Connect with us

LABARAI

Ya Kamata A Rika Mutunta Al’adun Kabilun Kasar Nan Domin Kyautata Zaman Lafiya -Kobi

Published

on

An hori ‘yan Nijeriya da su ke girmama al’adun sauran kabilun da suke kasar nan ta Nijeriya domin daurewar zaman lafiya da ci gaban kasa.
Mai rikon mukamin Daraktan wayar da kan jama’a na kasa a jihar Bauchi Alhaji Nura Yusuf Kobi shine ya yi wannan kiran a wajen bukin ranar Yarbawa da ya gudana a cikin jihar Bauchi.
Yusuf Kobi ya bayyana cewar wannan ita ce hanya daya tilau da za ta kawo karshen matsalar yawaitar banbance-banbancen da ke tsakanin al’umma, yana mai jaddada cewar yarda da juna da hakuri shine zai kara hada kan ‘yan Nijeriya waje guda, don haka ne ya nemi kowani dan kasa ya rungumi zaman lafiya da hakuri a matsayin hanyar taimakawa kasar nan.
Don haka ne ya nemi ‘yan Nijeriya su kasance masu ci gaba da mutunta al’adun kowace kabila da suke rayuwa guri guda tare domin kyautata mu’amala da ci gaban kasar Nijeriya.
A tasa jawabin shugaban kungiyar ‘yan kabilun Yarbawa Olaoti Shehu ya yaba sosai wa gwamnatin jihar Bauchi a bisa baiwa ‘yan kabilar Yarbawa yanayin rayuwa mai kyau hade da kiran gwamnatin da sauran masu ruwa da tsaki a jihar da su daura kan hakan domin ci gaban jihar.
Olaoti ya kuma nuna gayar godiyarsu ga Sarakunan Bauchi, Al’umman jihar hade da malamai a bisa goyon baya da kuma wanzar da zaman lafiya da suka kasance masu yi a kowani lokaci, don haka ne ya misalta zaman lafiyar da ake da shi a jihar bauchi a matsayin hanyar ci gaban jihar ta Bauchi.
Ya bayyana cewar suna shirya taron ne duk shekara domin tunawa da al’adunsu hade da girmama al’adunsu na kaka-da-kakanin da suka taso suka riska, don haka ne ya bayyana cewar za su ci gaba da taka rawa sosai wajen habaka ci gaban jihar Bauchi a kowani lokaci.
A cikin sakonsa, gwamnan jihar Bauchi ya sha alwashin ci gaba da baiwa ‘yan kabilar dukkanin hadin kai gami da samar musu da yanayin tsaro.
Ababen da suka wakana a wajen taron sun hada da baje al’adun yarbawa kala-kala, hade da gayyatar manyan baki a cikin jihar ta Bauchi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: