Kashi 90 na manoman Karamar Hukumar Kudan a Jihar Kaduna, na amfani da Garmar Shanu ne, wajen gyaran gonakinsu tare kuma da rashin samun kwararrun masu yin aikin, wanda hakan ya jawo rashin noma amfanin gona mai yawa.
An gano hakan ne, biyo bayan binciken da tawagar sa ido a fannin aikin noma tare da wata kungiya mai zaman kanta ‘PYDERA Global’ suka yi a karkashin shirin kungiykr na Rayuwa.
- Tura Ta Kai Bango, Zanga-zanga Ta Kai Gidan Buhari Da Sarkin Daura
- An Tarwatsa Masu Zanga-zanga Kan Kokarin Kunna Wuta A Kofar Gidan Gwamnatin Kano
Kwararre a aikin noma a karkashin shirin, Mista Nathaniel Otene; yayin da yake rabar da injinonin Garma na zamani guda 15 ga manoman da ke Kudan kuma da na Karamar Hukumar Kafur ta Jihar Katsina.
Ya ce, yin amfani da Garmar Shanu wajen yin noma; na jawo wa kananan manoma rashin samun kudaden shiga masu yawa, inda ya kara da cewa, don rage kalubalen rashin wadataccen abinci da kuma habaka tattalin arziki, musamman na kananan manoma; ya sa kungiyar ta wanzar da wannan shiri nata na Rayuwa, ta hanyar raba wa manoman injinon Garmar na zamani guda 15, domin yin noma.
A cewar Otene, wadannan kaya; ko shakka babu za su taimaka wa manoman da suka amfana wadannan injina matuka wajen gyara gonakinsu da kuma kara samar musu da kudaden shiga.
Ya kara da cewa, an zabo manoman da suka amfana da wannan tallafi ne daga cikin kungiyoyi daban-daban, bisa tsarin ba su wannan tallafi.
Ya sanar da cewa, kimanin manoma 375 ne da suka fito daga Kananan Hukumomin Kudan ta Jihar Kaduna da kuma wasu 200 daga Karamar Hukumar Kafur ta Jihar Katsina.
A jawabinsa a wajen rabar da kayan, Shugaban Karamar Hukumar Kudan, Shuaibu Bawa Jaja; ya yaba wa kungiyar a kan rabar da wadannan kaya tare da yin kira ga kungiyar da taimaka wa sauran kananan manoman da ba su samu damar amfana da kayan a wannan karon ba.
Shi ma, a nasa jawabin Dagacin Kudan; Alhaji Halliru Mahmood da kuma Dagacin Hunkuyi, Alhaji Aminu Ashiru; sun yi kira ga wadanda suka amfanan da kayan da su yi amfani da su ta hanyar da ta dace tare kuma da taimaka wa wadanda ba su samu ba, domin gyara nasu gonakin su ma.