Duk da hukuncin kotun kolin Nijeriya, rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar PDP da LP ya kara kamari, a halin da ake ciki har yanzu jam’iyyun guda biyu sun gaza magance rikicin shugabanci.
Duk da cewa shugabannin jam’iyyun biyu sun yaba da hukuncin kotun koli wanda a cikin hukunce-hukuncen daban-daban, har yanzu jam’iyyun biyu ba su sami masalaha ba game da warware rikicin cikin gida a tsakaninsu.
- Manchester Ta Kai Zagayen Semi Final A Europa Bayan Doke Lyon
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 157, Sun Ƙwato Bindigu Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
Yayin da jam’iyyar PDP ke fama game da rikicin sakataren jam’iyyar na kasa, inda jam’iyyar LP ke fama da rikicin shugabanta na kasa.
Mutane uku na ikirarin zama shugabannin LP, yayin da Sanata Samuel Anyanwu da Hon. Sunday Udeh-Okoye ke fafatawa kan wane ne ainihin sakataren PDP na kasa.
A cikin LP, Kwamared Julies Abure ya ci gaba da rike sakatariyar jam’iyyar, yayin da Sanata Nenadi Usman da Lamidi Apapa suma ke ikirarin zama shugabannin jam’iyyar.
Wata majiya ta ce PDP na cikin mawuyacin hali da kuma rashin tabbas a harkokinta wanda ya tilasta jinkirta taron shiyya da aka shirya gudanarwa a karshen makon da ya gabata.
Wata majiya ta ce hukuncin da kotun koli ta zartar akwai rikitarwa saboda an gwama siyasa a ciki.
Amma sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fada a wata hira kan cewa hukuncin kotun koli a bayyane yake kuma yana da fa’ida ga gudanar da jam’iyyar a kasar, ya kara da cewa an ba da ikon magance matsalolin da ke tattare da rikice-rikicen da za su iya shafi masu rike da mukaman jam’iyyar.
Ya ce abin da kotun ta yanke hukunci shi ne cewa dole ne a warware duk wani abu da ya shafi matsayi na jam’iyya ta hanyar tsarin cikin gida na jam’iyya, sannan kotun ta ce ba za ta yi katsalandan ga al’amuran jam’iyyu ba kamar yadda dokoki da ka’idoji suka bayyana.
Ya ce PDP ba ta cikin wani mawuyacin hali game da hukuncin, ya kara da cewa tsarin cikin gida na jam’iyyar zai yanke shawara tare da samar da mafita.
Yayin da PDP tana cikin mawuyacin hali saboda jinkirin warware matsayin sakataren jam’iyyar na kasa, al’amura na kara tabarbarewa a LP. A makon da ya gabata ne bangare uku suke ikirarin zama shugabannin jam’iyyar na kasa.
Julius Abure, Nenadi Usman da Lamidi Apapa sun ci gaba ikirarinsu na zama a matsayin shugabancin jam’iyyar, duk da cewa sakataren yada labarai na kasa, Obiora Ifoh, ya bayyana cewa wadanda ke fafatawa da Abure suna yin was an kwaikoyo ne kawai.
A cewarsa, a yayin da kotun koli ta fadi karara cewa ba ta da iko a kan lamarin da ya shafi rikicin cikin gida na jam’iyya kuma ta mayar da iko ga tsarin jam’iyyar, wasu mambobin jam’iyyar suna yin wasan kwaikwayo ta hanyar zuwa ofishin hukumar zabe ta kasa, lamarin da ya ce ba shi da tasiri.
Ya ce hukuncin kotun koli ya yi watsi da batun shugabancin jam’iyyar tare da soke hukuncin kotun daukaka kara, har ma ba ta tabbatar da wani mutum a matsayin shugaban jam’iyyar ba.
“Abin da wannan ke nufi shi ne, an mayar da jam’iyyar zuwa matsayi na farko. Kuma Abure ya kasance shugaban jam’iyyar na kasa har tsawon lokacin da wa’adinsa ya kare,” in ji Ifoh.
Mai magana da yawun jam’iyyar ya gargadin Sanata Nenadi Usman da sauran masu adawa da Abure cewa kar su yaudari ‘yan Nijeriya da fassarar da ba daidai ba game da hukuncin kotun koli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp