‘Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban APC Na Nasarawa Da Suka Sace

Daga Khalid Idris Doya

An tabbatar da mutuwar shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Nasarawa Philip Tatari Shekwo bayan da wasu masu garkuwa da mutane suka sace shi a daren ranar Asabar.

Kakakin ‘yan sandan jihar Rahman Nansel ya tabbatar da mutuwar shugaban, yana mai cewa an kai gawarsa zuwa dakin adana gawarwaki da ke asibiti sannan za su cigaba da bincike domin gano makasan gami da kamo su.

Da safiyar yau ne dai LEADERSHIP ta bada rahoton cewa an yi garkuwa da shugaban jam’iyyar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Emmanuel Bola Longe shine ya tabbatar da zancen sace shugaban jam’iyyar Philip Tatari.

CP Emmanuel ya tabbatar da cewar wasu ‘yan bindigan da ba a san ko su waye ba sun mamaye gidan shugaban karamar hukumar da karfe sha daya na daren ranar Asabar da ke kusa da Dunamis Church, Bukan Sidi a garin Lafia inda suka yi awun gaba da shi zuwa maboyarsu.

Daga bisani kuma ‘yan sandan suka tabbatar da mutuwar shugaban jam’iyyar da aka sace.

Cikakken Labarin Na Tafe…

Exit mobile version