Ya Kamata A Hada Kai Don Warware Matsalar Al`umma—Jifatau

Jifatu

Daga Mustapha Ibrahim,

Ganin yadda hukumomi da shugabani masu kishin aluma da kasasu ke kokari a kulli yaumun na ganin an aluma an gina kasa an warware matsalolin aluma, wannan shi ne burin duk wasu shugabani na gari na da can da na yanzu kuma wannan shi ne yakamata kowanamu yasa a cikin zuciyarsa na rayuwarsa dan haka warware matsalar aluma musamam matasa da raunana da marayu da sauran aluma da ta yadda ta tashi ta taimakin kanta na yakar talauci da fatara ta hanyar yin sanaa, yin noma ko kasuwanci da dai abubuwa na warware matsalar aluma Hausawa ko Hausa Fullani shi ya kamata shugabanimu na yau da mawadatanmu na yau da malamammu na yau shi ya kamata ayi gasar warware matsalar aluma ba nuna isa ko wadata abukukuwan auranmu ba.

Wannan Jawabin ya fitu ne daga bakin Alhaji Sabitu Yahaya Muhammad Jifatu a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan da kammala daurin  auran diyarsa mace ta farko Dr Aisha Sabitu Muhammad Jifatu wanda akayi a masallacin jumaa na Umar Bn Khattab dake shataletalan dangi Gyadi-Gyadi cikin burnin kano a wannan jumaar da ta gabata.

Bikin daurin auran wanda ya samu hallatar dinbun masoya da yan uwa na jini abukan muamala da sauransu duk da daukar matakai da akayi mutuka na takaita gayata aluma musamam in akai la akari da yadda shugaban Jifatu ya sawakewa aluma na rashin sa sanarwar a kafafan yada labarai kamar yadda akasan yadda mawadata da shugabani ke maida bikin Aure wani dandali na nuna wadata da isa duk da halin da aluma take ciki shugaban rukununin Jifatu Alhaji Sabitu Yahaya Muhammad na ganin cewa akwai bukatar alumar mu ta yau kullom ta rika dauka abu wanda yafi mahimanci akan abun da bai kaishi mahinmanciba ma ana duk da bakin aure abu ne na farin ciki da godiya ga Allah da ya yi ma bawa wannan baiwa ta ganin auransa ko na yayansa wanda wasu da dama Allah bai nuna musu wannan ranaba to amma a taimaki aluma raunana ta yadda ya kamata ina ganin  a gon Allah zaifi fiye da yadda alumamu ta ke kashe makudan kudade akan bukukuwan Aure da ba karewa yakeyiba duk kuwa da matsalolin da suka mamaye jahuhinmu na Arewa da alumarmu Hausa Fullani dama sauran aluma da ma Najeriya baki daya to lallai ya kamata ayi karatun ta nutsu akan irin abubuwa da ke faruwa ayau na fifita abun da ba shi ya kamata a fifata ba.

Haka kuma Alhaji Sabitu ya yi amfani da wannan dama wajen nuna farin cikinsa  da gamsuwarsa da kuma yabawa daukacin alumar da suka hallaci wannan daurin Aure daga wasu jahuhin kasarnan kamar su Katsina, Kaduna, Jigawa, Zamfara, sakoto, bauchi, legos, barno, yobe, da dai sauran jahuhin Arewa da kudancin kasarnan Musamam Gwamnan Katsina, Rt Hon Alhaji Bello Masari da sarkin sillibawan Katsina Dr Alhaji Abdulkarim Usman Hakimun Kaita da Alhaji Ibrahim Abdulkarim Usman magajin garin Kaita da dai sauran aluma daga bura ne da karkara da suka halarta.

Auran da baban limamun masalacin Jumaa na Umar Bn Kattab Sheik Yahaya Tanku ya Daura Auran Dr Muftahu Halliru Jibo da Amarya sa Dr Aisha Sabitu Muhammad  bisa yardar walihinta Alhaji Salisu Jifatu, da walihin Ango kamar yadda tsarin addini musilinci ya shardanta anbiya sadaki Naira dubu 250 wanda kuma bayanai suka nuna cewa duk wasu bidioi da wasu aladu masu tarnaki duk an ajiyesu ne a wannan aure an ba sadaki mahimanci kamar yadda addini ya koyar ayi

shi ma daya daga cikin manyan baki sarkin Sullibawan katsina Dr Abdulkarim Usman a jawabinsa, nasiha ya yi ga Amarya  da Ango na cewa kada su dauki Aure a matsayin al`ada ko wani abu na nishad, su dauke shi a matsayin ibada .

Daga nan ya neme su da su rike tarbiyya irin ta mahaifansu ,musamam shi Alhaji Sabitu  Jifatu, wanda ya san shi mutu ne mai karamci da haba-haba da jama`a, kuma mutum ne wanda ba ya son abin da ba shi da manufa.

Haka kuma, cikin mutanen da suka halarci wannan biki, sun hada da Farfesa Usman Zunnuraini, Dr. Sagiru, Alhaji Lawan, da dai sauran su, wanda dukkanin su sukai jawabi akan mahimmancin Aure da kuma yadda ya kamata mai gida da uwar gida ya kamata su yi mu`amala kamar yadda Addini ya tsara a rayuwar aure sabanin abubuwan da ke faruwa a gidajan aure a yau.

Shi ma Alhaji Lawan Dankama wanda aka fi sani da Deputy na Jifatu da Manajan saye da siyarwa, Mallam Nafiu Shuaibu Koki da Alhaji Baba Mahadi, da Alhaji Bashir ACC Injiniya Ibrahim, sai Alhaji Bello Malam Mahabu Kastina da dai sauran makusanta,  kuma jamiai a wannan wuri,  dukkansu yabawa suka yi kan Alummar da suka da halarci bikin, da wadanda suka aiko da addua da fatan Alkairi a wannan lamari da cewa abun a yaba  ne wwarai da gaske.

Sai dai kuma wakilin mu ya rawaito mana cewa wata majiya mai tushe cewa Taron daurin auran an so takaitashi ne da ko da mutum Biyar ne daga bangaran ango da Amarya  a daura shi, sai dai shawarwari da umarni daga magabatan Jifatu ne ya sa aka yi wannan taro ba tare da wata gagarumar gayyata da aka saba yi a aure irin wannan ba.

An jiwo wani bawan Alla, Malam Ibrahim Halilu na cewa bai taba ganin auran manya da ya burge shi kamar wannan ba, domin an isa a nuna isa, amma neman yadar Allah ya hana a nuna isa, kuma ga shi an yi wa alumma masu rauni hidima kamar yadda ya kamata, wannan abin koyi ne ga alumma.

Exit mobile version