An gudanar da taron kasa kan batun kiwon lafiya a nan birnin Beijing, daga ranar 12 zuwa 13 ga watan nan. Kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tare da gabatar da jawabi.
A cikin jawabin nasa shugaba Xi ya jaddada cewa, lokacin aiwatar da “shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15”, lokaci ne mai muhimmanci na cimma burin gina Sin mai lafiya nan zuwa shekarar 2035, kuma dole ne a nace ga bin hanyar ci gaban kiwon lafiya mai halayyar musamman ta Sin, da aiwatar da manufofin kiwon lafiya a sabon zamani, da kuma ingiza ci gaban ingantattun hidimomin kiwon lafiya. Kazalika, a karfafa matakin kula da lafiyar jama’a, da tabbatar da samun ci gaba na a zo a gani a wannan bangare.
Xi ya kuma nuna cewa, lafiyar jama’a wata muhimmiyar alama ce ta ci gaban al’umma da karfin kasa. Tun daga babban taron JKS karo na 18, kwamitin kolin JKS ya dora muhimmanci matuka kan aikin kiwon lafiyar jama’a, ya tsara manufofin aikin kiwon lafiya na sabon zamani, kana da yanke babbar shawara kan raya sha’anin tabbatar da lafiyar jama’ar Sin.
Ban da wannan kuma, ya ingiza gina tsarin kiwon lafiya da na maganin gargajiya, da na rigakafi da kula da cututtuka, da tsarin inshorar lafiya mafi girma a duniya, matakin da ya sa aikin kiwon lafiya ya samu gagaruman nasarori a kowane fanni. (Amina Xu)














