Tunanin da ake da shi na cewa akwai karancin mata masu rungumar fasahar gyaran waya da sarrafa shi a fadin Nijeriya, musamman a arewacin kasar yanzu ya fara sauyawa domin kuwa ana samun mata da dama da suke shiga harkar ta gyaran waya domin tafiya da zamani a bangaren fasaha, inda aka samu wata jarumar mace da ta shigo harkar gadan-gadan a jihar Borno.
Falmata Usman, wata ‘yar shekara 23 a duniya ce, da ta kasance ta rungumi sana’ar da maza suka fi yawa a kanta wato gyaran waya, inda ta janyo wasu matan a kusa da ita suke gwagwarmayar gyaran waya a garin Mafa, daya daga cikin kananan hukumomin da Boko Haram suka lalata a jihar.
- Masana Kimiyya Na Sin Da Afrika Sun Lashi Takobin Hada Gwiwa Wajen Ganin An Cimma Ajandar Kyautata Rayuwar Jama’a
- Al’adun Kasar Sin Na Da Tushen Neman Zaman Lafiya Tun Lokacin Da
Falmata, wacce take da matakin karatun diploma a bangaren harkokin kasuwanci, duk da cewar ba ta yi aure ba, tana matsayin budurwa, ta ce, ta samu turjiya da zagon kasa, tsangwama da izgili daga al’ummar yankin nata a lokacin da ta tsunduma sana’ar gyaran wayoyi.
“A lokacin da muke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira, wata kungiya mai zaman kanta, Plan International ta zo ta koyar da mata sana’ar gyaran wayoyi. A sansanin, mun samu dukkanin tallafin da ake bukata kala daban-daban, amma muna amsar tallafin da ya dace da irin al’adunmu da addininmu kawai mu bar wadanda ba su shafemu ba.
“Da yawa daga cikinmu mun samu horo da kayan aiki. Na ajiye nawa yayin da wasu kuma suka sayar da nasu.
“Hayaniyar ta fara ne a lokacin da na yanke shawarar zan fara gyaran wayoyi. Kowani mutum kawai sai yana kalubalantar tunanina, suna cewa ai rashin mutunci ne hakan ga mata, amma ni dai na tsaya tsayin daka kan tunanin na cewa banbancin jinsi ba zai hanamu cigaba ba. A maimakon hakan ma, na karfafi wasu mata ne da su shigo mu yi tafiyar tare da su.
Lamari ne mai wahala a gareni musamman sukar da na yi ta shafa, amma Alhamdullahi, nasarori nake samu zuwa yanzu tun da na fara,” ta shaida.
Daya daga cikin ‘yan matan da Falmata ta jawo a jika take koya musu sana’ar gyaran waya a garin Mafa, Aisha Mustapha, ‘yar shekara 17 a duniya, ta jinjina wa kokarin Falmata.
Ta ce, Falmata ta yanke shawarar bude cibiyar sana’a a garinta domin ta horas da mata yadda za su samu taro-sisi da za su kasance masu rike kawukansu kuma hakan wani taimako ga al’ummar yankin domin rage musu kashe kudin zuwa cikin Maiduguri domin kai gyaran wayoyinsu, kana domin bunkasa harkokin kasuwanci a yankin.
“Ni kaina, na janyo hankalin mata da su rungumi wannan fasahar gyaran domin abu ne mai sauki kuma za su iya yi daga cikin gidajensu na aure ma. Kuma, hakai zai ba su damar su taimaki mazajensu wajen kula da harkokin rayuwa da taimaka wa ‘ya’yansu da sauran masoyansu. Ana fama da talauci a yankinmu,” ta shaida.
Wani al’adar da arewaci ke amfani da shi, shi ne an san mace da kula da harkokin gida, hadawa da sana’a na mata wuya, sai ai Falmata ta ce, a kowani rana tana fara dafa abinci da tsaftace gidan iyayenta kafin ta je ta bude shago domin yin sana’arta.
“Har yanzu ni kadai ce bana da aure, amma a kullum ina fara tsaftace gidan iyaye na dafa musu abinci kafin na fara sana’ata. Don haka, ina shawartar mata da suke wannan sana’ar, musamman masu aure da su ke tsaftace gidajensu da dafa abinci domin kare aurensu da mutunta aurensu,” ta kara da shaidawa.
Cikin taimakon Allah, a kowace rana a halin yanzu bayan shan gwagwaryar kafa cibiyar gyaran waya, Falmata Usman, ta ce, tana samun naira N30,000 a kowace rana sakamakon gyaran waya da take yi. “Ina kashe wasu kaso daga cikin dubu 30 da nake samu wa kaina, iyaye da kuma sallamar wadanda nake koyarwa tare da ajiye wasu kaso domin biyan kudin hayar shago da sayan sauran kayan bukata na shago.”
Ta kuma yi bayani dalla-dallah kan yadda ta fara kasuwancin fasahar gyaran wayoyi, inda ta bada labarin yadda ta kaya a gyaran wayar da ta yi na farko, a cewar Falmata, “Bayan wasu watanni, na fara jin cewa an kashe maguden kudade wajen taimaka min amma ban iya tabuka komai ba, sai na tarwatsa wata karamar wayar da ke hannuna Tecno sai na sake hadata wato na bata kuma na gyara. Daga nan sai na fara amsar wayoyin da suka baci daga hannun abokaina da ‘yan uwana ina gyarawa ba tare da karbar ko sisi ba har zuwa lokacin da na gama kwarewa.
“Kodayake, tun ma kafin nan, an koyar da mu yadda za mu yi kasuwanci da kuma samun kudaden shiga, yadda mutum zai kashe da yadda zai tara jari, don haka na dauko ilimin da na samu na aiwatar da su a zahirance.
“Na sha fuskantar izgili daga wajen jama’a a lokacin da na fara sana’ar gyaran waya, amma yanzu, wasu daga cikinsu sun kawo ‘ya’yansu da ‘yan uwansu ina koyar da su.
“Yanzu haka ina da mata sama da 10 da suke karkashina muke sana’ar gyaran waya a shagona, kuma wasu na kara zuwa, amma bana da wurin da zan iya daukan wadanda suke ta zuwa neman za su yi sana’a a karkashina da koyon gyaran waya. 10 din dai nake iya rikewa a halin yanzu.”
Da aka tambayeta ko tana da wani shirin janyo matasa domin koyar da su yadda za su samu rike kansu a bangaren rayuwa, sai ta ce, “Ba dai yanzu ba, domin kuwa mata su ne suka fi shiga cikin kunci a sakamakon wannan rikicin, saboda an rabasu da ‘ya’yansu da mazajensu da za su ba su kulawa. Amma nan gaba za mu san yadda za mu yi mu samar da yanayin da za mu koyar da matasan.”
Falmata ta shawarci shugaban karamar hukumar da ya karfafi tunanin nasu domin taimaka wa mata da ‘yan mata da su cigaba da rungumar sana’ar gyaran waya.
“Saboda akwai wayoyi a kowani gida, ba tare da banbancin mai kudi ko talaka ba, kowa na amfani da waya, don haka idan aka taimaka wa mata aka koyar da su a wannan bangaren tabbas za su taimaka wa gidajensu da ahlinsu. Kuma za a samu sauki sosai a cikin al’umma domin za a rage wa mutane zuwa cikin Maiduguri domin kai gyaran waya.
“Daga karshe, ina kira ga gwamna Babagana Zulum da ya duba hanyoyin da zai iya bi wajen taimaka mana a wannan sana’ar da muka sanya gaba, musamman lura da matsatsin tattalin arziki da ake fuskanta.
“Mata da dama da suka sha fama da gudun hijira za su iya kula da kansu da ‘ya’yansu da iyalansu da ‘yan uwansu idan aka taimaka musu suka tsayu da kafafunsu.”