Dubban jama’a ne suka yi dafifi a Babban Masallacin Juma’a na garin Jere da ke ƙaramar Hukumar Kagarko a farkon makon nan domin halartar walimar da aka shirya ta musamman domin godiya ga Allah da kuma karrama tsohon shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa, CGI Isah Idris Jere bisa kammala aiki a hukumar lami lafiya.
Ƙungiyar Bunƙasa Ci Gaban Jere ta Matasa ce ta shirya walimar wanda ta samu halartar manya da ƙananan jami’an hukumar ta NIS.
An fara gudanar da walimar ce da buɗe taro da addu’a daga Babban Limamin Jere, Malam Muhammad Rabi’u Aminu, daga bisani aka gabatar da nasihohi daga malamai daban-daban na ɓangaren ɗariƙa da Izala na garin Jere.
Malami na farko da ya yi wa’azi mai taken “Riƙon Amana”, Malam Ahmad Ilyasu Makera, ya yi kira ga ɗaukacin al’umma ta riƙa tunawa da nauyin riƙon amana tare da mayar da amanoni ga ahalin abin, kana ya jaddada muhimmancin tsarkake zuciya cikin dukkan abin da za a aikata. Ya yi addu’ar Allah ya ninninka ladan kyawawan ayyukan da tsohon shugaban na NIS Isah Jere ya aiwatar a kan kujerarsa da ma ragowar abubuwan da za iyi a gaba.
Shi ma da yake nashi wa’azin a kan muhimmancin taimakon jama’a, Malam Abdulrahman Musa ya tunatar da jama’a muhimmanci da kyakkyawar sakayyar da Allah yake wa duk wanda ya taimaki halittarsa. Kana ya yi kiran a daina wulaƙanta almajirai domin a cewarsa, kowa almajiri ne kuma komai matsayinsa matuƙar mutum ya sa ƙafa ya bar garinsa zuwa wani wuri neman halaliyarsa.
Ya jinjina Wa Alhaji bisa ƙoƙarin da ya yi na ƙarfafa ilimi a garin Jere, yana ba da misali da wata makaranta da ya tabbatar da kafuwarta da za ta riƙa bayar da babbar shaidar takardar karatu.
Ya kuma yi kira ga sauran ma’aikata da ma ‘yan kasuwa su ƙara himma wajen taimakon al’umma saboda a halin yanzu mutane suna cikin wani yanayi na buƙata sosai. Daga bisani ya jaddada muhimmancin gyara zukata domin ƙara kyautata addini da zamantakewa.
A nashi ɓangaren, Malam Mustapha ɗalhat wanda ya yi wa’azi a kan gudunmawar matasa a cikin al’umma. Ya bayyana matasa a matsayin ƙashin bayan ci gaban al’umma kana ya buƙace su su yi ƙoƙari su ci gajiyar shekarun ƙuruciyarsu kafin tsufa ko mutuwa ta zo.
“Idan aka ce matasa ana nufin shekara 15 zuwa 45, daga nan ne mutum yake fara shiga farko-farkon shekarun dattako. Ina kira ga matasa su kauce wa ayyuka na assha saboda duk inda aka ga tsohon banza to ya lalata rayuwarsa ce tun lokacin da yake matashi.”
Ya bayyana cewa ayyukan alheri da CGI Isah Idris mai ritaya ya yi har aka shirya masa walimar taya murnar ritaya, tun yana matashi ne ya sa ɗigon aiwatarwa, don haka ya ja hankalin matasa su yi koyi.
Haka nan ya yi nasiha ga ɗaukacin al’ummar masarautar Jere su yi kaffa-kaffa da masu yaɗa gulmace-gulmace, domin ta haka ake hana masu niyyar aikata alheri aikatawa.
Da yake ƙarin bayani kan nasihohin da malaman suka gabatar, Malam Ibrahim Tahir
ya yi kira ga duk mai so ya gode wa CGI Isah Jere ya tashi cikin dare ya yi masa addu’a a kan Allah ya saka masa da alheri kuma Allah ya ƙara yi wa ratuwarsa albarka.
A nashi ɓangaren, mai martaba Sarkin Jere Alhaji Abdullahi Daniya ya yaba da ƙoƙarin tsohon shugaban hukumar ta NIS, Isah Idris Jere bisa yadda ya hidimta wa ƙasa cikin adalci da riƙon amana, yana mai bayyana cewa Masarautar Jere tana matuƙar alfahari da shi saboda bai watsa mata ƙasa a ido ba. Kana ya yi kira ga sauran al’ummar masarautar su riƙe gaskiya da adalci a duk inda suke domin gobe kiyama da kuma zama jakadun masarautar nagari.
Haka nan ya jaddada buƙatar zaman lafiya da taimakon juna a tsakanin al’ummar masarautar da kuma bin doka da oda yadda ya kamata domin ci gaban masarautar da ma Jihar Kaduna baki ɗaya.
“Muƙamin da Alhaji Isah ya riƙe abin godiya ne ga Allah. Ina iya tunawa lokacin da na kai su makaranta, a lokacin makarantar firamare aji 7 ake yi, ga shi yau muna taron godiya ga Allah ya yi aikin Immigration har ya kai matsayin Kwanturola Janar kuma ya kammala lafiya. Allah ya saka masa da alkhairi bisa yadda ya duba rayuwar matasa na baya. Kuma ina kira wannan ya zama abin koyi ga saura.” In ji sarkin.
Shi kuwa wanda aka shirya walimar domin sa, CGI Isah Idris Jere mai ritaya, ya fara ne da waiwaye adon tafiya kan karatun da ya yi da kuma shigarsa aiki, inda ya gode wa mai martaba Sarkin Jere, da ya zama sila.
“Lokacin da matasan nan suka zo mun da shawarar za su shirya wannan taro sai na ce a gudanar da shi a Masallaci, godiya ga Allah kenan. Kamar yadda Barade ya faɗa, duk abin da aka gani Allah ya yi amfani da mu ya yi, mai martaba shi ne mu’assasi. Na sha zuwa ɗaki na same shi na faɗa masa, waɗanda ba su sani ba, su sani. Shi ya ɗauke mu mu huɗu ya kai mu makarantar Sakandare, kenan duk abin da muka yi masa bai kamata mu yi ba? Waɗanda ba su sani ba su sani. Don haka duk abin da ya kamata mu yi, za mu yi. Kuma Alhamdu lillah, mun samu tarbiyya ta iyaye duk inda mu ke ba za ka samu aiki ko kallo na wulaƙanci a gare mu a waɗannan wurare (da muka yi aiki) ba. Sannan ganin damar Allah ne ya kai mu matsayin. Kuma kowa a kan jarrabawa yake, kai mai yi za ka yi biyayya shi kuma wanda aka ba zai yi adalci? Kowa cikin jarrabawa yake kuma kowa so yake ya ci, don kowa zai tsaya a gaban Allah Subhanahu wa Ta’ala ya amsa tambayoyi kamar yadda malamai suka yi mana nasiha. Fatanmu dai Allah ya ba mu ikon cin jarrabawa.
“Kamar yadda wasu suka sani, bayan karatu hatta shiga aikin ma mai martaba ne sila, a lokacin Garba Abbas yana Darakta na Immigration, duk shi ya yi mana, don haka ba za mu manta ba har abada. Allah ya ƙara wa sarki lafiya. Allah ya saka wa kowa da alkhairi.”
Wakazalika, tsohon shugaban na NIS, ya ja hankalin matasa a kan su yi amfani da damar da Allah ya ba su ba tare da zamewa daga turba tagari da aka ɗora su a kai ba, yana mai jaddada cewa ya zama wajibi kuma su riƙa mayar da al’amuransu ga Allah Ta’ala matuƙar suna son cin nasara a rayuwa, “domin duk abin da wani ya yi wallahi Allah ne ya yi, bisa ganin damar Allah ne, Allah ke shafe abin da ya so kuma ya tabbatar da abin da ya so… Za a wayi gari ka mutu amma duk abin da ka yi yana nan a rubuce. Alhamdu lillah, kamar yadda muka samu tarbiyya daga mai martaba muna nan muna ƙoƙarin nuna wa ‘ya`ya da ƙannenmu.”
Haka nan ya yi kira ga duk waɗanda suke samun manyan muƙamai su riƙa tunawa da gida cikin duk abin da za su yi, yana mai cewa, “al’ummar da aka haife ka a ciki, ka rayu a ciki kuma ita za ta kai ka kabari, don ka samu wata ɗaukaka sai ka ce ba ruwanka da ita, anya mutum idan ya yi haka yana da hankali kuwa? To ƙalubale musamman ga samari, an samu mutane da dama da suka shuɗe, kafin mu wasu sun yi. Alhamdu lillah, wannan aiki da na yi har na kai ƙololuwa bisa ganin damar Allah ne, cikin hikimarsa ne ya yi haka ba dabara ba, ba iyawa ba. Shi ya sa ya zama wajibi mu maida wa al’ummarmu abin da muka samu. Tarbiyyar da muka samu da taimakon da muka samu duka yanzu lokaci ne na biyan bashi. Duk wanda aka yi masa haka shi ma zai yi sakayya, yi ƙoƙari ka biya bashi.
“Daga ƙarshe ina godiya ga mai martaba da kowa da kowa, Allah ya saka wa kowa da alheri. Su waɗannan matasa da suka shirya wannan taro kamar yadda suka sani ban so ba a yi hakan saboda Abdulrazaƙ ya sani, ni ko ma’aikatata ba mai son a ce na iya ba ne, ka bari idan Allah ya ga dama zai maka. Kai a matsayinka na ɗan’adam kana da limitation (iyaka) kan abin da za ka iya yi, amma Allah Ta’ala ba shi da iyaka, idan ya ga dama zai yi ma…duk abin da Allah ya tsara maka zai same ka kuma duk abin da aka yi ba don kai ba wallahi ba zai taɓa samun ka ba. Idan muka wa’azantu da haka, za mu yi rayuwa cikin sauƙi, mu yi zumunci, mu kyautata wa ‘yan’uwa. Allah ya saka da alheri.” In ji shi.
A jawabinsa na fatan alheri, Kwanturolan NIS na Jihar Kaduna, CIS Muhammad Bashir Lawal, ya nuna jin daɗinsa da yadda CGI ya riƙe su kamar ‘ya’yansa a NIS, ya ce ba su da abin da za su iya saka masa da shi sai dai addu’a. Ya yi godiya ga dukkan waɗanda suka shirya wannan walimar a madadin ɗaukacin jami’an shige da fice.
Ya tabbatar wa da CGI cewa ba za su bashi kunya ba, kuma za su ci gaba da bin turbar da ya ɗora su a kai na alheri.
An kammala taron tare da gabatar da lambar yabo da kyautar girmamawa ga tsohon shugaban na NIS, Alhaji Isah Idris Jere.