Domin saukaka zuwa aikin Hajjin 2024 ga Musulmin Nijeriya, wani hadin gwiwa bisa jagorancin Sanata Ahmad Abubakar MoAllahyidi a karkashin inuwar Kungiyar Arewa New Agenda (ANA), ya kaddamar da gangamin da ya gudanar na musamman kan lamarin.
Wannan yunkuri ya yi duba na tsanaki a kan muhimman batutuwan da suka shafi farashin kujera da samun damar sauke farali, tare da ba da shawarar daukar matakai don saukaka matsalolin kudi da maniyyata ke fsukanta.
Yunkurin na ANA a cewar jagororin kungiyar, ya samu amincewa da cikakken goyon bayan shugabancin hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), tun daga farko har zuwa karshe.
An yi gangamin na ANA ne ta hanyar gudanar da wasu muhimman ayyuka a yankunan da suka hada da Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka hada malaman addini, masu ruwa da tsaki, da hukumomin alhazai na jihohi wuri guda, domin magance matsalolin da ke addabar maniyyata, gabanin cikar wa’adin biyan kudin aikin Hajji da aka sa da farko na ranar 31 ga Disamba.
Gangamin na ANA ya kunshi dabarun magance kalubale iri-iri da ke tasiri wajen samun damar zuwa aikin Hajji, da suka hada da masauki a kusa da Harami, tsarin ciyar da abinci, kudin harajin kasa, kudin jirgi, da kuma kudin hidindimu, wadanda duk suna ba da gudummawa ga kara tsadar kudin kujera ga maniyyata.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana damuwarsu a yayin gudanar da gangamin, musamman game da damfarar da ake yi wa alhazai, jinkirin yada bayanai, da rashin isasshiyar wayar da kan al’ummar karkara dangane da sabbin ka’idoji da wa’adin biyan kudin Hajjin 2024.
Binciken da aka yi na yanki ya nuna yadda wasu jihohin ke kokarin cike kason kujerun da aka ware musu na aikin Hajji, yayin da wasu kuma ke fuskantar kalubale saboda hukuncin da kotu ta yanke da kuma jinkirin abubuwan da aka sa a gaba. An gano bukatar tsawaita wa’adin karshe da samar da tallafi a matsayin manyan shawarwarin da za su saukaka zuwa aikin Hajji.
Yankin Arewa ta tsakiya ya bayyana rashin samun cikakkun bayanai tare da ba da shawarar gudanar da gangamin ilmantarwa don cike gibin wayar da kan maniyyata musamman wadanda suke karkara.
Masu ruwa da tsaki sun bayar da shawarar a rubanya kokarin wayar da kan jama’a, da kara hada kai da cibiyoyin hada-hadar kudi don magance matsalolin biyan kudi, da kuma yin kira ga gwamnatoci da su ba da tallafin kudin aikin Hajji, da magance matsalolin da suka shafi zamba, inganta gudanar da ayyuka, da kuma tsare-tsare na adashin gata a kan lokaci.
Wani abin karfafa gwiwa, jami’an gwamnati a jihohi daban-daban da suka hada da Kano, Kebbi, Birnin Abuja, Zamfara, Kwara, da Nasarawa, sun bayyana gamsuwa kan matakan da gwamnatocinsu suka dauka na ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin 2024, tare da tabbatar da kudirinsu na magance kalubalen da ake fuskanta.
Sanata MoAllahyidi ya mika godiya kan goyon bayan da hukumar alhazai ta kasa da kuma hukumomin alhazai na jihohi daban-daban suka ba su, inda ya yaba da kokarinsu na hadin gwiwa wajen samar da hanyoyin saukaka zuwa aikin Hajjin 2024 sauki ga musulmin Nijeriya.