Daga ran 14 zuwa 19 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kolin G20 karo na 17 da aka yi a tsibiri Bali na kasar Indonesiya, da taron kolin APEC karo na 29 a Bangkok na kasar Thailand, tare da kai ziyarar aiki a kasar, bisa gayyatar da aka yi masa.
A yammacin jiya ranar 19 ga wata, Xi Jinping ya kammala ziyararsa a wadannan wurare ya kuma dawo kasar Sin.
Kungiyar G20 na fuskantar kalubaloli masu tsanani idan aka kwatanta da sauran lokuta a tarihi, a matsayi wani dandalin dake tara manyan kasashe da dama, da kuma muhimmin dandalin hadin kan kasa da kasa.
Xi Jinping ya sake bayyana matsayin Sin kan manufofin da ta gabatar da yin kira ga sauran kasashe da su amince da ra’ayin kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, da hada kai don samun ci gaba da moriya tare da yin hakuri da juna da taimakawa juna a maimakon kawo baraka da yin fito-na-fito da nuna bambanci, ta yadda duniya za ta samu bunkasuwa mai dorewa.
AEPC ta kasance dandali mai muhimmanci ta fannin hadin kan tattalin arziki a yankin Asiya da Pacific.
A yayin taron APEC, Xi Jinping ya yi cikakken bayani kan dabarun da suka kai ga nasarar da aka samu a fannin tattalin arziki tsakanin kasashen Asiya da Pacific, a cewarsa, bai kamata kasashe masu karfi su rika yin takara a wannan yankin ba.
Kuma ya yi kira da a martaba hanyar samun bunkasuwa cikin lumana da yin hakuri da juna da bude kofa da zurfafa amincewa da juna da hadin kai da samun moriya tare a tsakanin kasashen wannan yankin, da kafa kyakkyawar makomar yanki ta bai daya yadda ya kamata.
Xi kuma ya sanar da cewa, Sin ta shirya karbar bakuncin dandalin koli na hadin gwiwar kasashe bisa shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3 a badi.(Amina Xu)