Shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun tattauna tare da shan shayi da shugaban kasar Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania Trump. Shugabannin kasashen biyu sun kuma amince da gina muhimmiyar dangantaka mai ma’ana bisa girmama juna da adalci da musaya.
Xi Jinping ya jaddada cewa, makomar dangantakar Sin da Amurka na da haske, wanda ke alamta wani yanayi da ba za a iya gujewa ba. A lokaci guda kuma, hanyar kyakkyawar makoma na cike da kalubale da wahalhalu daban-daban. Kuma da ma hakan ya dace da yanayin samun ci gaban komai. Ya ce, a shirye yake ya hada hannu da shugaba Trump, cikin kuzari da sanin ya kamata, domin hada hannu wajen rubuta kyakkyawan babi a tarihin dangantakar Sin da Amurka.
A cewar Donald Trump, ziyarar aiki ta shugaba Xi a Amurka tana tattare da ma’ana da nasara. Kuma bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi kan dangantakar kasashensu da manyan batutuwan kasa da kasa da na yankuna. Ya ce yana sa ran ci gaba da tuntubar juna da shugaba Xi, domin hada hannu wajen jagorantar raya dangantakar Sin da Amurka.
Bayan tattaunawar da suka yi yayin shan shayi, Xi da Peng Liyuan sun ziyarci Cibiyar Adana Bayanai ta Amurka tare da shugaba Trump da uwargidansa.
A cewar shugaba Xi, sama da shekaru 250 da suka gabata, Amurkawa sun yi gwagwarmayar cimma burin gina babbar kasa, mai wadata da kyau a nahiyar Amurka ta Arewa. Su kuma al’ummar Sinawa, sun daukaka al’adunsu na gargajiya, kuma suna ci gaba da samun sabbin nasarori a tafarkin cimma burin kasar na farfadowa.
Sin da Amurka kasashe ne da ke da bambancin yanayi. Sai dai duk da bambancin tarihi da al’ada da yanayin zamantakewa da tafarkinsu na neman ci gaba, al’ummomin kasashen biyu na da buri guda na samun kyakkyawar rayuwa. Ya ce amincewa da girmama bambance-bambancen da ke akwai tsakaninsu, da karfafa fahimta da koyi da juna da neman yanayi mai dacewa na hulda a tsakaninsu da fadada jerin bangarorin hadin gwiwa da tafiyar da bambancinsu yadda ya kamata, za su taimaka wajen samun kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu da dorewarta. (Fa’iza)














