Hukumar kula da ma’aikatan Gwamnatin Jihar Bauchi (BSCSC) da dakatar da Abdulkadir B. Aliyu, wani babban Sufeto na hukumar kashe gobara (Higher Fire Superintendent) daga bakin aiki sakamakon samunsa da laifin sata da rashin ɗa’a.
Aliyu wanda ma’aikacin hukumar kashe Gobara ta Jihar ne an turasa aiki a sashen kashe Gobara na ma’aikatar ayyuka da sufuri na jihar inda aka same shi da laifin satar takalman mutane a lokacin da suke yin sallloli a Babban Masallacin Sakatariyar gwamnatin jihar wato ‘Abubakar Umar Secretariat da ke Bauchi.’
A wata sanarwar da kakakin hukumar Saleh Umar ya fitar a jiya, ya ce, an ɗauki matakin ne a yayin zaman majalisar hukumar karo na 32.
Hukumar ta ce an sallami Aliyu ne bayan an bi dukkan matakan ladabtarwa da dokoki da ƙa’idojin Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Bauchi (PSR) suka tanada.
A cewar sanarwar, laifin ya saɓa wa dokar PSR mai lamba 0312 (ix da xii) da ta shafi rashin ɗa’a.
Hukumar ta kuma bayyana cewa a baya an taɓa bai wa Aliyu takardar gargaɗi a ranar 29 ga Satumba, 2025, saboda barin wurin aikinsa ba tare da izini ba, sannan an tuhume shi da sakaci wajen gudanar da aiki bisa dokar PSR mai lamba 0312, sashe na 4.
A wani ɓangare kuma, hukumar ta amince da ɗaukan aikin Abdulkadir Lamaran Gidado a matsayin jami’in tsare-tsare da Imran Lamaran Gidado a matsayin Jami’in Kasuwanci dukansu a matakin albashi na 8.
An tura Abdulkadir Gidado zuwa ma’aikatar kasafi, tsare-tsaren tattalin arziki yayin da aka tura Imran Gidado zuwa ma’aikatar kasuwanci, masana’antu da zuba hannun jari.
Hukumar ta kuma amince da tabbatar da aikin Hadiza Mohammed a matsayin mataimakiyar darakta, a matakin albashi na 15, bisa kwantiragi, ƙarƙashin hukumar kula da makarantu na musamman.
Hukumar ta kuma amince da sauya wurin aikin Ahmed Yahuza Nuhu, babban jami’in gudanarwa a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati, zuwa Kwalejin Ilimi ta A.D. Rufa’i da ke Misau, inda zai yi aiki a matsayin Malami na mataki na III (Lecturer III) a CONPCASS 8/2.
Shugaban hukumar, Dr. Ibrahim Alhaji Muhammad, ya sake jaddada ƙudirinsa na kare mutunci da martabar hukumar ta hanyar tabbatar da bin dokoki da ka’idoji yadda ya kamata.
Ya kuma gargaɗi ma’aikatan gwamnati a jihar da su guji aikata duk wani nau’in rashin da’a yayin gudanar da ayyukansu na hukuma.














