Hadakar shugabannin ‘yan adawa sun zargi gwamnatin tarayya da amfani da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa wajen tsoratarwa da tsangwama ga ‘yan adawa, suna gargadin cewa wannan yanayi yana kawo barazana mai tsanani ga dimokuradiyya mai jam’iyyu da dama a Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, shugabannin sun zargi gwamnatin Shugaba kasa Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati a matsayin makami, musamman hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ‘yansanda da kuma hukumar yaki da safararar haramtattun kudade, don tursasa wa ‘yan adawan siyasa a karkashin jagorancin yaki da rashawa.
- Wang Yi Ya Zanta Da Ministocin Wajen Cambodia Da Thailand
- Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Farfesa Ibrahim Tsafe A Matsayin Sabon Shugaban Jami’ar ZAMSUT
Bayanin ya kasance na hadin gwiwa ne da ya hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban jam’iyyar ADC, Sanata Dabid Mark da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Mista Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Edo, Babban John Odigie-Oyegun da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na yankin kudu, Babban Olabode George da kuma tsohon karamin ministan harkokin tsaro, Lawal Batagarawa.
“Yan Nijeriya sun shaida abin da yake faruwa yanzu a matsayin wata manufa ta boye, wadda ba ta bi tsarin dimokuradiyya ba, don tabbatar da cewa dukkan gwamnatocin jihohi suna karkashin ikon jam’iyyar shugaban kasa, ana hanyar tsoratar da gwamnonin adawa a boye ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa har sai sun mika wuya kuma sun karkata daga ra’ayisu.
“Kwanan nan wasu gwamnonin adawa da suka koma jam’iyyar gwamnati sun karfafa zargin da jama’a suke yi na matsin lamba na siyasa ba tare da tunani ko neman shawarwarin mutum ba, wannan lamari ya saba wa tsarin dimokuradiyya.
“Wannan tsarin ya kasace wani bangare ne na babban farmaki wanda ba wai kawai ga shugabannin da aka zaba ba har da manyan jiga-jigan ‘yan adawa da ake ganin sune masu tsara sabbin hadin kai kafin zaben shekarar 2027.
“Dole ne mu fadadar kan wannan mummunan aikin, idan aka bar shi ya ci gaba ba tare da kulawa ba, yana da hadari sosai ga makomar dimokuradiyyar Nijeriya,” in ji sanarwar.
Shugabannin sun kara zargin cewa hukumomi da ke yaki da cin hanci da rashawa sun aikinsu ne kadai a kan ‘yan adawa, suna yi ikirarin cewa ana yawan watsi da tuhumar da ake yi wa mambobin jam’iyyar gwamnati, yayin da ake matsa lamba sosai kan tuhumar da ake yi wa ‘yan adawa har ma a gabatar da su a kafafen watsa labarai.
Sun ce maganganun da aka yi a baya na cewa tsohon shugaban jam’iyya mai mulki, Adams Oshiomhole, ya ce “dazarar ka shiga APC, an gafarta maka dukkan zunubanka,” wanda suka ce ya zama alamar yadda jama’a ke kallon rashin daidaito wajen amfani da dokokin yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya.
Sun kara da cewa, “Wasu ‘yan misalai na baya-bayan nan sun kara tabbatar da wannan lamari. Watanni da suka gabata, an samu wata minista cikin wani al’amari na almundahanan kudade wanda har sai da ta kai fushin al’umma ya tilasta masa yin murabus.
“Duk da haka, bayan ta sauka daga mukaminta, ba a taba tuhuma ko gurfanar da ita a gaban EFCC ba, kuma yanzu tana shiga cikin yakin neman zaben shugaban kasa karo na biyu.
“Haka kuma, wani minista ya ci gaba da rike mukaminsa duk da cewa jami’ar da ya ce ya yi karatu sun musunta hakan, inda suka musanta takardar shaidar karatunsa a fili. Shi ma ya yi murabus ne kawai bayan matsin lamba daga jama’a. Watanni bayan haka, ba a shigar da kara a kansa ba.
“Wannan aikin na musguna wa ‘yan adawa yana rage ingancin yunkurin yaki da cin hanci da rashawa kuma yana keta amincin jama’a ga hukumomin kasa,” sanarwar ta kara da cewa.
A matsayin wani bangare na bukatunsu, shugabannin jam’iyyun adawa sun yi kira ga babban lauyan gwamatin tarayya, tare da tuntubar majalisar kasa da su kafa wata hukumar bincike mai zaman kanta don duba asusun gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi daga shekarar 2015 zuwa 2025.
Sun ce akwai bukatar hukumar da aka ba da shawarar ta sami cikakken damar shiga bayanan kudi na jama’a, ta wallafa bincikenta, ta bayyana tsarin tuhuma da shawarwari na gyara don karfafa EFCC.
Shugaban ‘yan adawa sun kuma ba da shawarar saka jami’an yaki da cin hanci da rashawa kai tsaye cikin tsarin biyan kudi da kashe kudaden gwamnati a dukkan matakan gwamnati maimakon kawai hukunta ta tsaya kan kamawa masu laifuka.
Sun yi kira ga ‘yan Nijeriya su kare dimokiradiyya, masu sanya hannu sun ce a makwannin masu zuwa, za su tattauna da abokan hulda na kasashen waje, ofisoshin jakadanci da kungiyoyin duniya don bayyana damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin karuwa cusa siyasa a hukumomin yaki da cin hanci na Nijeriya.
A ranar Asabar, ADC ta zargi hukumar yaki da cin hanci da rashawa kan saka siyasa da batun soke belin da aka bai wa tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami.
Sai dai a ranar Asabar, hukumar ta ce an bai wa Malami belin tun a ranar 28 ga Nuwamba, 2025, amma ya kasa bin sharuddan belin duk da an ba shi karin lokaci bisa dalilan lafiya.
EFCC ta ce an sake gayyatar Malami a karshe a ranar 8 ga Disamba, 2025, kuma an tsare shi har sai ya cika dukkan sharuddan belin da aka gindaya masa.














