Kungiyar ‘yan banga a Afirika ta Kudu mai lakanin Operation Dudula ta yi kaurin suna wajen kai samame a wuraren kasuwancin ‘yan kasashen waje tare da rufe shagunansu.
Sashen binciken kwakwaf na BBC Africa Eye ya bankado yadda masu cin zarafin baki suke cin karensu babu babbaka a kasar ta Afrika ta Kudu.
- Tashar Lekki Ta Sa Kaimin Bunkasuwar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka
- Halittar Mata Na Canzawa Bayan Aure
Dimakatso Makoena, wata uwa ce mai ‘ya’ya uku wadda ke aikin dafa abincin ‘yan makaranta a Kwa Thema da ke Gabashin Birnin Johannesburg, mai shekaru 57 ta yi wa BBC karin haske ta na zubar hawaye.
“A gaskiya na tsani baki, buri na su fice daga kasarmu,”
Abu ne mai matukar wahala fahimtar dalilin wannan tsananin kyamar baki, amma lokacin da Miss Makoena ta nuna wa BBC hoton wani yaro a rame ya zazzaro ido kuma jikinsa duk tabon kuna sai ta kara da cewa:
“Wannan dana ne ya fara shaye-shayen kayan maye tun yana da shekaru 14, ya kan fita ya sato kayan mutane don ya sayar ya samu kudin sayen kayan maye.
Wata rana ya je satar wayar na’urorin hasken lantarki sai wuta ta kama shi a nan ya samu wadannan raunukan da suka bata masa jiki da fuska.
Danta ya na shan kwayoyi irin su crystal meth da nyaope, wasu sinadarai masu tsananin sa maye wadanda a yanzu matasan da suke ta’ammali da su suka addabi yankuna da dama a fadin kasar ta Afrika ta Kudu.
Irin wannan yanayi ya sanya iyaye da dama sun goyi bayan kungiyar ‘yan banga ta Operation Dudula.
An fara kaddamar da Operation Dudula ne shekaru biyu da suka gabata a Soweto, ta kasance kungiya ta farko da ta fara kai hare-hare kan wadanda suke haifar da rikicin kyamar baki a Afirka ta Kudu, wanda ya samo asali tun bayan kawo karshen mulkin ‘yan tsirarun farar fata a shekarar 1994.
Kungiyar ta fara kiran kanta da sunan ”dudula” wanda yake nufin kora a harshen Zulu.
Soweto ta kasance a sahun gaba wajen yaki da wariyar launin fata a mahaifar Nelson Mandela zababben shugaban kasar Afirika ta Kudu na farko bisa tafarkin dimokuradiyya.
A yanzu garin ya rikide zuwa cibiyar masu kyamar baki ‘yan kasashen waje.
Baki na rayuwa cikin fargaba sakamakon barazana daga marasa aikin yi a Afirika ta Kudu, kasar da cikin kowanne rukuni na mutane uku daya ba shi da aikin yi.
Adadin baki ‘yan kasashen waje a Afirka ta Kudu bai kai yadda al’ummar kasar suke bayyanawa ba idan aka kwatanta da sakamakon binciken da Cibiyar Nazarin Tsaro (ISS) ta fitar a shekara ta 2022.
Rahoton cibiyar ya bayyana cewar akwai akalla bakin haure miliyan 3.95 daidai da kashi 6.5 na al’ummar kasar.
Gaba daya adadin da yake daidai da tsarin ka’idojin kasa da kasa, wannan adadi ya kunshi duk wanda ba dan asalin kasar ba ne ko daga ina ya zo.
Kalaman kyamar baki da wasu jami’an gwamnati da ‘yan siyasa da kungiyoyin masu kyamar bakin haure ke amfani da su sun rura wutar jita-jitar cewa kasar ta cika da bakin haure.
Wani binciken dabi’un al’ummar Afirika ta Kudu da hukumomin kasar suka gudanar a shekara ta 2021 ya gano cewar kusan rabin al’ummar kasar miliyan 60 sun yi imanin cewa bakin haure tsakanin miliyan 17 zuwa 40 ne suke rayuwa a Afirika ta Kudu.
Wani kwarya-kwaryan zabe ya nunar da cewar jam’iyyar ANC wadda Mandela ya taba shugabanta za ta iya samun koma baya da kashi 50 a karon farko.
Kungiyar ‘yan banga ta Operation Dudula ta dauki aniyar maye gurbin adadin da ANC za ta rasa, a yanzu ta rikide zuwa jam’iyyar da za ta yi takara a zaben da za a gudanar a kasar, badi.
Shugabar kungiyar mai suna Zandile Dabula wadda aka zaba a watan Yuni shekara ta 2023 mace ce mai nutsuwa da kwarjini tana sake yin duba game da taken kungiyar wanda ke cewa ”bakin haure ne tushen matsalolin tattalin arzikin Afirika ta Kudu.”
Yayin da aka tambaye ta game da ko yakin neman zaben zai karkata kan ‘yaki da bakin haure sai ta shaida wa BBC cewar:
“Ya zama tilas a fahimci cewar dukkan matsalolin da suka dabaibaye kasar nan, sun samu ne sakamakon kwararowar bakin haure da suka yi kama guri zauna.”
“Kasarmu ta rushe, ‘yan kasashen ketare sun kirkiri wani tsari na shekaru 20 da nufin su karbe ikon Afirika ta Kudu.”
Da aka kalubalance ta game da wannan batu na karbe ikon kasar sai ta ce jita-jita ce amma ita ta yarda.
“Duk inda ka duba kwayoyin shaye-shaye ne kuma wadanda suka fi amfani da su al`ummar Afirika ta Kudu ne maimakon ‘yan kasashen ketare, su na shayar da matasanmu ne don su samu saukin karbe ikon kasar?”
Tsanar da ake yi wa bakin hauren ta na karewa ne kan wadanda suke zaune a kasar bisa ka`ida.
Wani dan Nijeriya ya shaida wa BBC yadda ‘yan bangar suka ci zarafinsa tare da watsar da kayan kasuwancinsa ba tare da sun tambaye shi komai ba.
“Sai ka koma Nijeriya, mu ‘yan Afirika ta Kudu ne.” in ji ayarin ‘yan bangar.
Yanzu haka ba shi da sana’a yana kwana a kan hanya ya bayyana wa BBC cewar : “Na yi zabe a kasar nan a matsayi na na dan kasa, ban taba ganin kasar da ta ke tozarta mutane haka ba, idan na karya doka na cancanci a yi min hukunci ko a mayar da ni kasata, amma ban yi laifin komai ba kun ci zarafi na ko kudin haya ba zan iya biya ba, abin ya yi yawa zan koma kasata.”
Kungiyar ta Dudula ta jaddada cewar ta na ayyukanta ne don yaki da shigar kayan shaye-shaye to amma babu wata shaida da ta tabbatar da cewar masu sayar da kwayoyin ba ‘yan Afirka ta Kudu ba ne.
BBC ta hadu da dakarun na Dadula a Diepkloof da ke Gabashin Soweto lokacin da suke kan hanyar zuwa wurin wani dan kasar Mozambikue bayan wata ‘yar Afirika ta Kudu ta kai musu kara cewar bai biya ta kudin hayar gida ba.
Batu ne da ya kamata a tattauna amma sai Mandla Lenkosi na Kungiyar Dudula ya fara barazanar yi masa duka.
BBC ta tambaye su game da dabi’un cin zarafi da sara-suka sai suka amsa cewar suna aiki ne don mutane su bi doka.
Mista Lenkosi, wanda ya fito daga garin Soweto bayan ya rasa aikin yi, na sahun gaba a kungiyar musamman idan sun kai farmaki gidajen bakin haure ko cibiyoyin da ake zargi ana hada-hadar kwayoyi da kuma mutanen da izinin zamansu a kasar ya kare ba su fita ba.
“Mun girma a lokacin da kasar nan ta ke fuskantar wariyar launin fata, amma wancan lokacin ya fi wanan nagarta,” In ji dan kungiyar ta Dadula.
Cedric Stone jigo ne a kungiyar ta Dudula ya kara bayyana wa BBC cewar: “Akwai bukatar Afirika ta Kudu ta koma lokacin baya.”
“Kakanninmu ne suka fara shagunan cikin motoci amma yanzu ‘yan Bangaledesh da Somaliya da Habasha sun karbe sana’ar, ina dalili?”
Shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya yi Allah-wadai da kyamar baki da kuma harin da ‘yan banga suke kai wa ‘yan kasashen ketare bayan ya danganta irin wadannan halaye da lokacin wariyar launin fata.
Annie Micheals, wata ‘yar fafutuka ce a Johannesburg ta ce ‘yan Afirika ta Kudu sun dora alhakin yanayin da ake ciki kan wadanda ba su da laifi, kamata ya yi su gode wa bakin haure saboda irin jajircewarsu wajen dogaro da kai.
“Ku daina zama wuri daya kuna korafi da jiran gwamnatin da ta gaza wajen biyan bukatunku.”
Shugabar Kungiyar Dadula ta ce wadanda suke ganin wannan kungiya an samar da ita ne don kai hare-hare ba su fahimci ayyukanta ba.
A watan Mayu daruruwan magoya bayan kungiyar sun halarci babban taro a birnin Johannesburg inda mambobi suka kada kuri’ar yin rijista don mayar da kungiyar jam`iyyar siyasa.
A lokacin gangamin kungiyar, mambobi da magoya baya sun yi dandazo dauke da tutocin Afirika ta Kudu suna rawa da waka a kan tituna.
Amma wakokin da suke rerawa na dauke da sakon barazana: ”A kone bakin haure, za mu sayo fetur mu banka wa bakin haure wuta.”
Kayan Sojoji da suke amfani da su sun yi kamanni da lokacin yaki, Miss Makoena na daga cikin masu farin ciki a lokacin gangamin.
Yayin gangamin, Isaac Lesole mai mukamin mai bayar da shawara a kungiyar ‘yan bangar ta Dudula ya tambayi dandazon magoya baya: “Ku na so mu yi sulhu da bakin haure?”
“Ba ma so,” in ji magoya bayan Dudula.
A tsarin dokokin Afirka ta Kudu yi wa jam`iyya rijista ba ya nufin ta samu damar tsayawa takara akwai wasu sharudda da za ta bi.
Kungiyar Dudula ba ta da wani tsari ko manufa, sai dai ta na yada manufofinta na matsayarta kan baki ‘yan kasashen ketare, kodayake shugabar kungiyar Miss Dabula ta ce kungiyar ta na da tasiri a kowanne lardi ban da yankin Northern Cape.
Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar da suka zanta da BBC sun bayyana bukatar ganin an yi gyara a siyasar kasar.
An dora alhakin kyamar baki a Afirika ta Kudu kan fatara da rashin ayyukan yi da shaye-sharen kwayoyi da suka addabi da dama daga cikin al`ummar kasar.