A Jihar Kaduna, wasu manoma masu fama da nakasa daban-daban kama daga makafi da Guragu da kuma kurame sun rungumi dabarun noman zamani don tallafawa kansu.
Wadannan nakasassun manoma suna gudanar da aikin noma ne ta tsarin da aka fi sani da “Inclusibe Farming System for Persons with Disabilities To Fight Hunger in Nigeria ,” wanda ke da nufin shigar da kowa musamman masu nakasa wajen noma domin yakar yunwa a Nijeriya.
- WAFCON 2025: Yau Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Moroko A Wasan Ƙarshe
- NSCDC Ta Gurfanar Da Wanda Ake Zargi Da Badakalar Naira Miliyan 159
A halin yanzu, nakasassun manoma sun himmatu wajen aikin noma a matsayin hanyar ciyar da kansu, maimakon barace-barace.
Duk da karancin ruwan sama a bana, manoman ba su yi kasa a gwiwa ba; suna ci gaba da yin aiki tukuru a gonakinsu, ta hanyar amfani da dabarun zamani don tabbatar da samar da wadataccen abinci mai inganci.
A Jihar Kaduna masu bukata ta musamman sun kama hanyar zama gwarazan manoma, sakamakon yadda da dama daga cikin masu nakasa suka mayar da hankali kan noman zamani a jihar domin inganta rayuwarsu.
Wannan yana cikin wani tsari na noma da aka kirkiro musamman don masu bukata ta musamman domin su dogara da kansu maimakon rokon hatsi ko neman taimako.
Wannan yana cikin wani tsari na noma da aka kirkiro musamman don masu bukata ta musamman domin su dogara da kansu maimakon rokon hatsi ko neman taimako.
Wakilinmu ya ziyarcj wata kebabbiyar gona dake cikin garin Kaduna, inda gungun wasu manoma da ke fama da lalurori daban-daban irin su makanta da gurguntaka da kurma, suka rungumi sabbin dabarun noma na zamani domin tallafawa rayuwarsu, musamman a wannan damina da aka shiga.
Gonakin da wadanda makafi da guragu ne suke nomawa a duk shekara Sun bayyana cewa suna gudanar da nomansu ne ba tare da wata gudummawa daga gwamnati ba kama da samar musu da takin zamani da sauran kayan noma kamar yadda ake tallafawa Masu lafiya.
A zantawarsa da wakilinmu a cikin gonarsa, Mista William Makiya, wanda ke fama da matsalar gani (makaho), yana noma da huda domin ciyar da iyalinsa. Ya bayyana cewa:
“Ba na gani da idona. Dalilin da yasa nake yin noma shine domin ciyar da iyalina. Ba na yin bara kuma bana san yin bara kwata-kwata rayuwata. Ba na kaunar bara.”
William ya kara da cewa yana jin dadin aikin noma, kuma yana taimakawa makwabtansa masu lafiya da kayan abinci daga gonarsa. Wannan yana karfafa zumunci da hadin kai tsakaninsa da sauran al’umma da suke zaune tare a cikin muhalli daya.
Ya ce:“Da galma nake yin wannan noma. Ina amfani da fatanya da sauran kayan huda wajen noma da kuma cire ciyawa a gonaki.”
Ya ci gaba da cewa gonarsa tana da layukan shuka wanda yake amfani da su wajen shuka wake, dankalin hausa, gyada, da kayan lambu irin su tumatur da kubewa.
A kowace shekara, jajirtattun manoma masu bukata ta musamman ne ke amfani da wadannan filayen noma domin ciyar da kansu, kamar yadda wani matashi mai lalurar kafa Mai Suna Joshua Matthew, ya bayyana cewa Shi ma yana noma da huda a gonarsa.
“Abin da ya kamata a sani shi ne, ni ina noma da huda sosai domin ciyar da iyalina. Ina noma masara da shinkafa da sauran kayayyakin abinci domin rage tsadar rayuwa.”
Joshua ya ce duk da cewa ba shi da kafa, yana zaune yana jan jikinsa domin yin noma da cire ciyawa da sauran ayyukan noma. Ya tabbatar da cewa ya dade yana wannan aiki, kuma babu wahala kamar yadda mutane ke tunani.
Ya jaddada bukatar gwamnati ta tallafa musu domin su zama masu dogaro da kansu.
Duk da karancin ruwan sama a bana, wadannan manoma ba su karaya ba. Sun ci gaba da aiki tukuru a gonakinsu, suna amfani da dabarun noma na zamani domin tabbatar da samun abinci mai yawa da inganci.
Babu shakka, wadannan manoma suna gudanar da aikin noma ta hanyar wani tsarin hada kowa da kowa musamman masu nakasa cikin harkar noma domin yakar yunwa da talauci a Nijeriya. Wannan tsarin na “inclusibe smart farming” ya fara haifar da nasarori, a cewar Kwamared Rilwani Abdullahi, shugaban kungiyar masu bukata ta musamman a Nijeriya.
Ya ce:“Wannan wani yunkuri ne na zama masu dogaro da kai. Saboda haka, muna kira ga hukumomi da su tashi tsaye wajen tallafawa wadannan manoma, da kuma tabbatar da cewa ana sanya su a cikin jerin manoman da ake tallafawa a duk lokacin da ake rabon takin zamani.”
Yanzu haka dai, wadannan gwarazan manoma sun dukufa sosai cikin harkar noma domin ciyar da kansu maimakon barace-barace. Sai dai, sun koka kan yadda ake rarraba takin zamani ba tare da an tuna da su ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp