A kokarin rage radadin da al’umma ke fuskanta sakamakon hana
zirga-zirga da gwamnatin jihar Kaduna ta yi don dakile yaduwar cutar
coronavirus, wani shaharraren dan jarida kuma mawallafin jaridar
Kabido, Malam Adamu mashal ya gabatar wa da ‘yan jarida a Kaduna
tallafi na musamman.
Da yake tattaunawa da manema labarai bayan raba tallafin a Kaduna, ya
bayyana cewa, ya gabatar da tallafin don rage wa abokan aikin nasa
radadin da suke fuskanta sakamakon doka hana zirga-zirga da aka sanya
a fadin jihar. Tallafin ya kuma hada da sinadarin wanke hannu,
(sanitisers) da kuma kayan masarufi, ya kuma yi nuni da cewa, yana
fatan cigaba da samar da karin tallafin a nan gaba. Ya kuma yi kira ga
wadanda tallafin bai kai gare su a wannan karon ba su kara hakuri, ya
kuma yi kira ga manyan kamfanomi da masu hannu da shuni da kada su
manta da ‘yan jarida a tallafin da suke raba wa, musamman kayan kariya
daga kamuwa da cutar coronavirus.
Daga nan kuma Malam Adamu Mashal ya bukaci ‘yan jarida su bi dukkna
shawarwarin da likitoci masana ke bayar wan a hanyoyin kare kai daga
kamuwa da cutar coronavirus a yayin da suke ayykansu na sanar da
a’umma labaran halin da ake ciki game da cutar coronavirus.
Al’umma dai sun yaba da wannan tallafi da Malam Adamu Mashal ya bayar
sun kuma bukaci sauran jam’a su yi koyi da shi.