Wani rahoton tsaro na wata-wata da wani kamfani mai zaman kansa na tsaro, Beacon Consulting Ltd ya fitar, ya ce a Nijeriya an samu rahotannin tsaro 935, inda mutane 1,127 suka mutu a hannun ‘yan bindiga a watan Oktoba, 2023.
Rahoton da aka fitar a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2023, ya ce an yi garkuwa da mutane 518 a tsawon lokacin, yayin da matsalar tsaro ta kara ta’azzara idan aka kwatanta da watannin baya.
- Nijeriya Za Ta Bayar Da Fifiko Ga Fasaha Da Makamashi Shettima
- Yadda Za A Sake Farawa Daga Birnin San Francisco
Rahoton ya yi nazari ne kan al’amuran tsaro da suka faru a Nijeriya daga tsakanin 1 zuwa 31 ga watan Oktoban 2023.
A cewar rahoton, a watan Oktoban 2023, “Nijeriya ta fuskanci matsalolin tsaro 935 wanda ke nuni da karuwar kashi 70.6 cikin 100 daga bayanan da aka fitar a watan Satumba; an samu asarar rayuka 1,127 wanda ke nuni da karuwar kashi 93.97 cikin 100, sannan an sace mutane 518 da ke wakiltar kashi 50.6 cikin 100.”
Rahoton ya kuma yi nuni da cewa yankin Arewa-maso-Gabas ne ya fi kowane yankin yawan fuskantar matsalar tsaro da asarar rayuka, da kuma sace-sacen jama’a, yayin da yankin Arewa-maso-maso-Yamma ke bi masa baya.
Bayanai daga cibiyar tsaro ta Beacon sun nuna cewa an samu bayanan matsalar tsaro 466, kazalika an samu asarar rayuka 433, da kuma sace mutane 253 a fadin kananan hukumomi 62 da ke yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.
“Rikicin tsakanin ISWAP) da Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal Jihad (JAS) ya taimaka wajen karuwar adadin.”
Rahoton ya kara da cewa an samu asarar rayuka a yankin Arewa maso Gabas.
Manajan daraktan kamfanin Beacon Consulting Limited, Dokta Kabir Adamu, ya yi karin haske game da rahoton, inda ya bayyana matsalolin rashin tsaro a Nijeriya da kuma bukatar yin amfani da tsarin da bayanan da kamfanin Beacon Consulting ke fitarwa domin inganta rayuwar daidaikun mutane da tsaron kasa.