Za a iya cewa gasar firimiya ta kasar Ingila ta shammaci mutane musamman wadanda suke ganin wasu kungiyoyin kawai rakiya za su yi, yayin da ake ganin wadanda za su tabuka abin a zo a gani kuma suke tafiyar biri a yashi.
Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ce kungiyar da aka fara yi wa kallon wadda babu abin da za ta yi sai rakiya kawai, ganin yadda dab da za a fara gasar ta sayar da babban dan wasanta, Harry Kane, wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen akan zunzurutun kudi yuro miliyan 100 tare da tsarabe-tsarabe.
- Nathan Tella: Matashin Da Ke Fatan Buga Wa Nijeriya Wasa
- Arsenal Ta Koma Ta Daya A Rukunin B, Bayan Doke Sevilla A Champions League
Harry Kane ya kasance kyaftin din kungiyar ta Birnin Landan kuma shi ne jagoran kungiyar musamman wajen zura kwallo a raga, sai dai tafiyar dan wasan ta saka shakku akan hasashen da ake yin a cewa ko Tottenham za ta yi abin a zo a gani ko kuma akasin haka.
Sai dai bayan fara kakar wasa ta bana kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta yi abin a zo a gani a karkashin sabon kociyan ta, Ange Postocoglo, wanda ya ja ragamar kungiyar wajen buga wasa mai kyau tare da lashe wasanni da dama.
Kawo yanzu Tottenham ta buga wasanni 12 tana mataki na hudu da maki 26 kuma wasanni biyu kacal ta yi rashin nasara a wannan kakar su ne wasan da ta yi rashin nasara a hannun Chelsea da ci 4-1 har gida sai kuma wanda Wolbes ta doke ta da ci 2-1 kafin a tafi hutu.
Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za a iya cewa ta ba wa duniya mamaki bayan da tun kafin a fara kakar wasan ake ganin a wannan lokacin za ta tabuka abin a zo a gani musamman ma ganin ta sayi sabon mai tsaron raga Andre Onana da dan wasa Mason Mount da dan wasan gaba Rasmus Hojlund da kuma karbo aron dan wasa Sofyan Amrabat daga kungiyar Fiorantina ta kasar Italiya.
An yi tunanin Manchester United za ta kasance a ‘yan gaba-gaba wajen neman lashe gasar firimiyar Ingila a wannan kakar sai gashi kungiyar tana fama da kanta inda a yanzu take mataki na shida akan teburin gasar da maki 21 cikin wasanni 12 da ta fafata a kakar ta bana.
Kociyan kungiyar, Erik ten Hah yana fuskantar matsin lamba daga bangaren wasu daga cikin magoya bayan kungiyar da masu sharhi akan kwallon kafa a fadin duniya da kuma ‘yan jarida ganin gazawar kungiyar wajen buga wasa mai kyau mai kayatarwa.
Liverpool, ita ma da farko an yi hasashen za ta sha wahala a kakar bana ganin yadda ta sayar da ‘yan wasanta da dama irin su Sadio Mane da Jordan Henderson da Fabinho da Firminho da sauransu.
Ana ganin ‘yan wasan kwararru ne wajen taimakawa kungiyar wajen lashe wasa kuma a lokaci guda ta sayar da su ta dauki sababbin ‘yan wasa wadanda ake ganin za su dauki lokaci kafin su gano yadda ake buga wasa a kungiyar.
Amma kuma salon yadda Liverpool din take buga wasa shima ya ba wa masu kallo mamaki domin babu wanda ya yi hasashen kungiyar za ta yi irin kokarin da take yi a yanzu duk da cewa ‘yan wasa irinsu Muhammad Salah har yanzu suna kan ganiyarsu.
Yanzu Liverpool tana mataki na biyu da maki 27 cikin wasanni 12 da kungiyar ta fafata kuma a wasa na gaba kungiyar za ta kece raini da wadda take mataki na daya, wato Manchester City a filin wasa na Ettihad dake Birnin Manchester.
Manchester City daman tana daya daga cikin kungiyoyin da za su buga abin a zo a gani a wannan kakar ganin yadda a kakar da ta gabata kungiyar ta lashe kofuna uku rigis da suka hada da gasar firimiya da kofin kalubale na FA da kuma gasar cin kofin zakarun turai wanda ta doke Inter Milan a wasan karshe.
Amma kuma kungiyara ta saki wasu zakakuran ‘yan wasanta da suka hada da Riyadh Mahrez da Ilkay Gundogan, sannan kuma dan wasa Kebin De Bruyne ya tafi doguwar jiyya tun a wasan farko na fara gasar firimiya hakan ya sa aka yi hasashen kungiyar za ta sha wahala wajen kare kambunta na bana.
Sai gashi kawo yanzu tana mataki na daya bayan ta buga wasanni 12 kuma tana da maki 28 sannan kungiyar tana buga wasa mai kyau tun da ta sayi sababbin ‘yan wasa musamman Jeremy Doku da ta saya dan Belgium.
Ita daman kungiyar kwallon kafa ta Arsenal anyi hasashen za ta tabuka abin a zo a gani domin a kakar da ta gabata sai a wasannin karshe ta barar da damar lashe gasar firimiyar kuma a wannan kakar kungiyar ta yi sayayya mai kyau a kasuwa musamman ta dan wasa Declan Rice da kungiyar ta saya daga West Ham United akan kudi fam miliyan 115, wanda ake ganin ya yi tsada da yawa.
Amma irin yadda ya karawa kungiyar karfi ya sa ake ganin tabbas kociyan kungiyar Mikel Arteta yayi tunani wajen tilasta shugabannin kungiyar su sayi dan wasan a wannan kudin domin kwalliya tana biyan kudin sabulu.