A daidai wannan lokacin da Musulmin duniya ke shirye-shiryen fara yin azumin watan Ramadan na bana, wanda kuma a cikinsa ake samun dimbin lada na yin wasu ayyukan ibada.
Masu yin azumi na da wasu siffofi da ake gane su da su, da kuma ke tsayuwa a wannan lokaci na watan azumin wanda ake samun dimbin lada na yin wasu ayyuka ibada tare, domin kara karfafa wa juna gwiwa, azumi na da cikin aikin ibada wadda ke taiaka wa wajen kara samun lafiyar dan’adam da ma kare shi daga kamu wa da wasu cututtuka a lokacin rayuwarsa.
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Matsayinta Na Warware Matsalar Ukraine A Siyasance
- ‘Yan Bindiga Sun Harbe Shugaban APGA Har Lahira A Ebonyi
Jin ra’ayin jama’a da aka yi a kan azumin watan ‘Ramadan da karamar sallah’, ya nuna yadda fiye da mutum 18,000 suka tofa albarkacin bakinsu daga kimanin kasashe goma sha biyu, wadanda suka hada da Nijeriya, a watan azumi na 2022. Sakamakon ya nuna cewa, bayan kara kaimi wajen yin ibadoji, hada-hadar kasuwancin da ake yi a wannan lokaci na kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.
A Nijeriya a kowace rana, a irin wannan lokaci ana samun karuwa a kalla daga kashi 4 cikin 100, a mako daya bayan salla da kuma mako daya kafin sallar. Wadannan abubuwa na daga cikin irin sauyin da watan Azunin na Ramadan ke kawo wa. Haka kuma mutane na kokarin cika burinsu na samun farin ciki a wannan lokaci. Sannan kuma kashi 77 daga cikin kaya da ‘yan Nijeriya ke sa wa lokacin sallah sababbi ne.
Ana tanadin hidimar da za a yi a cikin watan Ramadan da sallah ,sannan kuma wadanda Allah ya hore wa kan bayar da kyaututtuka, musamman sadakar abinci. Haka kuma kashi, 88 daga cikin 100 a Nijeriya na mika sakonnin fatan alheri ga ‘yan uwa da abokan arziki a wannan lokaci. Sannan kuma binciken ya nuna cewa, wasu mutane a Nijeriya na kallon bidiyon hidimar da ake yi a lokacin azumin da lokacin sallah.
Watan azumi dama ce, ta musamman da mutum zai nemi lahira cikin sauki ta hanyar sadaka wadda ke kan gaba wajen abin da ake so, wadanda ke da hali su yi a lokacin azumin na Ramadan. Haka kuma ana so a kara karfafaf zumunci da taimakon juna.
Saboda haka babban darasin da watan azumin ke koyarwa shi wadanda Allah ya hore wa, suke da wadata da yalwar abinci, su sani akwai dimbin jama’a da ba su samu irin wannan damar ba, saboda haka suna bukatar a tallafa musu.
Enitan Denloye, Daraktan wata shiyya ne da ke yankin Saharar Afirka ya ce, “Wannan watan azumin na 2023 dama ce da mutum zai iya amfani da ita wajen samun riba mai yawa, ta hanyar kara kaimi wajen yin ibada da kautata wa jama’a.”