Ruwan sama mai ƙarfi ya haifar da ambaliyar ruwa a wasu sassa na ƙasar Saudiyya.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya mamaye hanyoyi a garin Makkah.
- EFCC Ta Kori Ma’aikata 27 Kan Zamba da Rashin Da’a
- Kasar Habasha Ta Jinjina Wa Kamfanin Kasar Sin Bisa Kirkiro Da Ayyukan Yi a Kasar
Haka kuma, an ga yadda wasu maza suka haÉ—a hannu don ceto yaran da suka makale a unguwar Al-Awali saboda ambaliyar.
A birnin Jeddah, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya sa an soke tashin wasu jiragen sama, sannan hukumomin Saudiyya sun rufe makarantu a duk faɗin ƙasar.
Wannan ba shi ne karon farko da Saudiyya ke fuskantar irin wannan yanayi ba.
A shekarar 2009, birnin Jeddah ya fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani, wanda ya janyo mutuwar mutum sama da 100 tare da lalata gidaje da tituna.
Hukumomin Saudiyya dai na ci gaba da ɗaukar matakai domin rage illar ambaliyar ruwan, ciki har da gina sabbin magudanun ruwa da ƙarfafa tsarin kulawa da muhalli.
Sai dai jama’a na fatan gwamnati za ta ƙara zuba jari a fannin kariya daga irin wannan annoba.