‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sa-kai sama da 70 a ƙauyukan Kukawa da Bunyun da ke Ƙaramar Hukumar Kanam a Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Litinin, lokacin da ɗaruruwan ‘yan sa-kai daga ƙaramar hukumar Wase ke kan hanyarsu ta zuwa daji inda aka ce ‘yan bindiga na ɓuya, amma sai aka yi musu kwanton-ɓauna a hanyar.
- ADC: Tinubu Na Yunƙurin Raba Kawunan Masu Haɗaka Kafin Zaɓen 2027
- Nijeriya Ba Ta Da Sha’awar Yin Gwajin Makamin Nukiliya — Shettima
Shugaban ‘yan sa-kai na Kukawa, Aliyu Baffa, ya ce ‘yan sa-kai sama 70 aka kashe, kuma akwai yiwuwar a gano wasu gawarwakinsu a daji.
Ya bayyana cewa kwanton-ɓaunar ta faru ne kusan kilomita ɗaya daga garin Kukawa, kusa da dajin da ake kira Madam Forest, wanda ke iyaka da Jihohin Bauchi da Taraba.
Baffa ya ƙara da cewa an gano gawarwakin wasu a gonaki.
“Mun riga mun binne sama da mutum 60 a Kukawa kaɗai,” in ji shi.
“Wadanda suka tsira sun ce ‘yan bindigar sun fi ƙarfinsu.”
Wani mazaunin ƙauyen Bunyun da ke gundumar Nyalun a ƙaramar hukumar Wase, Musa Ibrahim, ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kai hari ƙauyensu, inda suka kashe ‘yan sa-kai 10 da ke tsaron yankin.
Musa ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun ƙone gidaje da dama a ƙauyen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp