Cutar Hawan jini da aka fi sani da ‘Hypertension’ a turance ta zama matsalar lafiya da ke shafar miliyoyin al’umma a sasan duniya, wanda hakan ya sa zama wata barazana ga al’ummar kasa baki daya. Bawai a Nijeriya kawai cutar ke kisan bayar da tsoro ba lamari ne da ya shafi duniya baki daya.
Duniya ta san yadda cutar ke hallaka jama’a a kan haka ta ware rana ta musamman don a yi amfani da ita wajen fadakar da al’umma a ko ina a duniya yadda cutar take shiga kamar barawo tana hallaka mutane.
A duk ranar 17 ga watan Mayu, al’umma kan hadu don tunatar da juna tare da ankarar da mutane a kan bukata da muhimmanci gwajin hawan jini don sanin matsayin cutar a gare mu ta yadda za mu ci gaba da rayuwa da cutar ta tsawon lokaci.
Sau da yawa ana yi wa cutar hawan jini lakabi da “Mai kisan mummuke’ saboda yadda cutar ba ta nuna wasu manyan alamomi lokacin har sai ta kai ga mataki na kisa, wanda shigar da take yi a shiru shi kuma ke kai ga barazanar kamuwa da cuttutuka masu kisa kamar cutar zuciya, shanyewar bangaren jiki data koda da wasu cuttutuka da suka shafi zuciya.
Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa, cutar hawan jini na kashe mutum fiye da miliyan 9 a fadin duniya. A Nijeriya kuma yadda cutar ke hallaka al’umma nada ban tsoro don ita ke da alhakin mutuwar akalla mutum daya a cikin duk mutuwa uku da aka yi a kasar, don zaka samu yana fama da cutar.
Gidauniyar kula da cututtukan zuciya ta kasa ta sanar da cewa, cutar hawan jini ta kai a kalla kashi 38.1 na cuttukar da ke addabar al’umma. Inda aka ce kashi 38.1 na akalla al’ummar Nijeriya da sun kai miliyan 200 ya nuna cewa, kenan kusan mutum miliyan 26.7 na ‘yan Nijeriya na fama da cutar hawan jini kenan, lalle wannan abin takaici ne.
Haka kuma kungiyar likitoci ta kasa ta bayyana cewa, ‘yan Nijeriya na kashe Naira Miliyan 15.9 in aka kiyasata kudin magani a N15,964.76 a duk wata. Wannan ba karamin rikici ba ne a kasar da mutum miliyan 133 ke rayuwa a cikin talauci, kudin karbar maganin cutar hawan jini ya fi karfin kusan kashi 50 na al’umma Nijeriya. Masana harkokin kiwon lafiya sun tayyana cewa, abubuwan da suka shafi matsalar tsaro dana tattalin arzki sun kara karuwar cutar hawan jini a tsakanin ‘yan Nijeriya.
A wani sabon bincike da aka yi kwanan nan, an nuna cewa amfani da wayar salula yana taimakawa wajen hauhawar cutar ta hawan jini.
A ra’ayin wannan jaridar, sakamakon cutar hawan jini da ba a sha mata magani yana da tsananin gaske, nauyin tana hawa ne a kan wanda ke fama da cutar da ‘yanuwansu da kuma hukumomin kula da kiwon lafiya.
An kiyasta cewa, cutar hawan jini ce keda kashi 24 na kusan kashi 45 na matsalolin cututtutar da suka shafi cutar zuciya da ake samu a fadin tarayyar kasar nan, ba tare da wata shakka ba tabbas wannan ya zama lamari me tayar da hankali.
Taken bikin ranar cutar hawan jini ta wannan shekarar “Gwada hawan jininka, ka lura da shi don tsawaita rayuwa da shi ya yi daidai, ‘’wannan na kara nuna muhimmacin gwajin hawan jini a matsayin mataki na farko na maganin cutar.
Gyara hanyar rayuwa na daya daga cikin matakan da suka dace a yi amfani da su wajen rage barnar da cutar ke yi, cin abinci mai inganci da ke tattare da ganyayyaki, kayan lambu da sauransu da kuma rage amfani da gishiri a cikin abinci da rage amfani da abinci mai yawan suga.
Motsa jiki a kai-akai ta hanayr tafiya a kasa, hawa keke yana taimakawa wajen daidaita jinin da ke jikin mutum, ya kuma kamata a guje wa shan taba da barasa, don yin haka yana taimakwa wajen dakile hauhawar cutar.
Ga wasu mutane, motsa jiki kadai ba zai taimaka ba, ya kamata su lizimci amfani da magunguna su kamar yadda likita ya basu tare da kuma gwajin hawan jinin, ta haka ne likitan zai iya neman a rage ko a kara yawan maganin da ake sha tare da rage matsalolin da suka iya faruwa sakamakoin shan magunguna hawan jinin.
Maganin cutar hawan jini na bukatar hadin gwiwar kowa da kowa ciki har da gwamnati, jami’an lafiya da masu fama da cutar.
A ra’ayinmu ya kamata ta karfafa wayar wa da al’umma kai su kuma tabbatar da rage kudaden magunguna hawan jinin ta yadda al’umma za su samu saukin sayen magungunan da kuma samar da na’u’rorin gwajin cutar a cikin sauki.
Yana kuma da matukar muhimmanci, a wanna rana ta Hawan Jini na duniya kowa da kowa ciki har da yara kanana, tsofaffi su fahimmci illar da kisan mummuken da cutar hawan jini yake yi ga a cikin al’umma su kuma hada hannu wajen daukar matakin dakile shi.