Duk da cewa, ilimi kyauta ne kuma dole ga yara a matakin farko a fadin tarayyar Nijeriya, amma kudaden da ake karbar a bayan fage a hannun iyaye yana taimakawa wajen korar yara daga makaranta, abin kuma da ke kara matsalar rashin karatu da rubutu da ake fuskanta a kasar nan.
Wani yaro dan shekara 13 mai suna Khalifa Abdullahi yana wasa a kusa da wani shago a unguwar Karon Majigi, da ke yankin babbar birnin tarayar Abuja a ranar wata Litinin.
- INEC Za Ta Dauki Hayar Motocin Sufuri 100,000 Da Jiragen Ruwa 4,200 Don Raba Kayan Zabe – Yakubu
- Jimillar Jarin Da Asusun Raya Kasashen Sin Da Afirka Ya Zuba Ta Zarce Dalar Amurka Biliyan 5
Duk da cewa yakamata a ce Abdullahi yana zuwa makaranta amma a kullum aikinsa kenan yin wasa tun da ya bar zuwa makaranta saboda rashin kudi sheakra 4 da suka wuce.
Ya bayyana wa jaridar The ICIR cewa, mahaifinsa wanda yake sana’ar direba ya yi hatsari a shekarfar 2018, tun daga lokacin shi da sauran ‘yanuwansa suna kasa cigaba da zuwa makaranta.
“Dukkan abokai na na zuwa makaranta haka sauran yaran yankinmu nine da ‘yanuwa bama zuwa makaranta don mahaifinmu ya ce ba shi da kudaden da zai biya mana kudin makaranta.,” in ji shi.
Da take tabbatar da wannan labarin, mahaifiyar Abdullahi mai suna Khadijat, ta ce, al’amarin ya yi matukar wahala basa samun kudaden da za su sanya yaransu kowacce makarantu masu zaman kansu harma da makarantun gwamnati.
Ta bayyana cewa sun yi kaura ne daga kaduna ita da mijinta saboda matsalar tsaro a shekarar 2015 inda suke rayuwa ta hanyar yin kananan ayyuka.
“Babu wani yaro da ke zuwa makaranta a nan gidan, ba wai babu makarantan ba ne a amma babu kudin kai su makaranta ne, babban yarona yana zuwa makaranta amma daga baya muka kasa biyan kudaden makarantan, a halin yanzu yana nan a gida tun shekara 4 kenan da suka wuce,” in ji ta.
Kowanne dan Nijeriya nada hakkin samun ilimin farko a makarantun gwamnati kamar yadda dokar UBEC ta shekarar 2004 ta tanada. Wannan ya hada da matakin mjakaratun firamare da shekara 3 na matakin karamar sakandare.
Sashe na 2 na dokar ta bayyana cewa, matakin farko na firamare kyauta ne kuma dole ga dukkan ‘yan Nijeriya.
Dokar ta kara bayyana cewa, “Dukkan wata gwamanti a Nijeriya za ta bayar da ilimi a matakin farko kyauta kuma dole ga dukkan yara ‘yan Nijeriya da sukia kai shekaru 7 na karatu tun daga matakin firamare zuwa karamar sakandire,”.
Duk da cewa, akwai makaratun gwamnati da dama a sassan babbar birnin tarayya Abuja amma wasu kudaden da ake karba daga dalibai yana sanya iyayye da yawa na janye yaransu daga makaranta saboda rashin kudaden biya.
Bincike ya nuna cewa, kudaden da ake karba don shiga da makarantun gwamnati a matakin firamare na kaiwa Naira dubu 10,000 zuwa Naira 20,000 ga masu neman kai yaransu karamar makarantar sakandire, wasu lokutta ma abin ya kan kai fiye da haka.
A makarantar LEA Firamare na Karon Majigi, sai ka biya Naira 20,450 kafin a karbi yaronka a matsayin matakin Firamare.
A zaiyarar da manema labarai sukakai makarantar sun fahinci cewa, kudaden da ake karba na 20,000 ya hada ne da kudin rajista, N500; kudin kungiyar PTA, N1950; kayan Makaranta, N2500; kudin ajiyar bayanan dalibi, N500; rajista ta intanet, N500; kayan wassanni, N2000 da kudin wasu takardun karatu da sauransu.
Makarantar na kuma karbar N200 na jarabarwa da za a yi wa dalibi don tantance ajin da za a sa shi.
In har an dauki yaro ana kuma bukatar ya zo makaranta da bokiti da tsintsiya.
Haka lamarin ya ke a makarantar LEA ta ‘City Gate’ da ke Durunmi Abuja.
A ziyarar da manema labarai suka kai wannan makarantar sun fahimci cewa, ana bukatar akalla Naira 18,600 kafin ka iya sanya yaron ka sashin firamare na wannan makarantar.
Bayanin da aka samu daga makarantar ya nuna cewa, kudin rajista ya kai N1000, na PTA N1500; kayan makaranta, N3000; kudin jarabawa, N300; kayan wasanni, N2000; rajista ta intanet, N300; kudin jarabawa, N500; da kuma kayan aiki, N1000.
Sauran sun kuma hada da kudin littafan rubutu, N600; kudin tsaro, N500 wani kudin PTA na daban N500.
Kudaden littafan karatu da suka hada dana Lissafi, Turanci da sauran su, N7400, gaba daya kenan kudaden sun kai N18,600.
Haka kuma a makarantar LEA ta unguwar Durunmi II, shiga makarantar firamare ana bukatar Naira N25,400, wanda ya hada da kudin rajista, kayan makartanta, kayan wassani, littafan karatu, dozin daya na littafan rubutu da kuma kudin PTA.
Binciken ya naua cewa, sauran kudaden da ake nema bayan yaro ya shiga makarantar basu da yawa sukan kasance ne daga N1500 zuwa N5000 da kuma kudaden takardu a wasu lokutta in bukatar haka ya taso.
Haka lamarin yake a sauran kananan hukumomin yankin Abuja.
A makarantar UBE Firamare da ke Pasali a karamar hukumar Kuje, kana bukatar N10,000 don yi wa yaronka rajistar shiga ajin farko na makarantar, kudaden sun kuma hada da na rajista, kayan makaranta da kayan sanyi. Wannan kuma baya hada ba ne da takardun karatu da na rubutu ana kuma bukatar iyaye ne su sayo da kansu ne a kasuwa.
A Nijeriya da kusan rabin al’umma ke cikin matsananciyar talauci, mutum Miliyan 133 wanda hakan yana nuna kusan rabin al’ummar kasar kenan.
Matsalar tattalin arzkkin da ake fuskanta ya sanya iyaye da dama na fatutukar ganin sun biya kudaden nan a wasu lokutta kuma basu da zabi illa su cire yaran nasu daga makarantun sabo basu da kudin biyan kudaden da ake bukata.
Tabarbarewar Matsalar Rashin Zuwa Makaranta
Nijeriya nada yara fiye da Miliyan 20.2 da basu zuwa makaranta, kamar dai yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana, wanda wannan ne mafi yawa a cikin kasashen duniya gaba daya.
Dalilai da dama na daga cikin matsalolin da suka taimaka wajen hana yaran zuwa makaranta ciki kuwa har da matsalar tsaro da kuma talauci.
Maimakon a lura da yadda wadannan matsalolin suka taimaka wajen hana yara zuwa makaranta sai gashi kudaden da ake bukata na daukar yara a makarantun gwamati yana kara yawan yaran da suke gararanba a kan titunan kasar nan ba tare da samun ilimi ba.
Fatima Aremu ‘yar sheakra 14 da ke sayar da Kunu da Lemu a tashar nan ta Area 1 ta bayyana wa manema labarai cewa, ta daina zuwa makaranta ne bayan da mahaifinta ya rasu kuma uwarta ta rasa aikin da take yi.
“Na kammala makarantar Firamare amma na kasa cigaba saboda mahaifiyata ba za ta iya biyan kudin makarantar ba, sai ta ce in zauna a gida na dan wani lokaci har sai ta samu kudin da za ta iya biya min kudin makarantar, amma zuwa yanzu kusan shekara uku kenan har yanzu ina gida bana zuwa makaranta,” in ji ta.
Nijeriya nada karancin masu wucewa daga matakin firamare zuwa sakandire, a rahoton hukumar UBEC ta watan Afrilu, ta bayyanha cewa kasa da kashi 30 ne na mata ke samun wucewa mataki na gaba bayan kammala karatun firamare.
Lamarin yana kara ta’azzara ne a kan kudaden makaranta da ake tilasta wa iyaye biya a matakin na Firamare da Sakandire.
Ita kuwa Bictoria John mai shekara 12 a duniya tana sayar da piya wata ne a marabar ‘Life Camp’ a kullum banda ranakun Lahadi tana haka ne kuma don ta tallafa wa kudin shigar iyayenta.
Ta bayyana wa manema labarai cewa, iyayen ta sun kasa biyan kudaden makarantar ta dana sauran ‘yanuwanta ne a kan haka ta bar zuwa makarantar ta bar ‘yanuwan nata su cigaba da zuwa ita kuma tana neman kudaden tallafa wa gida.
“A aji na 6 na daina zuwa, ina gab da shiga JSS 1, ta ce za ta mayar da ni makaranta a shekara mai zuwa inta samu kudi amma yanzu bukatun kudaden sun kara yawa, don yanzu tana biyawa kani nane kudin makarantar, yana aji 3 ne a halin yanzu,” in ji ta.
A dukkan makaratun da manema labarai suka ziyarta an fahimci cewa ana biyan kudin ne ba tare da wata lambar asusun banki ba don ana biyan kudin ne kai tsaye ga hukumar makarantar, dalibai da aka tattauna da su sun tabbatar da cewa, suna bayar da kudin ba tare da an basu raciti ba.
Doka Ta Haramta Karbar Kudin Makaranta
Doka ta tabbatar da hukunci mai girma in aka karbi wani kudi daga dalibai na matakin firamare da karamar sakandire na karkashin dokokin UBEC.
Sashi na 3 na dokar ta bayyana cewa, “Za a bayar da ilimin a matakin Firamare da karamar sakandire kyauta, kuma duk wani da ya karbi kudi da sunan bayar da ilimi a wannan matakin za a hukunta shi da zaman gidan yari na wata uku ko kuma ya biya kudin tara na abin da bai gaza NI0,000:00 koi kuma a hada masa duka biyun.”
Amma duk wannan tanadin na doka, makarantu a yankin Abuja na ci gaba da karbar kudaden makaranta daga iyaye abin da ke kara nisantar da karatun daga ‘yan asalin yankin da dama.
Shugaban hukumjar ‘Unibersal Basic Education Board (FCT-UBEB)’ na yankin Abuja, Hassan Sule ya ce, wadannan kudaden da ake karba haramun ne, a tattaunawarsa da manema labarai.
“Kudin PTA abu ne a tsakanin iyaye da malamai, babu wani shugaban makaranta ko malamai da aka bashi izinin karbar kudi daga wani dalibi, doka ta haramta,” in ji shi.
Ya nemi iyaye da aka nemi su biya wasu kudade a makarantun gwamanati da su kai karar hakan ga hukumar UBEB na yankin Abuja.
Samar Da Mafita
Babban dalilin da makarantu ke karbar kudade daga iyaye a makarantun gwamnati shi ne rashin issasun kudaden gudanarwa daga gwamnati.
Yayin da majalisar dinkin duniya ta ayyana kashi 15 zuwa 20 na kasafin kudin kasa ga sashin ilimi a kasasfin kudin Nijeriya kashi 7.9 kawai aka warewa ilimi a cikin kasafin kudin 2022.