Yadda Yajin Aikin ASUU Na Tsawon Watanni 9 Ya Cutar Da Mu – Dalibai

Yajin Aiki

Wakilimu Mahdi Musa ya tattauna da wasu dalibai inda suka bayyana yadda yajin aiki da kungiyar Malaman jami’a ASUU ta yin a tsawon wata 9 ya shafi raayuwar su, duk ,uwa da cewa, kungiyar ta janye yain aiki ana kuma daf da bude makarantukin i  dawA cikin wannan rubutun, ADAM IBRAHEEM, ZAHRA AUWAL, BAKIR BELLO Da AMINA BELLO sun ba da rahoton abubuwan da suka fuskanta a yayin zanmansu a gida bisa dalilin yajin aikin da ya dauki sama da wata tara, wanda kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta dakatar kwanan nan.

Adam Ibrahim, ABU:

Ga Adam, wani dalibi da ke karatun digiri a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, ya bayyana cewa, “yajin aikin na tsawon watanni tara da malaman suka yi ya shafi karatunmu da sauran fannonin rayuwa. Yawancin dalibai suna karatu ne kawai a cikin harabar makaranta saboda suna da damar yin amfani da kayan karatu kamar littattafai da sauran kayan aiki. Amma yajin aikin ya hana su amfani da irin wadannan muhimman kayayyaki. Haka zalika, yajin aikin ya ba da gudummawa ga hauhawar ayyukan aikata laifuka tsakanin dalibai, saboda ba su da aiki kuma tunaninsu ya cika da munanan tunani da tasiri mara kyau. An kuma tilasta shiga kungiyoyin aikata laifuka, kamar kungiyar asiri da makamantansu.”

Zahra Auwal, FUDMA:

Zahra, wacce take mataki na daya a karatun digiri dinta a sashin ilimin halitta ‘Microbiology, kwalejin kimiyyar rayuwa, ta bayyana cewa, ta yi takaici matuka da wannan yajin aikin da ya sanya ta zaman gida har na tsawon watanni tara. Ta ce, “Yajin aikin ya kara tsayin lokacin karatu na kai tsaye, domin kammala karatun a shekarar 2024 ba zai yiwu ba. Karatun da ya kamata ya dauki shekaru hudu, yanzu sai ya dauki shekaru biyar zuwa shida. Idan aka yi la’akari da yajin aikin ASUU, an san cewa babu makawa anan gaba akwai sauran abubuwan da zasu faru, komai na iya faruwa. Abin bakin ciki ne.”

Bakir Bello, ABU Zaria:

Bakir, wani dalibi dake karatu a jami’a shima ya koka da cewa, kusan watanni 10 kenan da kulle jami’o’in mu a dalilin yajin aikin ASUU. Daya daga cikin hanyoyin da abin ya shafeni shine ina wahala wajen karanta littattafaina wanda hakan ya kan sani in ji kamar dalibi ne ni wanda bai taba zuwa makaranta ba. Hanya ta bitu ita ce kara tsayin kalandar karatu. Mafi yawa dalibai a jami’o’i masu zaman kansu sun gama da karatun su na 2019/2020, amma mu har yanzu muna cikin zangon karatu na farko saboda yajin aikin.

Bello Sani, ABU Zaria:

Bello Sani shima ya bayyana irin takaicin sa na wannan yajin aiki, a inda yake cewa, “Nauyi ne a wurina. Hakan ya shafi harka ta ta kasuwanci saboda shirina shi ne na kwashe wasu shekaru kalilan domin na koma na ci gaba da harkokina na yau da kullum, amma wannan yajin aikin ya haifar min da rashin tabbas. Ina kira ga Gwamnatin tarayyar Nijeriya da ASUU da su sake bude jami’o’i ba tare da bata lokaci ba.”

Muhammad S. Bello, ABU Zaria:

MS ya bayyana irin nasa damuwar shima na wannnan yaji aiki, a inda yake cwa, “Ina so in yi amfani da wannan damar don yin kira ga gwamnatin tarayya da ASUU da su yi la’akari da halin kuncin da talakawa ke ciki a jami’o’in gwamnati. Kuma na samu masaniya a kan cewa, mafi yawan abokan karatunmu da muka samu karatu tare a jami’o’i daban-daban, musamman jami’o’i masu zaman kansu, sun gama karatunsu, wasun su ma sun fara yiwa kasa hidima, amma mu har yanzu muna fama da yajin aikin ASUU.”

Amina Bello, ABU Zaria:

Amina ta bayyana cewa, yajin aikin ya shafe ta ta hanyoyi da dama, musamman kara tsayin shekarun karatun. Lokacin da sauran dalibai a wasu jami’o’i ke shirin zuwa mataki na gaba, ita tana gida ba tare da yin komai ba.

Exit mobile version