Miliyoyin Amurkawa a jihohi 15 da tsibirin Samoa na Amurka ne suka fara kada kuri’a tun a ranar Talata, a zaben ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Democrat da Republican.
Sakamakon farko ya nuna shugaba Joe Biden da tsohon shugaban kasa Donald Trump sun lashe zaben jam’iyyunsu a Virginia, North Carolina, Maine, Oklahoma, Tennessee da Alabama. Biden kuma ya lashe Vermont da Massachusetts.
- Bai Kamata Jama’a Su Tsorata Da Bullar Zazzabin Lassa A Adamawa Ba – Kwamishinan Lafiya
- Alkaluman Sun Shaida Cewa Dole A Fahimci Ci Gaba Yayin Da Ake Kokarin Samar Da Shi
Sai dai har yanzu ba a bayyana na bangaren Republican ba a jihohin biyu.
Amma da yake sama da kashi uku na wakilai a manyan tarukan jam’iyyun na wannan bazara ake zawarci, da Biden da Trump kowannensu na iya daukar wani babban mataki don samun nasarar cin mafi yawan wakilan babban taron, kuma nan ba da jimawa ba za su iya nasarar zama ‘yan takarar jam’iyyar a zabukan fidda gwani masu zuwa nan da makonni masu zuwa.
Biden bai fuskanci wani kalubale sosai ba a takarar Democrat, yayin da Trump ke da abokiyar hamayya daya kawai da ta rage, wato tsohuwar jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley.
Trump dai ya doke ta a kowace fafatawa a zaben fidda gwani na jahohin ko da yake kawo yanzu, Haley ce ta yi nasara a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Washington, D.C., inda ‘yan jam’iyyar Republican 2,000 suka fito don kada kuri’a a babban birnin.
Jam’iyyar Democrat ke da rinjaye. Ita ce mace ta farko da ta taba lashe zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican.