Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTAUNAWA

Ya Kamata Gwamnati Ta Kafa Hukumar Maganin Gargajiya Da Za Ta Yi Aiki Da NAFDAC – Dakta Hassan Salihu

by Muhammad
December 25, 2020
in TATTAUNAWA
4 min read
Maganin
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Dakta Hassan Salihu, na daya daga cikin wadanda suke ba da magungunan gargajiya a garin Jos babban birinin Jihar Filato, kuma shi ne shugaban masu magungunan gargajiya karkashin kungiyar Izalatil Bida WaIkamatis Sunnah (JIBWIS), na kasa mai hedkwata a Jos. Ya sami tattauna wa da wakilimmu dake Jos Lawal Umar Tilde, a kan abin da ya shafi harkarsu ta masu ba da maganin gargajiya da kuma irin nasarar da kungiyar IZALA ta samu tun kafuwarta a 1978. Ga yadda hirar ta kasance.

 

samndaads

 Assalamu Alaikum, masu karatu za su so sanin da wanda muke tare

Wa’alaikumussalamu Warahamatullahi Taala, wabarkatuhu, sunana Dakta Hassan Salihu, Shugaban masu maganin Gargajiya na Kungiyar Izalatul Bidah WaIkamatis Sunnah (JIBWIS), mai shelkwata a Jos fadar gwamnatin Jihar Filato.

Kasancewar ka Malamin Addinin Musulunci mai karantarwa, kuma ga shi kana ba da maganin gargajiya, mutane za su so sanin wannan sanaa shin ka gada ne ko kuma taka haye ka yi?

Alal hakika wannan sana’a gadar ta na yi, domin Babana da Ka kana, duk sanaarsu kenan, yanzu ba zan gaza shekaru Arbain ba akan wannan sanaa, ta ba da magani don tun ina dan karamin yaro nake taya babana gudanar da wannan sanaar, duk karatuttukan da na yi na yi su ne ina gudanar da wannan sana ta ba da magani.

 

Wace Cuta ce ka fi kwarewa kan bayar da maganinta?

To Alhamdulillahi akwai wani magani da nake kira mainasara, shi wannan magani ya na warkar da ciwon kafafuwa da ciwon baya, da sauran wadansu cututtuka.

 

To yaya maganinka ya karbu a hunnun jamaa?

 

Wadanne kalubalene ka fi fuskanta a wannan harka ta ba da magani?

Babbar masalar a nan kusan zan ce ba ni ka dai nake fuskantarta ba, kusan duk wani wanda ya san magani a kan harkar jinya yana fuskantarta, wannan abu kuwa shi ne na ya wai tar masu sayar da magungunan gargajiya a kasuwanninmu ba tare da suna da kwarewa ba a harkar ba da maganin.

 

Ko wane karin haske za ka yi game da cutar Korona wacce a yanzu ake rade-radin an samu rigakafinta?

Ni abin da zan ce a nan tarihi ne yake mai maita kansa domin duk abin da ka gani ya faru, to kuwa an yi irinsa a duniyar nan, kuma Allah bai taba saukar da cuta ba tare da ya samar da maganinta ba sai dai mutuwa ce kawai ba ta da magani, ko a nan Nijeriya a baya muna yara an yi ire-iren annoba makamanciyar wannan inda mutane suka yi ta mutuwa kamar wani ba zai ragu ba, cututtuka irin na Sankarau, Kwalara, ciwon Agana, sun yi kisa a kasar nan fiye da na Korona.

 

Har wayau mai karatu zai so sanin meye ya sa ka alakanta kanka da Kungiyar Izalatil Bidah Wa Ikamatis Sunnah [JIBWIS?

Ita kungiyar Izala, ka san ana mata kirari kowa Malam, kuma idan ka duba a cikin ayarin tafiya wajen gudanar da waazozi da take gudanarwa a jihohi ciki da wajen kasar nan akwai masu gudanar da sanaoi, daban-daban da suke cikin ayarin tafiyar, amma duk cikinsu ba sanaar da take illa da hadari kamar ta ba da magani gargajiya, shi ya sa kungiyar ta bani shugabanci a wannan bangare, don lura da irin mutanen da suke gudanar da irin wannan sanaar cikin tafiyar a wajen wazuzzukan da kungiyar ta ke gudanarwa a ko ina cikin fadin tarayyar kasar nan da kasashen waje.

Shekara nawa ka yi cikin tafiyar kungiyar Izala a fannin halartar wa’azi ?

Tun kafuwarta a 1978. Kasancewar ni Almajiri ne a fannin karatun Arabiyya.

To daga karshe wane irin taimako ne ka ke bukata gwamnati ta rika yi wa irinku masu taimakawa alumma wajen yin jinya?

Ina kira ga gwamnatin tarayya da kirkiro da wata hukuma da za ta rika kula da harkar masu ba da maganin gargajiya da za ta yi aiki kafada daya da hukumar NAFDAC, wajen tsabtace aikin masu ba da magun gunan gargajiya a kasar nan don tsabtace sanaara a kasar nan. Ina kuma yin amfani da wannan dama wajen yaba wa Gwamnan Jihar Filato, Rt. Honarabul Simon Bako Lalong, bisa nasarorin da gwamnati mai ci yanzu a Jihar karkashin jagorancinsa ta samu a wajen maido da zaman lafiya da kyakkyawar fahimta a tsakanin alummar jihar, kuma ina mai yin kira ga alummar jihar da su binne duk wani banbanci dake a tsakaninsu su hada kansu su bai wa gwamnan goyon baya don ya sami karin karfin gwiwar aiwatar da kyawawan manufofinsaa na kawo sauyi mai maan a jihar.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

‘Yar Kasuwa Ta Mutu Yayin Da Ake Rushe Kasuwa  A Kaduna

Next Post

Bincike Ya Gano Yadda ‘Yan Nijeriya Miliyan 170 Ke Zama A Kazanta

RelatedPosts

Gadon Siyasa Da Kasuwanci Na Yi – Hon. Mai-Shanu

Gadon Siyasa Da Kasuwanci Na Yi – Hon. Mai-Shanu

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

HON. MUHAMMAD UBA GURJIYA MAI SHANU shine wakilin al'ummar karamar...

Gwamnatin Jihar Kano Tana Bukatar Kowa, Inji Ibrahim Usman Bala

by Muhammad
6 days ago
0

Daga Haruna Akarada, A ci gaban da gwamnatoci ke kokarin...

Daukar Hoto

Mun Kawo Canji A Harkar Daukar Hoto A Arewa – Gali DZ

by Muhammad
1 week ago
0

Daya daga cikin masu ba da gudunmawa a harkar samar...

Next Post
Kazanta

Bincike Ya Gano Yadda ‘Yan Nijeriya Miliyan 170 Ke Zama A Kazanta

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version