan karkara wurin zakulo su a hukunta su, sannan jami’an ma’aikatun kare muhalli su rubanya kwazo wurin bullo da sabbin dabarun kare muhalli. Tabbas yin hakan zai taimaka a yi wa guru hanci kan matsalar amma ba a bar dukan jaki, ana dukan taiki ba!