Bisa labarin da jaridar ‘The Punch’ ta Najeriya ta bayar, an ce, a kwanan nan kwamitocin majalisar dokokin Amurka sun gudanar da taro, don tantance lamuran garkuwa da mutane da ke faruwa a Najeriya, da kuma batun zargin da aka yi cewa wai ana cin zarafin Kiristoci a kasar. Kafin hakan, shugaban Amurka Donald Trump ya furta a shafinsa na sada zumunta cewa, Najeriya ta zama “wuri mai barazana ga rayuwar mabiyan addinin Kirista”, ya kuma sake sanya Najeriya a cikin jerin kasashe da ake sa musu kulawar musamman bisa dokar ‘yancin addini ta kasa da kasa, kana ya umurci ma’aikatar tsaro ta Amurka, da ta shirya wajen daukar matakin soji a Najeriya idan hakan ya zama wajaba.
To ko me ya sa Amurka ta sa hannu cikin harkokin gidan Najeriya ba zato ba tsammani? Kuma ko mene ne ainihin burinta?
Lallai, Amurka tana zargin Nijeriya da “cin zarafin Kiristoci a Najeriya”, amma gaskiyar lamarin shi ne, mafi yawan rikice-rikice da ke faruwa a Najeriya suna da alaka da kwaton albarkatu da rikice-rikicen kabilu, yayin da kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta “Boko Haram”, ke kai hare-hare ba tare da bambanta wani addini ba. Ko musulmai ma suna cikin wadanda abin ya fi shafa. Don hakan zargin na “kisan kiyashi na addini” ba shi da tushe balle makama.
A bangaren siyasar cikin gidan Amurka, shugaba Trump yana amfani da “kare mabiyan addinin Kirista” don neman gamsar da masu jefa masa kuri’a mabiyan addinin kirista ‘yan bushara, don samun goyon bayansu, tare da dora laifi kan saura game da matsalolin tattalin arziki da rashin aikin yi a cikin Amurka.
A fannin tattalin arziki kuma, Najeriya a matsayinta na kasar da ta fi yawan samar da mai a Afirka, Amurka ta matsawa Najeriya lamba ne da nufin mallakar makamashinta da sauran muhimman albarkatu, tare da raunana tasirin wasu kasashe a fannin hadin gwiwar makamashi tsakaninsu da Najeriya.
A sa’i daya kuma, Najeriya muhimmiyar kasa ce a yankin yammacin Afirka. Amurka na neman shiga fagen tsaron Najeriya ne ta hanyar fakewa da batun “hadin gwiwar tsaro”, don dakile yunkurin adawa da kasashen yamma a yammacin Afirka, tare da tilasta wa Najeriya nuna goyon bayanta.
Sai kuma ta fannin dangantakar Najeriya da Amurka, game da harajin da Amurka ta kakabawa sassa daban daban, shugaban Najeriyar Bola Tinubu ya taba cewa: “Idan kudaden shigarmu da ba na bangarorin mai ba suna karuwa, ba za mu ji tsoron duk wani abu da Trump ke yi ba.” Kazalika, a babban taron MDD na karo na 80, mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya zargin matakan da Isra’ila ta dauka a Gaza, da kuma asarar rayukan Palasdinawa da hakan ya haifar. Hakan ne ma ya sanya kafofin yada labarai na Amurka, suka karawa labaran tashe-tashen hankula na cikin gidan Najeriya gishiri, don mai da martani ga Najeriya kan wadannan batutuwa.
A duniyar yau, yawancin kasashe suna mayar da hankali kan zaman lafiya da ci gaba, suna kara hadin gwiwa don cin moriya tare. Irin wannan dabaru da Amurka ke dauka na yin barazana, da matsin lamba, da sanya takunkumi bisa karfinta sam ba su dace ba. Dole ne ‘yan Najeriya su jagoranci kansu, su magance matsalolin Najeriya da karfin kansu. Kamata ya yi Amurka ta daina sa hannu cikin harkokin cikin gidan Najeriya. (Mai rubutu: MINA)














