Edita, don Allah ka ba ni fili a wannan jarida tamu mai farin jini don in kara sautin amon murya ta kan sauran muryoyin da ke ta kiraye-kiraye ga gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU game da yajin aikin da kungiyar ke yi tsawon kimanin watanni takwas kenan.
Yau kusan wata 8 kenan jami’oi a Nijeriya suke a kulle sakamakon rikicin da yaki ci yaki cinyewa tsakanin Gwamnati da ASUU, rikicin da ya sam oasali tun kusan 1999, an yi gwamnatoci da dama wadanda suke gadar wannan rikici kuma haka suke shudewa ba tare da kawo karshen shi ba, a namu bangarenmu dalibai wannan rikicin ba karamin cutar da rayuwarmu yake ba, domin duk lokacin da aka tafi irin wannan yajin aiki, komai na karatunmu tsayawa yake, kuma sannan da yawan mu komawa gida mukeyi muna zaman banza zaman jiran tsammani, saboda ko da mutum ya nemi wani abin yi dole sai dai ya zama na wucin gadi.
Tun daga lokacin da aka fara rikita rikita tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU ba a taba yin gwamnati da dalibai muka sanya rai da tsammanin za ta kawo karshen wannan rikici ba, irin wannan gwamnati ta mai girma shugaban kasa Muhammad Buhari, hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon irin kyautata mata zato da muke yi da kuma yadda muka ga tana yawan ambatawa a wajen yakin neman zabe cewa zata kula da rayuwar matasa, kuma zata bai wa harkar ilimi mahimmanci, amma sai dai kash gashi gwamnati tana shirin karewa lamarina kokarin chanjawa, a ranar 26 ga watan June, 2022 mun hango minister ma’aikata a fadar gwamanati da keAbuja, bayan kammala zaman Majalisar Ministoci watau FEC yana mana Albishir da cewa kusan komai ya zo karshe yanzu jira kawai suke yi hukumomin da abin ya shafa su tattara reports zuwa ranar laraba sai a yi sign, jin wannan labarin ya faranta mana rai sosai, ammah sai gashi mun ji shiru har zuwa yanzu.
Wani abu da ya kara daga mana hankali sai ji muka yi a ranar Litinin 4 ga watan Yuli Shugaban Kungiyar ASUU yana wata magana mai kama da habaici, inda ya cewa “a shirye suke su jira gwamnati ta neme su ko da nan da shekara 2 ne, inda ya kara da cewa su da membobinsu zasu tuka mortar hanya, su siyar da gyada domin su samu abin da zasu ci ”Wannann maganar ta daga mana hankali gaskiya, domin duk dalibi na kwarai dole ya tausayawa malamansa tsawon wata 8 basu da Albashi, da wannan muke rokon gwamnatin tarayyah karkashin shugabancin Muhammadu Buhari, don Allah su tausayawa mana, su cika mana Alkawarin da Suka mana lokacin Campaign, Su tausayawa halin da yan uwanmu matasa ka iya fadawa sakamakon wannan dogon yajin Aiki.
Umar Kabir Dakata, marubuci ne kuma matashi mai sharhi kan harkokin ilimi da rayuwar matasa, shi ne kuma shugaban kungiyar Arewa Media Writers na Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp