Abba Ibrahim Wada" />

Yakamata Manchester United Ta Sayar Da Pogba – Evra

Pogba

Tsohon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Patrice Evra, ya bayyana cewa lokaci yayi da kungiyar zata sayar da dan wasa Paul Pogba zuwa Real Madrid saboda yafi bukatar komawa kungiyar a halin yanzu.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na sha’awar dauko dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba, amma rahotanni na nuni da cewa hakan zai yiwu ne kawai idan mai horar da ‘Yan wasanta, Zinedine Zidane ya ci gaba da zama a Santiago Bernabeu.

Zidane dai babban masoyi ne na Pogba, wanda dan kasar Faransa ne, kuma ya nuna cewa a shirye yake ya dauke shi daga Old Trafford da zarar an bude kasuwar hada hadar ‘yan wasa a shekarar 2021.

A wannan makon ma, Paul Pogba ya fito karara ya bayyana sha’awar komawa Real Madrid, inda ya ce fatansa kenan a ce ya buga wasa a filin wasa na Estadio Santiago Bernabeu wanda zakarun na La liga suke buga wasanninsu na gida.

Sai dai sanya farashin Yuro miliyan 114 da Manchester United ta yi a kan Pogba ya sanya Real Madrid ta janye daga batun sayen dan wasan amma Pogba da Zinedine Zidane sun hadu, har sun tattauna yadda za su samo mafita a game da sauya shekar.

 

Exit mobile version