Wasu ‘yan majalisar dattawa na jam’iyyar APC guda 22 sun yi barazanar sauya sheka zuwa jam’iyyun PDP da LP da NNPP da dai sauran su, bisa kara fusatasu da aka yi sakamakon zaben fid da gwani da aka kammala.
Ganin haka ne ma ya sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya roki sanatocin na APC kan kar su bar jam’iyyar domin kar ta rasa rinjaye a zauren majalisan dattawan Nijeriya.
Shugaba Buhari ya samu zama da wasu ‘yan majalisan dattawa na APC domin jin irin matsalolin da aka samu a wurin zaben fid da gwani da aka kammala. Ya dai amshi korafinsu tare da tabbatar da cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar za ta bi ba’asi a kan lamarin.
Ya bukaci ‘yan majalisan da su ci gaba da kokarinsu wajen ganin shugabancin jam’iyyar APC ya bunkasa kasar nan.
Ya ce, “Na ji dukkan korafe-korafenku kan zaben fid da gwani da aka kammala, zan yi kokarin ganin an share wa kowa hawayensa domin jam’iyyarmu ta ci gaba da iko a zauren majalisan dattawa da kuma babban zaben 2023. Ba za mu taba barin wannan barazanar ba tabbata ba.
“Akwai hanyoyin da za mu bi wajen warware duk wata matsa da ta kunno kai.
Wannan shi ne kyakkywan tsari a cikin dimokuradiyyarmu wanda muke gudanarwa. Tun daga lokacin da aka kammala zaben fid da gwani nake ta samun rahoto na korafe-korafe,” in ji shi.
A cewar mashawarcin shugaban kasa a fannin yada labarai, Femi Adesina, Shugaba Buhari ya sha alwashin karfafa shugabancin jam’iyyar APC ta hanyar yin adalci a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar kafin babban zaben 2023.
Shugaba Buhari ya fada wa sanatocin APC cewa samun nasarar jam’iyyar a babban zabe ya ta’allaka ne da yanayin hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar da kaucewa rashin adalci a tsakaninsu.
Sai dai kuma Buhari ya gode wa ‘yan majalisan dattawan bisa bayar da shawaran gudanar da tattaunawa ta yadda za a su damar dinke bakin zaren na matsaloli da suka faru a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a lokacin zaben fid da gwani.
A nasa jawabin, shugaban tawagan kuma babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa a yanzu haka akwai a kalla sanatoci 22 da wasu mambobi na jam’iyyar ba su ji dadin abubuwan da suka faru a zaben fid da gwani da aka kammala ba a jihohinsu ba, saboda an gudanar da wasu lamari ba bisa ka’ida ba, wanda suka yi barazanar sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun na daban.
Ya kara da cewa ‘yan majalisan dattawan sun sadaukar da kawunansu wajen ganin jam’iyyar ta bunka a cikin dimokuradiyyar kasar nan. Ya yi kira da shugaban kasa ya kawo daukin gaggawa kan wannan lamari.
Ya ce, “Mai girma shugaban kasa, tabbas a zauren majalisa mun yi aiki tukuru wajen ganin duk manufofinka sun gudana. Muna tabbatar maka da cewa a ko da yaushe muna goyon bayanka,” in ji shi.