• English
  • Business News
Friday, October 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya

by Abubakar Abba
7 months ago
Apapa

A yanzu, masu hada-hadar fitar da kaya da shigo da su a kasar nan, sun samu damar safarar kayansu a hanyar yin amfani da hanya a layin Jirgin kasa na Apapa-Moniya.

Wannan zai kara taimakawa wajen damar da damar fitar da kaya kai tsaye zuwa kasuwannin da ke a duniya.

  • Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba
  • Trump Ya Dakatar da Harajin Da Sanya Wa Ƙasashen Duniya, Ya Ƙi Cire Wa China

A watan da ya gabata ne, aka kadamar da aikin ta hanyar yin hadaka da Hukumar Kula Da Sufurin Jiragen Kasa Ta Kasa, wanda a yanzu, ake gudanar da aiki sau uku a mako.

Jigilar kaya ta hanya, an jima a kasar tana zama babban kalubale, musamman wajen safarar kayan amfanin gona, musamman masu saurin lalacewa wanda hakan ke janyo yin asara da kuma haifar da jinjir da tsadar safarar kayan zuwa ga tashar Jiragen Ruwa.

Kazalika, kaddamar da wa za ta taimaka wajen saurin safarar amfanin gona da rage bata lokaci da kuma lalacewar kayan da aka yi safarsu.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

A makon da ya wuce ne, masu kula da wajen aijiye kaya a tashar Jiragen Ruwa ta Apapa, suka tattauna da masu safarar kayan amfanin gona da kuma wakilan Gwamnatin jihar Oyo domin tattaunawa kan yadda za a yi jigilar kayan amfanin gonar.

Manajan lura da sashen wajen ajiye kayan Steen Knudsen ne, ya jagoranci tawagar zuwa layin Dogon na Moniya, domin duba yadda aikin ke tafiya da ke a Ebute-Metta.

Knudsen ya bayyana cewa, aikin zai taimaka wajen ragewa masu jigilar kayan yin asara ta hanyar yin jigilarsu, ta hanya.

Ya kara da cewa, aikin zai kara taimakawa wajen jigilar kayan a cikin sauki.

Ita ma Jette Bjerrum, daga kasar Denmark ta bayyana cewa, kasar Denmark a shirye take wajen taimakawa Nijeriya don yin jigilar kayan amfanin gonar da kuma dabbobin da ake da bukatar yin jigilarsu, matukar Gwamnatin kasar ta amince da shirin na bunkasa hada-hadar kasuwancin.

Sai dai, masu ruwa da tsaki da sauran kwararru, sun nuna fargabar su, dabgane da batun tanadar tura kayan daga Ibadan ba tare da jigilarsu zuwa jihar Legas ba.

Shi kuwa mai bai wa gwamnatin jihar Oyo shawara ta musamman Tilewa Folami, aikin zai taimaka wajen kara bunkasa sadarwa a tsakanin babbar kasuwar da ke a Afrika ta tsakiya da kuma jihar ta Oyo.

Sauran masu ruwa da tsaki a fannin sun bayyana cewa, yin amfani da tashar ta Moniya, zai kara taimakawa wajen kai kayan a cikin sauki.

Shi kuwa Farfesa Frank Ojadi, wanda ya fito daga makarantar koyon kasuwanci da ke a jihar Legas ya sanar da cewa, aikin zai taimaka wajen rage jinkirin jigilar kaya a tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.

A cewar Farfesa Frank Ojadi, fitacciyar Dalar Gyada ta da, wani alamu ne ragin da aka samu na sarrafa kaya, wanda hakan ya janyo saboda fuskatar karancin kayan aiki da kuma rashin watatattun layukan Dogo a kasar nan. “A wadancan shekarun baya, babu wadattun layukan Dogo a kasar nan, inda hakan ya sanya sai dai kawai a ajiye kayan, inda hakan ya sanya aka fara yin Dalar Gyada a kasar”. Inji Frank.

Frank ya yi gargadi da cewa, idan har Nijeriya kayan aikin da ake son yin amfani da su wajen jigilar kayan suka gaza, cimma burin da aka sanya a gaba, Nijeriya za ta ci gaba da fuskantar kalubalen safarar kaya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA
Tattalin Arziki

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

October 17, 2025
Next Post
Hanyoyi Biyar Na Kare Kajin Gidan Gona Daga Tsananin Zafi

Hanyoyi Biyar Na Kare Kajin Gidan Gona Daga Tsananin Zafi

LABARAI MASU NASABA

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa

October 31, 2025

Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda

October 31, 2025
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai

October 31, 2025
Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

October 31, 2025
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

October 31, 2025
Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta

Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta

October 31, 2025
Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?

Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.