ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Gwamna Lawal Ya Samu Gagarumar Tarba A Ɗansadau

by Sulaiman
3 days ago
Gwamna lawal

Dubban jama’a ne suka mamaye manyan ƙauyuka da hanyoyin da ke kaiwa garin Ɗansadau domin tarbar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a wata ziyara ta tarihi da ya kai yankin.

A ranar Laraba ne gwamnan ya ziyarci al’ummar Ɗansadau da ke Ƙaramar Hukumar Maru, ziyara da ta ɗauki hankalin jama’a tare da nuna farin cikin al’umma bisa zuwansa.

  • Kifi Na Ganin Ka Mai Jar Koma!
  • Tinubu Zai Gabatar Da Daftarin Kasafin Kuɗin 2026 Ga Majalisun Tarayya

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa kusan shekaru fiye da ashirin kenan rabon da wani gwamnan Zamfara ya taka ƙafa zuwa Dansadau, tun daga zamanin tsohon gwamna Ahmad Sani Yariman Bakura.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ƙara da cewa, Dansadau, wadda ita ce mafi girman gunduma a Ƙaramar Hukumar Maru, ta shafe tsawon lokaci cikin mantuwa da sakaci daga gwamnatocin baya, duk da girman al’ummarta da muhimmancinta ga ci gaban yankin.

A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya ratsa wasu al’ummomi da suka haɗa da Wanke, Magami da Dan Gulbi, inda jama’a suka fito kwansu da kwarkwata domin nuna masa ƙauna da goyon baya.

LABARAI MASU NASABA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

Gwamnan ya kuma duba aikin gina titin Gusau zuwa Dansadau mai tsawon kilomita 108, wanda gwamnatinsa ta bayar da kwangilar aiwatarwa a matsayin wani muhimmin bangare na ƙoƙarin buɗe hanyoyin sufuri da bunƙasa tattalin arzikin yankin.

A wani bangare na ziyarar, Sarkin Dansadau, Mai Martaba Alhaji Garba Mohammed Sarkin Kudu, ya karrama Gwamna Lawal da sarautar gargajiya ta Garkuwan Dansadau, a matsayin girmamawa ga yadda ya nuna damuwa da sha’awar kawo ci gaba ga yankin.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa wannan ziyara ta nuna ƙarara ƙudurin Gwamna Lawal na sauka ƙasa-ƙasa domin kusantar al’umma da kuma tabbatar da cewa ayyukan raya ƙasa sun shafi dukkan sassan jihar. Tarbar da jama’ar Dansadau suka yi masa na nuni da ƙaruwar goyon bayan da gwamnatinsa ke samu, sakamakon manyan shirye-shiryen raya ƙasa da ake aiwatarwa ƙarƙashin manufar ‘Zamfara Rescue Mission’.

A cewar jama’a, ziyarar gwamnan ta sake farfaɗo da fata da kwarin gwiwa cewa Dansadau da makamantanta ba za su sake zama a bayan layi ba a tsarin ci gaban jihar Zamfara.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Next Post
Jan Aikin Da Ke Gaban Sabon Babban Ministan Tsaro

Jan Aikin Da Ke Gaban Sabon Babban Ministan Tsaro

LABARAI MASU NASABA

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.