Yadda Zazzabin Lassa Ya Lakume Rayuka 176 A Nijeriya

Lassa

Daga Abubakar Abba,

Hukumar dakile  yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da cewa, kimamin mutane 176 sun mutu a dalilin kamuwa da zazzabin lassa a kasar nan.

Hakan na kunahe ne a cikin rahoton da hukumar ta fitar a makon da ya gabata,  inda hukumar ta NCDC ta bayyana cewa,  daga watan Janairu zuwa 22 ga watan Maris na shekarar 2020 hukumar ta gwada jinin mutane 4012 inda sakamakon gwajin ya nuna cewa, mutane 932 na dauke da cutar sannan 176 sun mutu.

Hukumar ta ce, wasu daga cikin almominta sune, ciwon kai, inda ciwon kai alama ne cewa lallai sai an duba mutum a asibiti, domin idan zazzabin lassa ya kama mutum ciwon kai na daga cikin alamun dake fara nunawa.

A cewar Hukumar akwai kuma zazzabi, inda wanda ya kamu, zai  rika jin jiki yayi nauyi kamar zazzabi-zazzabi haka idan Lassa ta shiga jikin mutum kuma zazzabi ko masassara zai rika damun mutum a wannan lokaci.

Har ila yau, NCDC tace, akwai ciwon jiki, inda Jikin mutum zai rika yawan yi masa ciwo sosai ko kuma rika jin ciwo yake masa, inda hakan yake  nuna alama ce dake nuna an kamu da Lassa.

Akwai kuma sun hada da ciwon gabobin, ciwon baya, yawan gajiya sannan a wasu lokutan har da ciwon kafafu.

Hukumar ta kara da cewa, akwai kuma amai saboda zafin zazzabi da ciwon kai mutum kuma zai rika yawan yin amai.

Har ila yau, akwai rashin iya cin abinci domin yana hana cin abinci.

Wanda ya kamu kuma zai dinga yawan yin Bahaya a dalilin kamuwa da wannan cuta sannan hakan zai sa mutum yawan jin kishin ruwa.

Hukumar ta sanar da wasu hanyoyin da za a iya kaucewa kamuwa da zazzabin wadanda suka hada da, saftace Muhalli,  zubar da Shara.

Akwai kuma bukatar a dinga killace abinci  kuma  haka zai taimaka wajen hana Bera ko kwari shiga cikin abincin.

Ana son a dinga dafa nama kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman.

Kaucewa namun daji, inda ya kamata a nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin Berayaye da birai.

Akwai bukatar a dinga cin yayan itatuwa Kafin a ci yayan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai, inda kuma hakan na kau da datti a jikin su.

A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci, inda  Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

Akwai kuma toshe kafafen da suka bude, don a tabbatar an toshe ramin da Bera zai iya shiga cikin dakunan kwana ba.

Bugu da kari, akwai tsafta wato a yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.

Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

Kona daji wato na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane ana kuma son a kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu.

 

Har ila yau, wanke gawa a cikin Daki ,inda hakan na da illa matuka.

Akwai kuma hanyoyiin samun magani da suka hada da, da zarar mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi, haka  kuma ba a iya kamuwa da cutar zazzbin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shih aka kuma za a iya warkewa daga zazzabin lassa idan an gagga.

 

Exit mobile version